• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, November 27, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Babban Ƙalubalena Shi Ne Yadda ‘Yan Kasuwa Suke Riƙe Mani Kuɗin Littafi

Marubuciya Hassana Hunƙuyi

Binta Tukur Ta'alhazai by Binta Tukur Ta'alhazai
November 25, 2026
in Adabi
0
Babban Ƙalubalena Shi Ne Yadda ‘Yan Kasuwa Suke Riƙe Mani Kuɗin Littafi

Hassana Abdullahi Hunƙuyi da bangayen wasu littattafanta

20
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Babban Ƙalubalena Shi Ne Yadda ‘Yan Kasuwa Suke Riƙe Mani Kuɗin Littafi

– Marubuciya Hassana Hunƙuyi

Related posts

Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-03)

Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-03)

November 26, 2026
Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-02)

Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-02)

November 19, 2026

__________

A tattaunawa ta musamman, BINTA TUKUR TA’ALHAZAI ta gana da fitacciyar marubuciyar Hausa, Hajiya Hassana Abdullahi Hunƙuyi. Yaushe ta fara rubutu, waɗanne nasarori da ƙalubale ta fuskanta, mene ne burinta a rayuwar rubuce-rubuce? Waɗannan da ma wasu tambayoyi na daban, su ne ƙunshiyar wannan tattaunawa. Ku sha karatu lafiya.

__________

TG: Da farko muna so mu ji taƙaitaccen tarihinki.

Hassana: Sunana Hassana Abdullahi Hunkuyi. An haife ni a shekarar 1980. Ina zaune da maigidana da yarana a garin Hunkuyi, Ƙaramar hukumar Kudan ta Jihar kaduna.

Na yi karatun firamare, daga nan na wuce makarantar kwana ta ‘yan mata da ke Kaduna (GGSS). Ina da takardar shaidar malanta ta NCE. Haka kuma na yi digiri a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, a fannin Library and Information Science. A yanzu haka ina aiki a sashin ilmi na Ƙaramar Hukumar Kudan. Ina riƙe da matsayin Jami’a Mai Kula Da Al’amuran Makarantu (Schools Support Officer – SSO).

Na taɓa shiga gasar BBC Hausa a shekarar farko da aka fara ta. Na shiga da labarina na “Furucin Nadama,” inda na zo ta uku cikin masu gasa 15 da suka sami yabo.

Na taɓa cin Gasar Ƙagaggun Gaherun Labarai ta Pleasant Library and Book Club tare da Makarantar Malam Bambadiya, inda na zo ta biyu a labarina mai taken “A Sasanta.”

Haka kuma na taɓa cin gasar da Sana’a Da Ilmi Foundation ta gabatar a shekarar 2021, tare da Abubakar Imam Prize for Hausa Fiction. Na samu wannan nasara da littafina mai taken  “Wuƙar Fawa.”

Haka kuma na ci gasar Open Arts da labarina mai taken, “Magaribar Jaki.” Na taɓa cin gasar Bashir Tofa da labarina mai taken “Yaro Masomin Babba.”

Ina sha’awar karatu fa rubutu da tafiye-tafiye, haɗi da son jin labarai da kuma bincike a kan abubuwan da ke wakana a duniya.

TG: A matsayinki na fitacciyar marubuciya, a wace shekara kika fara rubutu kuma wane littafi kika fara wallafawa?

Hassana: Na fara rubutu a shekarar 2005, inda na fara da littafin “Makircin Zuciya.”

TG: Ya zuwa yanzu, adadin littattafan da kika wallafa za su kai guda nawa?

Hassana: Na wallafa littattafai kimanin ashirin da ɗoriya, kimanin guda goma sha tara suna kasuwa.

TG: Tun da farko ma, mene ne ya ja hankalinki har kika fara rubuta littafi da harshen Hausa?

Hassana: Sha’awa ce ta kai ni ga faɗawa harkar rubuce-rubuce.

TG: A cikin littattafan da kika wallafa, wane littafi ne ya fi burge ki? Sannan a cikin littanfan naki wanne ne kika fahimci ya fi burge masu karatu?

