• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, March 8, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Shanshani

KAMUN LUDAYIN JEMAGE

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 16, 2023
in Shanshani
0
KAMUN LUDAYIN JEMAGE

Tsohon Shugaban Ƙasa, Obasanjo a Fadar Ooni na Ife, kwanakin baya

237
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Mukhtar Mudi Spikin

Kamun Ludayin Jemage

Related posts

SABON ZUMUNCI: KWANKWASO DA GANDUJE SUN YI SULHU

SABON ZUMUNCI: KWANKWASO DA GANDUJE SUN YI SULHU

December 22, 2023
KAMUN LUDAYIN JEMAGE

KAMUN LUDAYIN JEMAGE (26-08-2023 da 02-09-2023)

September 2, 2023

Salwa salihar tsuntsuwa ta ce “Rawar Jemage ta yi kama da ta Babba-Da-Jaka, sun san hanyar ƙuntata wa tsuntsaye, amma kamar ba su san hanyar kyautatawa da sauƙaƙawa tsuntsaye ba, Kaico!”

Kurciya ta ce “Lamarin dai masu mulkin tsuntsayen dajin nan sai addu’a kurum. Wai kuna da labarin cewa Jemage ya shirya tsaf zai fara raba sulalla takwas-takwas a sheƙar tsuntsaye miliyan sha biyu har tsawon wata shida don a rage wa tsuntsaye raɗaɗin cire tallafin ruwan sinadiri? Ina hikima a nan? To bayan wata shida shi sai a dawo gidan jiya ke nan ko me?”

Hazbiya ta kada baki ta ce “To yanzu ni da nake da ‘ya’ya sha biyu a sheƙata, me sulalla takwas za su yi min? Kawai dai an shiryo wata hanyar wawashe sulallan dajin nan ne kurum.”

Kanari ta ce “Wai kun ji su Ragon-Maza ma neman ƙarin sulalla suke ko? Wai sulallan da ake ba su a majalisa sun yi kaɗan. Tun da su masu uwa a bakin murhu ne, har an sahale za a ƙara musu sulalla malala gashin tinkiya, mu kuma tsuntsaye mu je mu mutu ko?”

Alhudahuda, wanda tun da aka fara magana bai ce komai ba, ya kalli tsuntsaye ya ce “Duk wannan maganganun da kuke yi, su Jemage da muƙarrabansa sun sani, sun san wannan hanyar da suka ɗauka ta ƙarya ce, amma fa suna sane, a kullum suna nuna wa tsuntsaye cewa su ɗin ba su da basirar warware matsaloli yadda ya kamata ne don ai ta cece-kuce, a duk shirmen nan faɗa mun abu ɗaya da suke yankewa, wanda zai cutar da su? A kodayaushe sai dai su kawo tsarin da zai cutar da mu!”

Cikin takaici, sai Hudahuda ya kece da ruwan Turanci kamar Gwamna Gwalangwam. Ko me yake nufi? Oh o’o, ga dai abin da na jiyo yana faɗa:

“The elaborate act of our leaders masquerading as fools constitutes a Machiavellian stratagem that pervades the pages of history. By adeptly donning this cloak, they adroitly divert attention, manipulate public perception, and evade the very essence of accountability.”

Da yawan tsuntaye dai jikinsu ya yi sanyi daga yadda Jemage ya fara kamun ludayinsa.
~~~~~~~
Mukhtar Mudi Sipikin,
15-07-2023.
~~~~~~~~

Previous Post

Gwamnatin Tinubu: Tallafin ₦8000 Ba Zai Yi Tasiri Ba!

Next Post

Dogo Na Magayaƙin Kano Ya Angwance

Related Posts

SABON ZUMUNCI: KWANKWASO DA GANDUJE SUN YI SULHU
Shanshani

SABON ZUMUNCI: KWANKWASO DA GANDUJE SUN YI SULHU

December 22, 2023
KAMUN LUDAYIN JEMAGE
Shanshani

KAMUN LUDAYIN JEMAGE (26-08-2023 da 02-09-2023)

September 2, 2023
KAMUN LUDAYIN JEMAGE
Shanshani

KAMUN LADUYIN JEMAGE (19-08-2023)

August 20, 2023
Next Post
Dogo Na Magayaƙin Kano Ya Angwance

Dogo Na Magayaƙin Kano Ya Angwance

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

ABBANY RARA YA AMSA ƘALUBALEN NAZIRU

ABBANY RARA YA AMSA ƘALUBALEN NAZIRU

October 18, 2025
Abin Da Ya Sa Na Naɗa Mataimaka 85 – Ciyaman Mukhtari City

Abin Da Ya Sa Na Naɗa Mataimaka 85 – Ciyaman Mukhtari City

September 18, 2025
KISAN MAWAƘI MOHBAD: Darasi Da Jan Hankali G Al’ummar Arewa

KISAN MAWAƘI MOHBAD: Darasi Da Jan Hankali G Al’ummar Arewa

September 22, 2023
Ɗan Iyan Galadiman Katsina Emerges Chairman of Arewa Consultative Forum

Ɗan Iyan Galadiman Katsina Emerges Chairman of Arewa Consultative Forum

June 19, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • RAMADAN KARIM: 19-1447
  • FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
  • RAMADAN KARIM: 18-1447

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

RAMADAN KARIM: 19-1447

RAMADAN KARIM: 19-1447

March 8, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.