TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (3)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Masu shirya wannan taro, sun tsara cewa muƙaloli guda biyu ne za a gabatar a yayin taron. A rahotannin baya, mun gabatar da muƙalar da Hon. Abdullahi Mahuta ya gabatar, wacce Bashir Yahuza Malumfashi ya yi wa ta’aliƙi. A yau kuma za mu gabatar da muƙalar da Malam Haruna Musa Rugoji ya gabatar, wacce kuma daga bisani Dokta Aminu Garba Waziri ya yi wa ta’aliƙi.
√ Wane Ne Haruna Musa Rugoji?
Malam Haruna, jajirtaccen mutum ne mai ƙima, wanda kuma ayyukansa suka bayyana cewa shi cikakken mai kishin al’ummar Malumfashi ne da Jihar Katsina da ma Najeriya gaba ɗaya. Yana ɗaya daga cikin muhimman mutane da aka karrama da kambin girmamawa a wannan taro. A yanzu haka shi ne Shugabar Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina (KTSTA). Malami ne wanda daɓensa ya ji makuba a ɓangaren ilimin Musulunci da na zamani. Haka kuma shi ɗan kasuwa ne, kamar kuma yadda yake ɗan siyasa.

√ Muƙalar Malam Haruna Rugoji
Taken muƙalar da ya gabatar shi ne, “Soshalmidiya A Mahangar Musulunci.” Wannan muƙala wa’azi ne na musamman ga masu amfani da Soshalmidiya, domin a kiyaye dokokin Musulunci.
A yau, Soshalmidiya ta zama wani babban ɓangare na rayuwar mutane. Don haka muƙalar Malam Rugoji ta nuna cewa, tana da amfani wajen yaɗa ilimi, sada zumunci, da watsa saƙonni cikin sauri. Sai dai, da yawa daga cikin masu amfani da kafar ba su lura da illar da ke tattare da amfani da ita ba bisa ƙa’ida ba, musamman wajen bijire wa dokokin addinin Musulunci.
Muƙalar Malam tana ɗauke da nasiha da misalai domin tunatarwa ga Musulmi masu amfani da kafafen sada zumunta, domin su kiyaye haɗin kai da biyayya ga dokokin Musulunci. Ya kafa hujja da cewa fitattun malamai na duniyar Musulunci, kamar Dokta Zakir Naik da Sheikh Mufti Menk da sauransu, sun tabbatar da fatawar cewa Musulmi zai iya amfani da Soshalmidiya, musamman ta hanyoyin da ba su saɓa wa Musulunci da dokokinsa ba.
Muƙalar ta ja hankalin al’umma da su gane cewa, addinin Musulunci ya umarci muminai da su riƙa kyautata niyya a duk lokacin da za su aikata wani al’amari. Ya umurci al’umma da su zama masu taimakon juna, inda ya kafa hujja da hadisin Manzon Allah (saw) da ke buƙatar mu so wa ‘yan uwanmu abin da muke so wa kanmu. Mu zama masu faɗin gaskiya da guje wa yaɗa karya.
Kamar yadda ya ce, a kullum ana samun mutanen da ke yaɗa labaran da ba su tabbata ba a dandalin sada zumunta. “Ina jan hankalin ‘yan jarida masu lasi da marasa lasi, da su kula da abin da suke yaɗawa,” in ji Malam Rugoji.
Ya kafa hujja da faɗin Allah (SWT) a cikin Alkur’ani, aya ta 6 a cikin Suratul Hujurat: “Ya ku waɗanda suka yi imani! Idan wani fasiƙi ya zo muku da wani labari, ku bincika…” Wannan aya tana koyar da cewa Musulmi ya kamata ya riƙa tantance labari kafin ya yaɗa shi. Amma abin takaici, da dama daga cikin masu amfani da Soshalmidiya ba sa yin haka.
Muƙalar ta ja hankali da cewa, Musulunci ya haramta zagin mutane, tozarta su ko tona asirinsu. A yau, mutane da dama suna amfani da Soshalmidiya wajen ɓata suna, zagi, gugar zana da habaice-habaice da ɓullo da munanan kalmomi a kan wasu. Akwai hadisin Manzon Allah (SAW) da ya ce: “Wanda ya yi shiru a kan abin da bai dame shi ba, to hakan yana daga cikin kyawawan halayensa na Musulunci.” (Tirmidhi). Don haka, Musulmi ya kamata ya yi taka tsantsan da abin da yake wallafawa.

Malam ya yi nasiha ga masu ganin ƙyashi da hassada ga wasu da Allah ya ɗaukaka daga cikinsu, ko da mulki ko dukiya da sauransu. Ya ce bai kamata ba, domin dai Allah shi ke bayarwa ga wanda ya so kuma shi ke ɗaukaka wanda ya so kuma ya ƙaskantar da wanda ya so. “Don haka idan ka ga Allah ya ni’imta wani, ba hassadarsa ko ƙyashi ko zaginsa ya kamata ka yi ba. Kai ma ka nema wurin Allah, zai iya ba ka,” a cewar Malam Haruna.
Haka kuma ya ce Allah ya haramta bincike da bin ƙwaƙƙwafin juna. Mu daina cin zarafi da tozarta juna a Soshalmidiya. Ya ce idan mutum yana wani saƙon gyara da zai ankarar da wani mai mulki, ya riƙa yin haka cikin hanya mai dacewa.
A takaice dai muƙalar Malam Haruna tana kira ga al’umma, musamman masu tu’ammali sa Soshalmidiya da su yi taka-tsan-tsan wajen amfani da kafar, su kiyaye dokokin Musulunci.
A rahoto na gaba, za mu gabatar da ta’aliƙin wannan muƙala daga bakin gogaggen malamin jami’a kuma fitaccen ɗan siyasa mai kishin al’umma, Dokta Aminu Garba Waziri.
_______________
Bashir Malumfashi, shi ne Editan Mujallar Taskar Gizago (online)













