• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Abin Lura Game Da Bazuwar ‘Yan Kasuwar Sola Da Janareta A Najeriya

TSOKACI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
October 23, 2025
in Gizago
0
Abin Lura Game Da Bazuwar ‘Yan Kasuwar Sola Da Janareta A Najeriya

Tsakanin 'yan kasuwar sola da na lantarki

26
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Abin Lura Game Da Bazuwar ‘Yan Kasuwar Sola Da Janareta A Najeriya

Tsakanin ‘yan kasuwar sola da na lantarki


                             •••••••
A cikin ‘yan shekarun nan, al’ummar Najeriya sun shiga wani sabon yanayi na dogaro da hasken rana wajen samar da wuta, sakamakon matsalar rashin wadatacciyar lantarki. Amma abin takaici, rahotanni da zargi suna yawo cewa wasu gurɓatattun ‘yan kasuwar solar panels suna haɗa kai da baragurbin ma’aikatan lantarki domin su gurgunta samar da wutar gwamnati. Wannan ya zama wata hanya ta kasuwanci mai hatsari ga ci gaban tattalin arzikin ƙasa da kuma walwalar jama’a.

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026

Akwai alamun cewa wasu daga cikin waɗannan ma’aikata suna tozarta aikinsu, ta hanyar rashin gyara layin lantarki yadda ya kamata, ko kuma ta hanyar ƙirƙirar matsaloli don ganin mutane sun fi karkata ga amfani da kayan solar. A sakamakon haka, an wayi gari kasuwanci da sayar da solar panels ya karu fiye da ƙima, inda ake shigo da sabbin kayayyaki daga ƙasashen waje a kowane mako. Wannan bai zama alheri ba idan ana yin hakan ne bisa cutar da jama’a.

Yanzu haka, kowane yanki na ƙasar nan, daga Arewa zuwa Kudu, ana tallar solar panels, inverters, da baturori. Wannan ya nuna cewa akwai wata alaƙa tsakanin rashin wutar gwamnati da haɓakar kasuwancin solar. Idan aka bincika da kyau, za a ga cewa mutane sun daina sa ran samun wutar gwamnati saboda sun gaji da rashin tabbas, wanda ya sa suka rungumi solar da hannu bibbiyu. Amma idan akwai wata maƙarkashiya a bayan wannan, to lallai gwamnati ta sa baki.

Haka kuma, wannan matsala tana da illa mai tsanani ga tattalin arzikin ƙasa. Domin yawancin kayan solar da ake amfani da su ana shigo da su ne daga ƙasashen waje, wanda ke nufin kuɗin Najeriya na fita zuwa wajen ƙasa. Idan ma’aikatan lantarki suna da hannu a wannan maƙarƙashiya, to suna cutar da ƙasa ruɓi biyu, ta hanyar tozarta aikin gwamnati da kuma haifar da asarar tattalin arziki.

Akwai buƙatar hukumar samar da lantarki ta Najeriya, ta gudanar da cikakken bincike kan wannan zargi. Dole ne a tantance dalilin da ya sa wasu wurare ke zama cikin duhu na tsawon watanni, alhali ana karɓar kuɗin wuta a kowane lokaci. Idan aka gano akwai hannun wasu ma’aikata a wannan ɗanyen aiki, to wajibi ne a hukunta su domin zama izina ga sauran masu tunanin yin irin haka.

Haka kuma, gwamnati ta tarayya da ta jihohi su ɗauki matakai na gaggawa don gyara tsarin samar da wuta a Najeriya. Ya kamata a mayar da hankali wajen inganta kayan aiki, horar da ma’aikata da kuma tabbatar da cewa ana gudanar da aiki bisa gaskiya da amana. Bugu da ƙari, ya kamata a ƙarfafa bincike kan hanyoyin samar da wuta ta hanyoyin zamani ba tare da cutar da jama’a ko ƙasar gaba ɗaya ba.

Wannan batu na haɗin kai tsakanin wasu ‘yan kasuwar solar da baragurbin ma’aikatan lantarki ya kamata a ɗauke shi da muhimmanci. Idan gwamnati ba ta sa baki yanzu ba, to al’ummar Najeriya za su ci gaba da rayuwa cikin duhu, yayin da wasu ke tara dukiya bisa cutar jama’a. Gwamnati da kamfanin lantarki na Najeriya su tashi tsaye don gyara wannan lanari, su dawo da amincewar jama’a, kuma su tabbatar da cewa wutar lantarki ta zama haƙƙin kowa, ba kasuwanci na wasu mutane ƙalilan ba
_______________

Previous Post

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

Next Post

Taya Murna Ga Injiniya Muntari Sagir

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
Taya Murna Ga Injiniya Muntari Sagir

Taya Murna Ga Injiniya Muntari Sagir

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Shin Wai Akwai So? (1)

Shin Wai Akwai So? (1)

June 5, 2025
NO TO WAR

NO TO WAR

June 20, 2025
YAU TAKE SALLAH!

YAU TAKE SALLAH!

March 20, 2026
Buhari & Tinubu Era: Lingering Debt, Nigeria’s Woes and the Suffering Masses

Buhari & Tinubu Era: Lingering Debt, Nigeria’s Woes and the Suffering Masses

July 31, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.