Hassana: Gaskiya, ni duk littafin davna rubuta yana matuƙar burge ni. Ba zan iya cewa ga littafin da ya fi burge masu karatu ba, domin duk littafin da ya fito, a lokacin za ki ga masu karatu suna son shi.

TG: Wace nasara ko ƙalubale kika taɓa fuskanta a harkar rubuce-rubuce?

Hassana: Bari in fara da nasara, domin ba zan taɓa mantawa ba, nasarorin da na samu suna da yawa. Na yi nasarar shiga gasanni kuma na ci wasu, wasu kuma ban ci ba amma hakan ya sa na sake samun dabarun rubutu. Sannan na samu nasarar haɗuwa da mutanen daban-daban, haka zalika na samu nasarar zuwa wurare daban-daban.

Babban ƙalubalen da na samu kuma bai wuce na riƙe kuɗi ba, a lokacin da muke ba ‘yan kasuwa littattafanmu, domin su siyar mana.

TG: Waɗanne shawarwari za ki ba ‘yan uwanki marubuta game da hanyoyin da suka kamata su bi, domin ƙara bunƙasa rubutu da harshen Hausa?

Hassana: Shawarata ga marubuta ‘yan uwana ita ce, mu tsarkake alƙalaminmu. Mu riƙa rubuta labarai masu ilmantarwa da nishaɗantarwa, tare da amfani da daidaitacciyar Hausa. Mu kuma rungumi fasahar zamani wajen tallata littattafanmu da jawo hankalin matasa zuwa karatu da harshen Hausa.

TG: Wane fata gare ki zuwa ga marubuta da makaranta littattafan Hausa?

Hassana: Fatana shi ne, in ga marubuta muna ci gaba da samar da ingantattun labarai, yayin da masu karatu za su ƙara mayar da karatun Hausa wani ɓangare na rayuwarsu. Ina kuma fatan gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki za su tallafa mana wajen bunƙasa harkar rubutu da karatu.

TG: A ƙarshe, mene ne burinki a nan gaba, dangane da harkar rubuce-rubuce?

Hassana: Burina shi ne, a rungumi fasahar zamani wajen rubutu da karatun Hausa, ta hanyar samar da littattafan karatu a intanet (ebook) da na saurare (audio book). Ina fatan hakan zai sauƙaƙa hanyar samun littattafan Hausa,  musamman ga matasa, tare da adana harshenmu da al’adunmu.

__________

Previous Post

NASIHARMU TA YAU (62)

Next Post

Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-03)

Related Posts

Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-03)
Adabi

Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-03)

November 26, 2026
Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-02)
Adabi

Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-02)

November 19, 2026
Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-01)
Adabi

Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-01)

November 12, 2026
Next Post
Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-03)

Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-03)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

RAMADAN KARIM: 11-1447

RAMADAN KARIM: 11-1447

February 28, 2026
MALUMFASHI: Yau Haƙuri Ya Yi Rana

MALUMFASHI: Yau Haƙuri Ya Yi Rana

July 21, 2026
Gwamnan Katsina Ya Raba Ma’aikatar Ilimi Zuwa Gida Uku

Gov. Raɗɗa Sponsors 40 Katsina Indigenes to Study Medicine Abroad

October 6, 2023
Buƙatarmu Mu Bunƙasa Rayuwar Mata, Matasa Da Kyautata Muhalli – Gwamnan Jigawa

Gwamna Namadi Ya Ladabtar Da Shugabannin Babban Asibitin Gumel

August 1, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Review of Gidan Badamasi Film (08-03)
  • Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-03)
  • Babban Ƙalubalena Shi Ne Yadda ‘Yan Kasuwa Suke Riƙe Mani Kuɗin Littafi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Review of Gidan Badamasi Film (08-03)

Review of Gidan Badamasi Film (08-03)

November 27, 2026
Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-03)

Sharhin Fim Ɗin Gidan Badamasi (08-03)

November 26, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.