• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, September 20, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Ƙaddamar Da Babban Aikin Samar Da Ruwa

BABBAN LABARI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
November 6, 2025
in Babban Labari
0
Gwamnatin Jihar Katsina Ta Ƙaddamar Da Babban Aikin Samar Da Ruwa

A dama, Manajan Darakta na Hukumar Ruwa ta Jihar Katsina, Dokta Tukur Tingilin tare da jami'an kamfanin da aka ba kwangilar aikin, a yayin ƙaddamar da aikin

28
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Ƙaddamar Da Babban Aikin Samar Da Ruwa

Daga Abdullahi Salisu

Related posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, tare da MD. Dokta Tukur Tingilin, a yayin ƙaddamar da aikin ruwa na dam ɗin Zobe


                            •••••••
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya kafa tubalin gina kashi na biyu na aikin samar da ruwa daga dam ɗin Zobe zuwa wasu sassa na jihar.

Bikin kafa tubalin aikin, wanda ya gudana a jiya Laraba, a maharbar ruwa da ke Kafinsoli cikin Ƙaramar Hukumar Kankiya, wani muhimmin mataki ne na gwamnatinsa domin tabbatar da samun ingantaccen ruwan sha ga jama’ar jihar.

Aikin, wanda ake sa ran zai amfanar da dubban jama’a, zai shafi garuruwan Karofi, Raɗɗa, Kafinsoli, Tafashiya, Kankiya, Koda-Charanchi, ‘Yarranda, Tashar Albasa, Are, Ci Ka Ƙoshi, Faduma, Tudun Ƙadiri, Rijiya Mai Siminti, Lambar Rimi, Abukur, Tashar Bala da Ɓatagarawa.

Waɗannan garuruwa suna a cikin ƙananan hukumomin Dutsin-ma, Kankiya, Kusada, Charanchi da Ɓtagarawa. Wannan aikin yana daga cikin manyan ayyukan Gwamnatin Dokta Raɗɗa na kammala muhimman ayyuka da za su kawo sauyi mai ma’ana ga rayuwar jama’a a faɗin Jihar Katsina.

Yayin jawabinsa a wajen taron, Gwamna Dikko Umar Raɗɗa ya jaddada cewa gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar magance matsalar ƙarancin ruwa a jihar ta hanyar saka hannun jari mai yawa da samar da tsarin kula da albarkatun ruwa mai ɗorawr. Ya bayyana cewa kammala aikin Zobe zai taimaka wajen rage matsalolin ƙarancin ruwa da kuma inganta rayuwar al’umma.

Kwamishinan Ma’aikatar Ruwa ta Jihar Katsina, Hon. Bishir Gambo Saulawa ya bayyana cewa aikin mataki na 1B ya haɗa da gina bututun tura ruwa, manyan ma’adanan ruwa, da tsarin rarraba ruwa zuwa garuruwa. Ya ce ma’aikatar tana aiki tare da Hukumar Ruwa ta Jihar Katsina da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa aikin ya kammalu cikin lokaci da kuma bisa ƙa’idar da aka tsara.

Shugaban Hukumar Ruwa ta Jihar Katsina, Dokta Tukur Tingilin, ya yaba wa Gwamna Raɗɗa bisa hangen nesa da jajircewarsa wajen farfaɗo da tsoffin ayyukan ruwa a jihar. Ya ce wannan aiki zai taimaka wajen ƙara samun tsaftataccen ruwa, rage yaɗuwar cututtukan da suka shafi ruwa da kuma bunƙasa harkokin noma da tattalin arziki a yankin.

Taron ya samu halartar shugabannin ƙananan hukumomin Dutsin-ma da Kankiya da Kusada da Charanchi da Ɓatagarawa. Haka ma sarakunan gargajiya daga yankunan da aikin zai amfana da mambobin majalisar zartarwa na Jihar Katsina da jami’an ma’aikatar ruwa da sauran muhimman baƙi, duk sun samu halarta.
_______________

Previous Post

Burna Boy: Fitaccen Mawaƙin Da Ya Rabauta Da Ni’imar Musulunci

Next Post

Matsalolin Tsaro: Ƙungiyar ‘Yan Jarida Ta Arewa Ta Shirya Taron Neman Mafita

Related Posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?
Babban Labari

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta
Babban Labari

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026
KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya
Babban Labari

KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya

August 29, 2026
Next Post
Matsalolin Tsaro: Ƙungiyar ‘Yan Jarida Ta Arewa Ta Shirya Taron Neman Mafita

Matsalolin Tsaro: Ƙungiyar ‘Yan Jarida Ta Arewa Ta Shirya Taron Neman Mafita

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Tribute to Cultural Broadcaster: Muhammad Salissou Hamissou

Tribute to Cultural Broadcaster: Muhammad Salissou Hamissou

February 24, 2024
KO ME YA SA MABIYA PETER OBI SUKA RIƘA MURNAR MUTUWAR HON. EKENE ABUBAKAR ADAMS?

KO ME YA SA MABIYA PETER OBI SUKA RIƘA MURNAR MUTUWAR HON. EKENE ABUBAKAR ADAMS?

July 17, 2024
Gidauniyar Qatar Foundation Za Ta Gina Katafariyar Makaranta A Jigawa

Gidauniyar Qatar Foundation Za Ta Gina Katafariyar Makaranta A Jigawa

July 7, 2023
Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.