Rundunar Sojin Najeriya Ta Kama Wanda Ake Zargin Dillalin Harsasai Ne
Daga Wakilinmu

_________
Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ta kama wani mutum da ake zargin dillalin harsasai ne, tare da ƙwato harsasai guda 300 kirar 7.62 x 39mm, waɗanda aka ɓoye cikin wani buhun wake, a wani samame da aka gudanar da nufin tarwatsa hanyoyin samar da makamai da sauran kayan aiki da ke taimaka wa ayyukan ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.
Kamen ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri, waɗanda suka sa dakarun rundunar Atsawa Blocking Force, tare da haɗin gwiwar ‘yan sa-kai na yankin, suka tare wanda ake zargin mai suna Umaru Muhammad, mai shekaru 47, da misalin ƙarfe 9:30 na daren Talata, 17 ga watan Nuwamba, 2026.
Umaru Muhammad, wanda mazaunin ƙauyen Ashe ne, ya fuskanci bincike, inda jami’an sojin suka gano harsasan da aka ɓoye cikin hikima a cikin buhun wake, a wani yunƙuri na ɓoye safarar miyagun kayayyakin a matsayin kayan kasuwanci na yau da kullum.
Binciken farko da aka gudanar kan wanda ake zargin ya nuna cewa, wai an tanadi harsasan ne domin kai su ga wasu mutane biyu da aka bayyana sunayensu da Gimba da Dare, waɗanda ake zargin mazauna ƙauyen Gori ne, da ke kusa da mashigar Kogin Neja a Ƙaramar Hukumar Lokoja ta Jihar Kogi.
Rahoton ya bayyana cewa, an ce mutanen biyu ‘yan sa-kai ne na yankin. Wannan batu ya haifar da damuwa game da yiwuwar kutsawa da kuma amfani da tsarin tsaron al’umma wajen gudanar da safarar harsasai ga masu aikata laifuka.
Sai dai, ana ci gaba da gudanar da bincike kan waɗannan zarge-zarge.
Sauran kayayyakin da aka ƙwato daga hannun wanda ake zargin, sun haɗa da babur ƙirar Bajaj guda ɗaya, wayar hannu da kuma kuɗi Naira 30,500.
A halin yanzu, wanda ake zargin yana hannun rundunar sojin, inda ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken tsarin safarar harsasan da kuma gano wasu mutanen da ke da alaƙa da wannan haramtacciyar harka.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba, 2026, Muƙaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Ƙasa, Kanal Appolonia Anele, ta bayyana cewa nasarar wannan samame na nuna ƙudurin rundunar na tarwatsa hanyoyin samar da kayayyakin da masu aikata laifuka ke dogaro da su, tare da hana ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga samun muhimman kayan aikin da suke amfani da su wajen kai hare-hare kan al’ummar da ba su ji ba, ba su gani ba.
Ta sake jaddada aniyar rundunar na ci gaba da gudanar da samamen da suka dogara da bayanan sirri, ƙarfafa haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki a harkokin tsaron al’umma da kuma tarwatsa hanyoyin safarar makamai, harsasai da sauran kayayyakin da ke taimaka wa ayyukan ta’addanci, fashi da makami da garkuwa da mutane a faɗin ƙasar.
Haka kuma, rundunar ta yi kira ga al’umma da su kasance masu sanya ido tare da gaggauta sanar da hukumomin tsaro duk wani motsi da suke zargi, musamman safarar makamai, harsasai da sauran kayayyakin da doka ta haramta cikin ɓoyayyen yanayi.
Ta kuma sake tabbatar da aniyarta ta kare rayuka da dukiyoyin al’umma masu bin doka, hana miyagu samun damar gudanar da ayyukansu cikin walwala, da kuma ci gaba da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a faɗin ƙasar.
Majiyar Rahoto: Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya (18 ga Nuwamba, 2026).
__________












