NASIHARMU TA YAU (08)

__________
A yau ne NIGERIA ta cika shekaru 66 da samun ‘yancin kai. A matsayinmu na ‘yan ƙasa, ya kamata mu natsu, tun daga shugabanninmu da mu kanmu talakawa, mu yi nazarin ƙasarmu: Me muke yi daidai, wanne ne ba mu yi daidai? Mu taru mu gyara, domin rayuwarmu ta inganta, domin kuwa MU NE NIGERIA – Idan muka gyaru, ƙasa ta gyaru. Idan muka lalace, to mu ne muka lalace!”
__________












