• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Soshalmidiya: Shawara Ga Zainab Bint Hijazi

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 19, 2023
in Gizago
0
Soshalmidiya: Shawara Ga Zainab Bint Hijazi
37
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Gizago

Na daɗe ina son ki ɗauki wani tsari na zama a Soshalmediya, ki fahimci matsayinka da ƙimarki, ki saita al’amuranki yadda za su dace da ƙimarki. Bari in ba ki wasu ‘yan shawarwari, idan kika bi su, in sha Allah ba za ki yi da na sani ba.

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026

1-Ko kin lura da cewa mafi yawan masu kawo maki raini, ba ‘yan ajinki ba ne? Mafi yawan su ba su kai darajar ‘yan aikinki ba. To saboda me za ki tsaya tanki-in-tanka da irin waɗannan?

2-A rayuwa irin ta zamanin yau, ki fuskanci lamuran gabanki kawai ba tare da kula shashashai ba. Ya kamata ki ɗauki misali da rayuwar KARE. Idan kina tafiya sai kare ya riƙa bin ki da haushi, me ya kamata ki yi domin maganinsa? Za ki bi shi da jifa ko kuma ki taya shi haushi? Abin da ya kamata ki yi shi ne, ki yi banza da shi, ki ci gaba da tafiya. Shi da kansa dole zai bar haushin, ke kuma ki isa inda kika nufa. Amma idan kika tsaya jifan sa, za ki ɓata lokacinki a banza, kuma ki zama abin kallo ga jama’a, saboda kin biye wa kare.

3-Masu iya magana sun ce SAI AN KULA KASHI YAKE ƊOYI. Misali kina tsakar tafiya a titi, sai ki wuce ta wurin kashi, ƙuda na bibiyar shi, idan kika tsaya kore wa kashin ƙudaje, zan ishe ki da ɗoyi. Kamar haka ne a nan soshalmediya, idan kika biye wa shashashai, kamar kin biye wa kashi ne, ɗoyi zai dame ki har wasu su riƙa jin ƙyamar ki.

4-Wani mai azancin magana ya ce: “Never argue with a fool, people may never spot the difference. Idan kina biye faɗa da irin waɗannan a soshalmediya, kina ƙara masu ƙima da suna ne. Babu wanda ya san su, amma ke an san ki, don haka sai ki haskaka su. Da ma abin da suke nema ke nan, su yi suna.

5-Hajiya, ki koyi share su daga duniyarki. A duk lokacin da wani ya tsokane ki. KI YI KAMAR MA ALLAH BAI HALICCE SHI BA. Ki yi kunnen shegu da shi. Haka zai gaji ya bari!

Allah kare mu daga masu son taɓa mutuncinmu, Amin.

Previous Post

Shugaba Tinubu Ya Sauke Shugabannin Rundunonin Tsaro

Next Post

Burina In Shiga Aljanna A Sanadiyyar Waƙa – Alkantamawy

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
Burina In Shiga Aljanna A Sanadiyyar Waƙa – Alkantamawy

Burina In Shiga Aljanna A Sanadiyyar Waƙa - Alkantamawy

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

INSECURITY IN MALUMFASHI: A CLARION CALL TO SERIOUS ACTION

INSECURITY IN MALUMFASHI: A CLARION CALL TO SERIOUS ACTION

March 6, 2025
BIU TO LAGOS: An Adventurous Journey to Honour Dr. Bukar Usman

BIU TO LAGOS: An Adventurous Journey to Honour Dr. Bukar Usman

August 24, 2024
SAƘON JUMU’A: Daga Malam Anas Saminu Ja’en

SAƘON JUMU’A: Daga Malam Anas Saminu Ja’en

October 6, 2023
Abin Da Ya Sa Na Naɗa Mataimaka 85 – Ciyaman Mukhtari City

Abin Da Ya Sa Na Naɗa Mataimaka 85 – Ciyaman Mukhtari City

September 18, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.