• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, May 18, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Addini

YADDA NA ƊAUKI SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA

TSOKACI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 19, 2025
in Addini
1
YADDA NA ƊAUKI SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA

A hagu, Sheikh Yakubu Yahaya Katsina da Bashir Yahuza Malumfashi a dama

39
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

YADDA NA ƊAUKI SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
A hagu, Sheikh Yakubu Yahaya Katsina da Bashir Yahuza Malumfashi a dama

 

Na daɗe ina bibiyar harkokin Malam Yakubu, musamman ma lokacin da nake aiki a Katsina, a tsakanin shekarun 1990. Yana daga cikin malamai mabiya mashabar Shi’a da nake gani da ƙima.

Akwai dalilai masu tarin yawa da suka sanya yake burge ni. Wasu daga cikin dalilan su ne, shi malami ne mai ILIMI, kuma da ilimin yake aiwatar da nasihohinsa da karatuttukansa. Madamar za ka saurare shi, to tabbas za ka fahimci karatunsa kuma za ka gane cewa ba kame-kame yake ba (irin wancananka).

Wani dililin da ya sa yake burge ni shi ne, yana da son zaman lafiya. A tsawon kasancewarsa shugaba a Jihar Katsina, ba a cika samun hatsaniya tsakaninsa da gwamnati ko mutanen gari ba. Wannan kuma ya samu ne saboda nagartar shugabancinsa.

Haka kuma Malam Yakubu yana da haƙuri da hangen nesa matuƙa. Yana nuna dattako a cikin lamurransa. Misali, ko a kwanakin baya da matar Zakzaky da magoya bayanta suka yi ta yi masa tijara da tozarci, bai ɗauki al’amarin da zafi ba. Ya riƙa bin abin cikin hikima.

Da a ce shi ba dattijo ba ne, lallai da ya biye wa mabiya an yi “ƁATATTA” tsakaninsa da Iyalan Sheikh Zakzaky. Amma ya jure wa cin kashin da suka yi ta yi masa. Yara sun riƙa shiga Soshalmidiya suna yi masa shaguɓe da waƙoƙin zambo, wasu ma har da zage-zage. Amma ko a jikinsa. Ya jure, saboda haƙurinsa da tsinkaye mai kyau.

Waɗannan halaye nasa nagartattu, su ne ma suka sanya, a lokacin da “MAJIYATA” ta sanar da ni cewa zai je GAISUWAR BUHARI DAURA, na amince da cewa lallai zai iya. Domin kuwa shi mutum ne mai jin ƙai da yafiya. Kuma shi ya san irin tasiri da alfanun da ke akwai ga mutumin da ya MAIDA ALHERI GA MUGUNTA. Ya san haka halayen Manzon Allah (saw) ne. Babu wanda zai zama mai yafiya, mai biyar wanda ya yi masa sharri da alheri, sai nagartaccen mutum mai koyi da Manzon Allah.

Wannan dalili ne ya sanya ko kaɗan ban yi mamaki ba, lokacin da na samu labarin cewa zai je Daura. To, amma komai sai Allah ya yarda, don haka bai samu zuwa ba. Amma tabbas na kyautata masa zato.

Malam Yakubu Yahaya Katsina – ina yi maka fatan alheri, tare da addu’ar Allah ya ƙara maka ilimi da fahimtar gaskiya.
__________
Bashir Malumfashi, Editan Mujallar Taskar Gizago (online)

Previous Post

WILL ATIKU’S EXIT FROM THE PDP BRING HIM VICTORY IN 2027?

Next Post

SHUGABA BUHARI: TA’AZIYYAR JAN GWARZO

Related Posts

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447
Addini

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
Duniya Ba Gidan Zama Ba
Addini

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Mu Ji Tsoron Allah
Addini

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026
Next Post
SHUGABA BUHARI: TA’AZIYYAR JAN GWARZO

SHUGABA BUHARI: TA'AZIYYAR JAN GWARZO

Comments 1

  1. hayatu nura says:
    8 months ago

    Slm wallahil azem kaibakadauki mal.yaqub yahya(h)da mutunciba saboda naga bakakaunar malaminsa da iyalansa amma abintambaya yaushenekaji iyalan malam sunyima shaik yakubu wulaqanci? Allah yatadaka ranar shaida gobe qiyama dukwannan maganganun dakai nakaiwa mal.yakubu yagani ajiya kuma yafada cewar kai maqiyin harkane kuma munacigabada addua.kanku allah rusame qarya kai malam kabincika tarihi dukwani maqiyin malam zakzaky baici nasara kansaba tundaga yan tawayiyya yan zuhudu gwamnati kuma tun abacha izuwayau malam yaga bayansu barekai qaramin shedan inatausayinka amma bakinka zayajawomaka ruwan dafakanka

    Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

General Buratai Wears New Status As Patron of Institute of Security…

General Buratai Wears New Status As Patron of Institute of Security…

November 24, 2024
Ba Mu Goyon Bayan Juyin Mulki Kuma Ba Ma Goyon Bayan Yaƙi Da Niger

Ba Mu Goyon Bayan Juyin Mulki Kuma Ba Ma Goyon Bayan Yaƙi Da Niger

August 5, 2023
BIU: A Visit to a City on a Plateau (2)

BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (2)

December 13, 2023
Yan Bindiga Sun Sako Miji Da Matarsa Bayan An Biya Naira Miliyan 50

Yan Bindiga Sun Sako Miji Da Matarsa Bayan An Biya Naira Miliyan 50

September 18, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki
  • Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447
  • ALHAMDU LILLAH

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki

Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki

May 18, 2026
Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.