• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, May 12, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

BAKIN JAƁA (2) (Labarin Cin Amana)

LABARIN GASKE

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 2, 2025
in Adabi
0
BAKIN JAƁA (2) (Labarin Cin Amana)

Bakin Jaɓa-2

61
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

BAKIN JAƁA (2)
(Labarin Cin Amana)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
Bakin Jaɓa-2


_______________
Abubuwa ne da yawa suka taru suka haddasa wa Jummalo ‘Yarkaka tsintsinar tsiya. Waɗannan kuwa sun haɗa da irin tarbiyyar da ta samu tun daga ƙuruciyarta. Yarinya ce da mahaifiyarta ta sangarta, ta riƙa shagwaɓa ta. Ta taso cikin tsageranci da raina mutane, kamar kuma yadda ta koyi kwaɗayi da son abin duniya. Uwa uba kuma ta siffatu da munanan halayen da suka haɗa da ƙarya, yaudara, ha’inci da kuma cin amana.

Tun lokacin da Jummalo take makarantar sakandare idanuwanta suka buɗe da duniyanci. Kasancewar makarantar jeka-ka-dawo ce ta yi. Wannan ya ba ta damar yin ƙawance da maza, abokan karatunta.

Tun daga aji ɗaya har zuwa shida, ba za ka taɓa ganin tana ƙawance da mata ‘yan uwanta ba, sai maza. Ko a cikin aji, ko a filin shaƙatawa – cikin ɗalibai maza take sha’aninta. Tana daga cikin ƙungiyar dirama ta makarantarsu, inda ta yi suna sosai. Duk inda ta gitta, za ka ji ɗalibai suna kirara sunanta – ‘Yarkaka!

Mahaifinta ya yi iya ƙoƙarinsa wajen saita mata tarbiyya, amma inda gizo ke saƙar shi ne, mahaifiyarta. A duk lokacin da ya yi yunkurin tarbiyantar da Jummalo, mahaifiyar kan nuna fushi, har ma sukan samu saɓani da juna. Shi kuwa mutum ne mai sanyin zuciya. Sannu a hankali har ta ci ƙarfinsa, ya daina sa bakinsa – duk abin da yarinyar ta aikata bai da ikon ya tanka. Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da suka sanya wata rana igiyar aure ta datse tsakanin mahaifan nata.

Wata rana ce aka wayi gari Jummalo ba ta kwana gida ba. Shi dai mahaifinta ya ga lokacin da za ta tafi makaranta da safe, tana sargafe da jikka. Ta gaishe shi, har ma ya kawo kuɗin kashewa ya ba ta. Lokacin da ya dawo gida kimanin ƙarfe biyar na marece, bai ga Jummalo ba, wacce ta kamata ta dawo tun ƙarfe biyu zuwa uku na rana.

“Ni kuwa ina ‘Yarkaka, ko har yanzu ba ta dawo daga makaranta ba?” Mahaifinta ne yake tambaya amma ko gezau matar tasa ba ta yi ba. Sai da ya maimaita magana kusan sau uku, sannan ta amsa masa magana cikin fushi.

“Don Allah ka bar ni in sarara!” In ji mahaifiyar Jummalo. “Idan da ta dawo ba za ka gan ta ba? Ko kuwa ita jaririya ce da zan goya ta a baya?”

Wannan al’amari ya ɗaure masa kai. Kawai daga tambaya, sai cibi ya zama ƙari? Kodayake in da sabo, ya saba da irin wannan wulakancin. Saboda haka bai sake furta komai ba. Ya fitar harkar matar tasa gaba ɗaya. Har zuwa dare, ƙarfe 12, bai ga Jummalo ko alamarta ba. Haka kuma mahaifiyarta ba ta ƙara kula shi a kan batun ba. Dalili ke nan ya fahimta da cewa, koma yaya aka yi, ta san inda Jummalo ta maƙale daga makaranta.

“Babu shakka da walakin, wai goro cikin miya.” Abin da ya furta ke nan shi kaɗai, a lokacin da yake kulle gida. “Da ba ta san inda take ba, da yanzu hankalinta ya tashi.”

