Mummunar Zanza-Zanga A Ƙasar Nepal
Daga Wakilinmu

__________
Rahotanni daga ƙasar Nepal sun tabbatar da cewa matasa ‘yan bana-bakwai, waɗanda ake wa laƙabi da “Gen Z” sun gudanar da zanga-zanga mai ƙarfi, inda suka ƙalubalanci gwamnati saboda hauhawar almundahana da dukiyar gwamnati, cin hanci da rashawa da zalunci, rashin ayyukan yi ga matasa da kuma takunkumin da aka sanya wa kafofin sada zumunta; kamar yadda Jaridar The Times of India ta ruwaito.
A sakamakon taɓarɓarewar tsarin mulkin dimokuraɗiyya, wasu ɓangarorin al’umma a ƙasar sun nuna buƙatar a koma tsarin mulkin sarautar gargajiya.
A yayin da zanga-zangar ta yi tsanani, ta haddasa Firaministan Nepal, K.P. Sharma Oli ya yi murabus. Al’amura sun hargitse a birnin Kathmandu. An kuma sabya dokar hana da zirga-zirga a wasu wurare.
An rufe wasu ofisoshi, wasu gine-ginen gwamnati sun ƙone, wasu jama’a sun samu raunuka. Haka kuma an tarwatsa wasu gidajen yari, inda ɗaruruwan fursunoni suka tsere.
Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum, musamman a Najeriya sun ja hankalin shugabanni da su tashi tsaye wajen gyara al’amura, domin hana faruwar irin haka a ƙasashensu.
__________














Ma sha Allah Laakuwwata illah billah 😍, muna addu’ar Allah yakawo sanadin faruwar haka a Najeriya.