• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, January 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

BAKIN JAƁA (4)

Labarin Cin Amana

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 16, 2025
in Adabi
0
BAKIN JAƁA (4)

Bakin Jaɓa (4)

28
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

BAKIN JAƁA (4)
(Labarin Cin Amana)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

December 6, 2025
Bakin Jaɓa (4)


                      _______________
Alƙawarin farin wata, kwana goma ne. Haka ma abin ya kasance a zaman auren Jummalo da angonta Big Boy. Ƙyale-ƙyalen soyayyarsu ta gama walwali ne a cikin mako biyu kacal. Abubuwa ne masu yawa suka taru suka haddasa masu rashin jituwa.

Makon farko dai ya tafi sumul, inda suka ƙare shi cikin murna da shagulgula tare da abokai da ƙawaye. A cikin rana ta uku a mako na biyu ne al’amura suka fara canjawa.

Wata ranar Juma’a ce, kimanin ƙarfe biyar na maraice, Big Boy ya sha kwalliya irin ta ‘yan zamani. Faskacecen wando ne na jins yake sanye da shi. Sai kuma wata ɗangalallar riga mai ɗauke da zanen wani mawaƙin Amurka. Bisa kansa kuwa wata rantsattsar hular hana-salla ce, sai kuma ya lulluɓe ƙafarsa da wani farin kambas. Yayin da ya rufe fuskarsa ruf da baƙin tabarau kamar sabon makaho.

Fitowarsa daga uwar ɗaki, ya iske amaryarsa Jummalo a bisa kushin, tana kallon wasu mawaƙa suna sha’aninsu a faffaɗan allon talabijin, wanda ke liƙe jikin bango. Ya sanya hannu ya ɗauki ɗan mabuɗin motarsa da ke ajiye a bisan ƙaramin teburin da ke gabanta.

Hannunta akwai kwalin popcorn. Shi kuwa sai ya sunkuya, ya kama kwalin daga hannunta da leɓɓansa, ya ɗebi wani adadi na guggurun. “Yarinya, ni fa zan fasa… sai na dawo”

Abin da ya faɗa ke nan, a yayin da yake taunar guggurun, tare da juyawa ya yi wa ƙofar fita daga falon tsinke.

“Tsaya, tsaya… Biggy! Ban gane ba. Ina kuma za ka tafi ka bar ni nan ni kaɗai?”

A firgice Jummalo take wannan magana, tare da miƙewa tsaye daga kan kujerar da take zaune; bakinta a wangale cikin mamaki.

“Ba ki gane mene ba? Shin ba ki san cewa yau Jimmy yake bedday ba?” Mijinta ya ba ta amsa, kasancewar ta san Jamilu (Jully), wanda ajinsu ɗaya a sakandare kuma tana sane da cewa abokinsa ne.

“Kana nufin kai kaɗai za ka tafi, ni aikin me zan maka a nan?” In ji Jummalo, ta ƙara da cewa, “ko dai akwai wata ƙulalliya da kuke shiryawa a ƙasa?”

“Kai…!” Cikin wata fuska mai cike da ɓacin rai ya ambata wannan kalma. “Ke kuwa anya kin san matsayinki a yanzu? Da ke zan tafi fati cikin ƙattin ‘yan iska a kulob?”

“Haba Biggy, yau mene ne? Su ma ƙattin ai kowa da yarinyarsa zai je ko? To ina laifinka idan ka tafi da ni, amaryarka kuma masoyiyarka?

Ba ta jira shi ya ba ta amsa ba, sai ta miƙe zumbur ta nufin uwar ɗaki. “Ba ni minti biyu, ni ma in saka kayan da suka dace, sai mu rangaɗa.”

A wannan lokaci sai da suka yi ɓatatta. Ba Jummalo ce ta ƙyale mijinta ya fita ba, sai da ya kumbura mata fuska da mari. Ya kama gabansa ya fita, ya bar ta tana ta rusar kuka. Ba shi ya dawo gida ba, sai wanshekare da asuba.

