• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, September 10, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Al’ummar Arewa Mu Farka

MUƘALA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
October 18, 2025
in Gizago
0
Al’ummar Arewa Mu Farka

Al'ummar Arewa Mu Farka

108
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Al’ummar Arewa Mu Farka
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Al’ummar Arewa Mu Farka


                                •••••••
Al’ummar Arewa na cikin wani hali da ke buƙatar farkawa da tunani mai zurfi. Shekaru da dama muna fama da matsalolin tsaro, talauci, jahilci da rashin cigaba. A yayin da sauran yankuna ke ci gaba da gina tattalin arzikinsu da bunƙasa rayuwar jama’a, mu a Arewa muna ci gaba da dogaro da gwamnati da kuma dogon tattaunawa kan batutuwan da ba sa kai ga ci gaba. Wannan ya sa ake samun giɓin da ke ƙara nuna bambanci tsakanin Arewa da Kudu a fannonin ilimi, fasaha, kasuwanci da sana’o’in dogaro da kai da sauran al’amuran rayuwa masu muhimmanci.

Related posts

Ayyukan Alheri Daga Gidan Amana

Ayyukan Alheri Daga Gidan Amana

September 5, 2026
Zuwa Ga Sanata Ahmad Babba Kaita

Zuwa Ga Sanata Ahmad Babba Kaita

September 4, 2026

Wani babban abin takaici, shi ne yadda mu a Arewa muka maida hankali kan gardaddami kan batutuwan addini, maimakon mu yi amfani da addinin wajen ƙarfafa haɗin kai da ƙoƙarin cigaba.

Kuma babban ma abin takaicin, ya tsaya ne inda za ka ga ana rikici kan lamarin addinin da bai da nasaba kai tsaye da rayuwar al’umma. Misali, za ka ji ana magana kan makomar al’ummar da suka gabata, ko a riƙa kutse zuwa lamarin iyayen Manzon Allah (saw) da sauransu. Wannan hali ya hana Arewa shiga sabbin hanyoyin bunƙasa rayuwa da fasahar zamani, kamar yadda sauran sassan ƙasar nan suke yi.

Idan muka duba al’ummar Kudu, za mu ga cewa sun maida hankali sosai wajen gina makarantun zamani, horar da matasa da ƙarfafa kasuwanci. Sun fahimci cewa ci gaban ƙasa ba ya zuwa da addu’a kawai, sai da aiki, fasaha, da jajircewa. Shi ya sa a yau, masana’antu, kamfanoni da cibiyoyin koyarwa da yawa suna can, alhali yawancin matasan Arewa na zaune babu sana’a, babu ilimi, babu burin samun cigaba a nan gaba.

Lallai kam lokaci ya yi da ya kamata matasa a Arewa su tashi daga barci, su daina zama cikin dogon jiran taimakon gwamnati ko ƙungiyoyi. Su fahimci cewa ba wanda zai zo daga waje ya gina musu rayuwa sai su da kansu. Su fara koyon sana’o’in hannu, su rungumi fasahar zamani, su yi amfani da intanet da dabaru wajen neman ci gaba. Duniya ta canza, kuma wanda bai tashi ba, zai ci gaba da zama a gefe yana kallon sauran suna tafiya.

Haka kuma, shugabannin Arewa, manya da ƙanana, ya kamata su daina yin siyasar raba kan al’umma, wacce ke haifar da gaba da ƙiyayya. Ya zama wajibi su daina amfani da addini, ƙabilanci da ɓangaranci wajen samun muradunsu na siyasa. Idan aka mayar da hankali wajen saka jari a ilimi, lafiya, noma, kasuwanci da tsaro, Arewa za ta dawo da martabarta. Amma idan muka ci gaba da dogaro da tunanin cewa “Allah zai yi” ba tare da mun yi ƙoƙari, mun yi aiki ba, to babu abin da zai canza.

Ya kamata malamai, mawaƙa, da ‘yan jarida su mayar da hankali wajen faɗakar da jama’a kan muhimmancin aiki da ci gaba. Kada su tsaya kan yin suka ko rikici kan finafinai da mawaƙa da ƙwallon ƙafa da sauran wasanni. Dole mu gane cewa addini da al’adu ba sa hana cigaba, sai dai suna tsara yadda za a same shi cikin tsari da mutunci. Idan muka yi watsi da wannan, Arewa za ta ci gaba da zama baya cikin al’umma, a wannan zamani na cigaba.

Wannan kira ne ga kowane ɗan Arewa, lallai ne mu farka daga dogon barcin da muke ciki. Mu daina ɓata lokaci kan batutuwan banza, mu tashi tsaye wajen gina makomarmu da ta ‘ya’yanmu. Arewa tana da albarkatu, tana da mutane masu ƙwarewa amma rashin haɗin kai da son zuciya ne suke hana ta ci gaba. Lokaci ya yi da za mu tashi, mu jajirce, mu farka, domin duniya ba ta raggo ba ce!

Jama’ar Allah, wace shawara za ku ƙara mana, domin mu gina al’ummarmu a wannan zamani na cigaba? Ku bayyana mana a Comment Section:
_______________

Previous Post

Neman Hanyar Gaskiya A Addini

Next Post

ABBANY RARA YA AMSA ƘALUBALEN NAZIRU

Related Posts

Ayyukan Alheri Daga Gidan Amana
Gizago

Ayyukan Alheri Daga Gidan Amana

September 5, 2026
Zuwa Ga Sanata Ahmad Babba Kaita
Gizago

Zuwa Ga Sanata Ahmad Babba Kaita

September 4, 2026
Tsakanin Maza Da Mata Wa Ya Fi Yawa A Duniya?
Gizago

Tsakanin Maza Da Mata Wa Ya Fi Yawa A Duniya?

August 13, 2026
Next Post
ABBANY RARA YA AMSA ƘALUBALEN NAZIRU

ABBANY RARA YA AMSA ƘALUBALEN NAZIRU

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Rusau A Kano: Ina Bayan Gwamna Abba Gida-Gida

Rusau A Kano: Ina Bayan Gwamna Abba Gida-Gida

June 4, 2023
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (5)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (5)

February 11, 2026
GOBARA DAGA KOGI: ‘Yan Bindiga Sun Farmaki Fadar Gwamnatin Amurka

GOBARA DAGA KOGI: ‘Yan Bindiga Sun Farmaki Fadar Gwamnatin Amurka

November 27, 2025
Nazari Da Sharhin Littafin “Sai An Yi Da Gaske”

Nazari Da Sharhin Littafin “Sai An Yi Da Gaske”

May 21, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai
  • Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?
  • SANATA BELLO MANDIYA: Mun Yi Babban Rashi – Gwamnan Katsina

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026
Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.