NASIHARMU TA YAU (65)
A Tausaya Wa Masu Ciwon Suga…
__________
Marubuciya, Sadiya Garba Yakasai ta yi nasiha ga masu yayata al’amarin masu ciwon suga, inda take cewa:
Maganar gaskiya ana tsorata masu ciwon suga a sahar nan. An san ciwo ne mara daɗi da yake barazana da rayuwar mutum amma yadda ake faɗar sa, yana sa mutane a cikin zullumi, su rasa ma yaya za su yi?
Kowa likita ne a fannin suga, wanda yana daɗa bai wa ciwon barazana ga masu shi, tamkar ba su da makoma a rayuwa. Ba a gaya musu yadda za su samu afuwa sosai, an fi tsorata su da ciwon, kamar bai da sauƙi. Abu mafi alheri shi ne, masu shi, su bi shawarwarin likitocin da suke gani. Kawai mutum ya yi dokokin da likita ya ba shi, game da abinci, shan ruwa a kai-a kai, shan magani da motsa jiki.
Waɗannan su ne abubuwan da suke dole kuma muhimmai, sannan kuma a riƙa samun isasshen barci da rage ciye-ciye marasa amfani. Amma idan muka bi ta wasu likitocin soshalmidiya, to wallahi mutum sai ya mutu da tsoro.
Allah ƙara mana lafiya, Amin.
__________