A ransa, ya sanya tsammanin Jummalo tana gidan kakarta, domin wani lokaci takan je can ta kwana, ba tare da ta sanar da shi ba. Hasali ma, akwai alaƙar shaƙuwa sosai tsakaninta da kakar tata. Ita ma ta taka rawa sosai wajen sangarcewar ta. Saboda yadda take tarairayarta, shi ya sa ake mata laƙabi da ‘Yarkaka.

Da safe misalin ƙarfe goma, mahaifin Jummalo ya ji wasu matasa suna sallama a ƙofar gidansa. Ya amsa, ya fita. Yana zuwa sai ya iske wata ƙaramar mota a tsaye bakin ƙofar gidan nasa. Matasa biyu suna a bayan motar, suna riƙe da Jummalo, wacce ba ta cikin hayyacinta.

Matasa biyu da ke zaune a gaban motar ne suka fito da sauri suka tarbi mahaifin nata. Bayan sun gaishe shi, nan take suka labarta masa abin da ya faru. Kafin ma ya saurare su, sai da ya gama nazarin yanayinsu, inda ya fahimci dai ba yaran kirki ba ne. Kowanensu yana sanye da ɗagaggar riga. Sun sassauko da wandunansu ƙasan mazaunai. Kansu kuwa da ya duba, wani irin aski ne na Allah-tsine – gashi ya yi cirko-cirko kamar sheƙar tsuntsaye.

“Subhanallahi…!” Mahaifin Jummalo ya tunkari bayan motar, ya kalli ‘yarsa ta langaɓe a jikin kafaɗun matasan.

“Me ya faru da ita…?” Abin da ya faɗa ke nan, yayin da ya janyo murfin motar da matasan suka turo kaɗan. Bai tsaya sun ba shi amsa ba, kawai ya riƙo hannayenta. Ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin fitowa daga motar amma ta koma rakwab ta zauna kan cinyoyin matasan biyu.

“Baba, sai dai fa ka yi haƙuri…” in ji ɗaya daga cikin matasan, yana magana cikin maye. “Wallahi baba, damun kauri ta sha. Tun jiya take barci.”

A daidai lokacin ne mahaifiyarta ta leƙo, dalilin hayaniyar da ta ji ana yi. Yaran unguwa sun baibaye ƙofar gidan, suna kallon abin mamaki. A haka suka cicciɓi Jummalo, suka shigar da ita gida.

Daga bisani ne dai baban Jummalo ya gano kan al’amarin. Ashe waɗannan matasa, makarantarsu ɗaya da ita. Saurayinta ne wai ya shirya liyafar zagayowar ranar haihuwarsa. Dalili ke nan suka kwana suna cashewa a wani keɓaɓben wuri da suka tanada, inda suka yi shaye-shayen kayan maye.

A tsawon ranar nan, ba a samu kwanciyar hankali ba a gidan su Jummalo. Takaici ya cika ran mahaifinta, musamman ganin yadda ɗiyarsa ta kama hanyar lalacewa. Nan da suka yi ta musayar miyau tsakaninsa da matarsa. Al’amarin ya ta’azzara, inda ta kai ga nan take ya rubuta mata saki – aure ya rabu.

(Za a ci gaba)
_______________

Previous Post

Dokta Bukar Usman, Sarkin Daura Da Bikin Ranar Hausa Ta Duniya

Next Post

SASSANYAN AMINCI (1)

Related Posts

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana
Adabi

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza
Adabi

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Next Post
SASSANYAN AMINCI (1)

SASSANYAN AMINCI (1)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

An Ƙarfafa Ƙawance Tsakanin Jigawa Da Zinder

Ambaliya: Gwamnan Jigawa Ya Nemi Tallafin Bankin Duniya

July 8, 2023
MENE NE SO?

MENE NE SO?

April 27, 2025
KAMUN LUDAYIN JEMAGE

KAMUN LADUYIN JEMAGE (19-08-2023)

August 20, 2023
Taya Ni Mu Gyara: Kisan Baƙi Sai Gayya

Taya Ni Mu Gyara: Kisan Baƙi Sai Gayya

November 1, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)
  • Malumfashi An Yi Babban Rashi
  • Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)

May 12, 2026
Malumfashi An Yi Babban Rashi

Malumfashi An Yi Babban Rashi

May 11, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.