Haka fa Biggy da Jummalo suka ci gaba da zaman aurensu a cikin ɗigirgire. Sun samu bambancin fahimta ta nesa da ta kusa. Dalili ke nan suka kasance kullum cikin rigima.

A yayin da Jummalo take son ta ga sun ci gaba da rayuwar jin daɗi, kamar yadda suke kafin aure, shi kuwa mijinta ya nuna mata cewa hakan ba za ta saɓu ba, wai bindiga a ruwa. A duk lokacin da ya ci kwalliya zai fita, sai ta tada masa hankali. Tana zarginsa da cewa idan ya je kulob, yana tarayya da wasu matan, kasancewar sauran abokansa, kowa yana da yarinya, domin babu wanda ya yi aure.

Haka a cikin rikicin yau da kullum har suka cika wata uku da aure. Iyayensu sun sha yin sasanci a tsakaninsu amma abin bai tsaya ba. Inda abin ya kai gargara da maƙura shi ne, wata rana da Jummalo ta kasa daurewa, ta matsa dole sai ta bi shi kulob.

Ranar wata Asabar ce da dare, Biggy da abokansa suna wajen raƙashewa, sai Jummalo ta bi shi. Ta kuwa yi mugun gani, domin ta same shi yana rawa a manne da wata budurwa. Bai yi aune ba sai dai ya ji saukar kwalba a kansa.

Kulob ya hargitse, sai kururuwa ake da iface-iface. Biggy dai ya farashe kwance cikin jini. A lokacin da aka kai shi asibiti a sume, ita kuma Jummalo a ofishin ‘yan sanda ta kwana.

Da ƙyar likitoci suka samo rayuwarsa, domin kuwa kwalbar nan da matarsa ta doka masa ta yi masa illa sosai. Kaifin kwalbar ya yanka masa kai da zurfi. Sai da ya kwashe mako uku a gadon jinya, sannan aka sallame shi.

A ranar da ya dawo daga asibiti, a ranar ya saki Jummalo. Da ma tun da ‘yan sanda suka sallame ta, gidansu ta yi wa tsinke. Kuma ƙarshen auren nasu ke nan. Sun rabu dutse hannun riga.

A cikin wannan aure da ya gaza cika wata uku, Jummalo ta samu shigar ciki. Lokacin da ya isa haihuwa, a gidansu ta haife shi. Ta haifi yaro, mai kama da ubansa. Jummalo – zaman jawarci salamun alaikum!

(Za Mu Ci Gaba)
_______________

Previous Post

TARON JIGAJIGAN KATSINA ALHERI NE

Next Post

Hukumar NDLEA Ta Kama Ɗan Indiya Da Muggan Ƙwayoyi Na Naira Biliyan 3.9

Related Posts

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)
Adabi

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine
Adabi

Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

December 6, 2025
Yau Take Juma’a: Allah Ka Albarkace Mu
Adabi

Yau Take Juma’a: Allah Ka Albarkace Mu

December 5, 2025
Next Post
Hukumar NDLEA Ta Kama Ɗan Indiya Da Muggan Ƙwayoyi Na Naira Biliyan 3.9

Hukumar NDLEA Ta Kama Ɗan Indiya Da Muggan Ƙwayoyi Na Naira Biliyan 3.9

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Gwamnan Jigawa Ya Kama Ma’aikatan Asibiti Suna Sayar Da Magungunan Gwamnati

Gwamnan Jigawa Ya Kama Ma’aikatan Asibiti Suna Sayar Da Magungunan Gwamnati

July 5, 2023
Buƙatarmu Mu Bunƙasa Rayuwar Mata, Matasa Da Kyautata Muhalli – Gwamnan Jigawa

Gwamna Namadi Ya Ladabtar Da Shugabannin Babban Asibitin Gumel

August 1, 2023
Taya Murna Ga Manaja Isma’il A. Sanda

Taya Murna Ga Manaja Isma’il A. Sanda

October 16, 2025
GIRO ALLAH KYAUTA MAKWANCI

GIRO ALLAH KYAUTA MAKWANCI

September 6, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation
  • Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco
  • Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026
Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

January 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.