• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, April 18, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Siyasa

KWANKWASO BAI CIKIN WAƊANDA SUKA KAFA APC

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 22, 2025
in Siyasa
0
KWANKWASO BAI CIKIN WAƊANDA SUKA KAFA APC

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

11
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

KWANKWASO BAI CIKIN WAƊANDA SUKA KAFA APC

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

•••••••
A wani saƙo da aka wallafa a shafin Buhari Reporters a Soshalmidiya, an bayyana cewa Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ba ya daga cikin ‘yan siyasar da aka kafa Jam’iyyar APC da su. Ga abin da sakon yake cewa:

Related posts

Najeriya 2027: Yadda ADC Za Ta Murƙushe APC

Najeriya 2027: Yadda ADC Za Ta Murƙushe APC

April 9, 2026
2027: SABUWAR GUGUWAR SAUYIN SIYASA A KANO

2027: SABUWAR GUGUWAR SAUYIN SIYASA A KANO

February 24, 2026

Ya mai girma Kwankwaso, gaskiyar magana ita ce, kai ba ka cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar APC. An kafa jam’iyyar kuma aka yi mata rijista a hukumance a shekarar 2013, sannan kawai zuwa ƙarshen shekarar 2014 ka shiga tare da Amaechi, Wamakko, Nyako da Saraki. Amma Mu’azu Babangida Aliyu da Sule Lamiɗo sun ƙi shiga, suka zaɓi ci gaba da zama a Jam’iyyar PDP.

Ga halastattun jigajigan ‘yan siyasar da suka kafa Jam’iyyar APC:
√ Muhammadu Buhari, GCFR – daga ɓangaren CPC
√ Bola Ahmed Tinubu, GCFR – daga ɓangaren ACN
√ Rochas Okorocha – daga wani reshe na APGA
√ Kashim Shettima, Bukar Abba Ibrahim, Ibrahim Shekarau, da Yariman Bakura – daga ɓangaren ANPP

Ya Kwankwaso, ba ka taɓa zama cikin jagororin da suka kafa APC ba. Ka shiga ne bayan dangantakarka da Jonathan ta lalace har ya kai ga ba za ka iya zama a PDP ba, kuma kana buƙatar wata mafita ta siyasa.

Duk da haka, babu wanda zai iya musanta muhimmancin shigowarka cikin APC. Ka bayar da gagarumar gudummawa wajen nasarar jam’iyyar, har ta kafa gwamnati. Amma idan aka zo ga batun kafa ta – ba ka cikin masu kafawa.

Sai dai kuma, an yi maka sakayya bisa ƙoƙarinka, domin ka zama Sanata, Mataimakinka da kuka daɗe cikin aminci, Gabduje ya lashe kujerar Gwamna a Jam’iyyar APC, sannan kashi 99% na ’yan Majalisar Tarayya da ta Dokoki, daga jiharka dukkaninsu amintattunka ne.
________________

Previous Post

Digirin Girmamawa: Ya Kamata Jami’o’in Najeriya Su Karrama Rarara

Next Post

ALLAH YA JI ƘAN ASP ALHAJI ƊAHIRU

Related Posts

Najeriya 2027: Yadda ADC Za Ta Murƙushe APC
Siyasa

Najeriya 2027: Yadda ADC Za Ta Murƙushe APC

April 9, 2026
2027: SABUWAR GUGUWAR SAUYIN SIYASA A KANO
Siyasa

2027: SABUWAR GUGUWAR SAUYIN SIYASA A KANO

February 24, 2026
Komawar Kwankwaso Zuwa APC: Gaba Kura Baya Sayaki
Siyasa

Abubuwan Da Za Su Iya Faruwa Idan Kwankwaso Ya Koma APC

September 28, 2025
Next Post
ALLAH YA JI ƘAN ASP ALHAJI ƊAHIRU

ALLAH YA JI ƘAN ASP ALHAJI ƊAHIRU

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Neman Hanyar Gaskiya A Addini

Neman Hanyar Gaskiya A Addini

October 17, 2025
ENDING BANDITRY AND KIDNAPPING IN THE NORTHWEST: WHETHER DIALOGUE IS THE ANSWER

ENDING BANDITRY AND KIDNAPPING IN THE NORTHWEST: WHETHER DIALOGUE IS THE ANSWER

February 6, 2025
Gwamnan Katsina Ya Taya Murna Ga Ganduje Da Sauran Shugabannin APC

Gwamnan Katsina Ya Taya Murna Ga Ganduje Da Sauran Shugabannin APC

August 6, 2023
Sasanci Da ‘Yan Bindiga: A Sake Duba Lamarin Nan A Tsanaki

Sasanci Da ‘Yan Bindiga: A Sake Duba Lamarin Nan A Tsanaki

October 13, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?
  • Mu Ji Tsoron Allah
  • Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

April 18, 2026
Mu Ji Tsoron Allah

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.