BAKIN JAƁA (5)
(Labarin Cin Amana)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

_______________
Jummalo ‘Yarkaka ta faɗa sahu na gaba cikin ƙalubalen rayuwa. A baya ta kasance ɗaliba a makaranta, inda ta riƙa sakarci da sunan ƙuruciya, bisa ɗaurin gindin mahaifiyarta. Daga bisani ta yi aure, inda ta ƙuduri niyyar rayuwa irin ta shagala a gidan miji, lamarin da ya zama kanwa uwar gamin rashin jituwa da mijinta. Kodayake shi ma taron kwara da ama ne, bikin ruwa ya iske sakaina. To, a yau ga ta a gidan iyayenta a matsayin matashiyar bazawara, ɗauke da cikin wata uku.
Babu shakka mahaifinta ya yi matuƙar baƙin ciki da wannan lamari na ɗiyarsa. Duk da cewa ya rabu da mahaifiyarta, amma lokacin da Jummalo ta yi aure, ya ɗan samu natsuwa, tare da fatan za ta kintsu, zai samu sauƙin kallon biri-boko da ‘yan uwansa suke masa. Amma sai ga shi ba a je ko’ina ba amma har igiyar aurenta ta tsinke. A yanzu ya sake dasa wani sabon fushi da ita.
A kan haka Jummalo ta ci gaba da zaman gida, kodayake zaman na raba-da-rabi ta riƙa yi, kasancewar ba ta jima ba ta fara fita yawace-yawacen da ta saba tun tana budurwa.
A kan haka wata rana sai ga shi sun haɗu da tsohon mijinta Mamman Big Boy a wani kulob. Ranar wata Asabar ce kuwa, wurin ya cika da matasa maza da mata. Wasu suna zaune a gaban tebura suna shaye-shaye da hirarraki, wasu kuma suna kan dandamali suna tiƙar rawa.
Mamman Big Boy yana zaune tare da abokansa a wani zagayayyen tebur, suna ta hira ba kama hannun yaro sai ga wani ya zo daidai kunnensa ya raɗa masa wata magana.
Nan da nan sai fuskarsa ta yamutse, kamanninsa suka canza, hankalinsa ya dugunzuma. Ya fara wani huci kamar baƙar kububuwa. Zunbur sai abokansa suka ga ya miƙe tsaye, yana ta waige-waige tare da nannaga kai kamar jangwalgwada. Su ma nan take suka miƙe, tare da tambayarsa ko lafiya?
Bai ba su amsa ba, sai dai suka ga ya dunƙule hannu, ya naushi tsakiyar teburin, ya buga wata irin gumza, ya ce “Nooooo…!” Gaba ɗaya kulob ɗin ya amsa, har muryar tasa ta saki wata amsa-kuwwa. Gaba ɗaya hankalin mutane ya dawo kan teburinsu. Sautin da ke tashi a saman dandalin rawa sai ya zama tamkar babu shi.
“Biggy, please, whats going on?” Ɗaya daga cikin abokan nasa ne yake tambayarsa, shi ma da alamar damuwa sosai a fuskarsa.
“No, a’a, ƙarya ne wallahi. Yau za a yi babbar bura’uba a kulob ɗin nan.” In ji Biggy, yana magana cikin kakkausar murya, hannunsa na dama a dunƙule, yana nannaga shi a cikin na hagu.
“Wai wancan ƙazamin gayen, ɗan gidan Dagacin ƙauye ne yake tare da my ex! Kai…wallahi ƙarya ne.”
Bai idasa maganar nan ba, sai suka ga ya fara tafiya, yana barin teburinsu zuwa wani teburi na daban da ke lungun yamma. Ya riƙa kutsawa tsakankanin tebura da kujerun da mutane ke zazzaune. Sauran abokansa kuwa ba su ga ta zama ba, sai suka take masa baya.
Bai tsaya ko’ina ba sai daidai wani teburi, inda wasu samari uku suke zaune, tare da mata uku – nufin kowa da tasa ke nan. Cikin matan kuma har da Jummalo, tsohuwar matarsa.
Mamman Biggy na isa bakin teburin, bai tsaya wata-wata ba, sai ya tsinka wa Jummalo mari. “Kutumar uban me ya kawo ki nan wurin?”
Gaba ɗaya samarin da ‘yan matansu sai suka miƙe tsaye, suna tambayar bahasi. Jummalo ce kawai ba ta tashi tsaye ba. Ta ci gaba da zama a kan kujerarta. Ta sanya hannu ta tallabe fuskarta tana rusar kuka.
Matashin da ke kusa da ita, wanda ga alama shi ne yake tare da ita, ya kalli Biggy ya ce masa: “Kai kuma me ya same ka ne za ka zo ka mari yarinya, ko kanka ya kwance ne?”
Yadda ka san kububuwa ta fasa kai za ta kai sari, haka Mamman ya koma. Kafin a yi aune har ya cakumi rigar wuyan saurayin nan ya shaƙe. Haka kuma ya haɗa da kai masa naushi a tsakanin hanci da idonsa na dama.
“Kutumar uban tsinin d+rin uwarka!” Tare da wani sabon naushin, Mamman yake zuba wannan ashar. Kafin ka ce kwabo, fuskarsa ta kumbura, ta fara zubar da jini.
Ganin haka, sai sauran matasan da ke tare da shi suka shiga rabawa. Nan take kulob ɗin nan ya hautsine. Tun da faɗan ya kaure sai DJ ya kashe sauti. Ba ka jin komai sai hayaniya, ana ta cece-kuce. Cikin lokaci sai aka ga wasu murɗaɗɗun ƙatti sun keto cikin mutane zuwa teburin da ake rigimar, suka ɗauki Mamman Biggy da shi matashin da suke faɗa. Haka ita ma Jummalo, ba a ƙyale ta ba. Tare aka fitar da su daga harabar kulob ɗin zuwa wani ɗakin masu gadi. Daga nan kuma sai ga jami’an ‘yan sanda, suka kwashe su sai ofishinsu.
(Za Mu Ci Gaba)
_______________













