• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, July 27, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Burina In Samar Da Maslaha Tsakanin Ma’aurata – LIKITAR MA’AURATA

Binta Tukur by Binta Tukur
August 8, 2023
in Adabi
0
Burina In Samar Da Maslaha Tsakanin Ma’aurata – LIKITAR MA’AURATA

Malama Zuwaira Dauda Kolo

103
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Burina In Samar Da Maslaha Tsakanin Ma’aurata – LIKITAR MA’AURATA

Daga Binta Tukur 

Related posts

Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage

Nazari Da Sharhin Littafin Tarihin Garin Lassa

July 18, 2026
Maryam ‘Yar Aljanna (2)

Maryam ‘Yar Aljanna (2)

June 22, 2026
Malama Zuwaira Dauda Kolo

~~~~~~~
Malama Zuwaira Dauda Kolo, marubuciya ce da ta sha bamban da gamagarin marubuta. Baya ga kasancewarta Ma’aikaciyar Lafiya, ta kasance kuma Malamar Sassaita Matsalolin Ma’aurata. A tattaunawarta da BINTA TUKUR, ta bayyana irin gwagwarmayar da take sha a fagen rubuce-rubuce da kuma tagomashin da take samu. Ga bayanan Likitar Ma’aurata:
~~~~~~~

TG: Kina ɗaya daga cikin manyan marubutan Hausa, ko za ki gaya mana tarihinki a taƙaice?

ZUWAIRA: Sunana Zuwaira Dauda Kolo. NI haifaffiyar garin Jos ce, ma’aikaciyar lafiya. A yanzu haka ina Jami’ar Jos, inda nake ƙara karatu kan aikin nawa, domin sake samun ƙwarewa.

TG: Tun yaushe kika fara rubutu kuma mene ne ya ja ra’ayinki ga harkar rubuce-rubuce?

ZUWAIRA: Na fara rubutu a shekarar 2005 amma ban buga littafi ba sai a 2007, sannan ya shiga kasuwa.

Abin da ya ja hankalina na fara rubutu, gaskiya a lokacin yana da nasaba da karance-karancen da nake yi, wanda ta kai har na fara sha’awar ni ma a ce na samar da wani ɗan kundi da zai aika saƙo ga al’umma kuma musamman kan abin da ya shafi zamantakewa. Cikin hukuncin Allah kuma sai ga shi ina fara gwadawa sai abin ya riƙa tafiya yadda ake so.

TG: Ya zuwa yanzu, littattafai nawa kika rubuta? Guda nawa aka buga a littafin takarda kuma nawa kika buga a intanet?

ZUWAIRA: Na rubuta littattafai da dama gaskiya kuma kusan duk an buga su. Littattafan sun haɗa da kamar su Mardiyya, Bulalar Zuciya, Taya In Mu Gyara, Ƙanin Ajali da sauransu.

Littattafai a internet kuwa ai ba za su ƙirgu ba, tun da kusan kullum akan hakan ake.

TG: Waɗanne irin matsaloli kike fuskanta a matsayinki na marubuciya, musamman ma a soshalmidiya?

ZUWAIRA: Matsaloli ba zan iya cewa ga su ba, sai dai ba za a rasa ‘yan ƙananan ƙalubale ba gaskiya, musamman wani post ɗin da in ka yi wasu kan nuna ka goyi bayan wani ɓangare, a dinga ƙoƙarin sai an taɗe ka. To amma hakan dai ba zai hana mu yin abin da muka kan yi ba.

TG: Tun daga fara rubutu, waɗanne irin nasarori kika samu ko kuma akasin su?

ZUWAIRA: Gaskiya ni kam a yanzu ba zan iya lissafta nasarorin da na samu ba, domin suna da yawa. Abubuwan da ban taɓa tunanin samu ba na samu, garuruwan da da sai dai na ji su a labari sanadin rubutu na je su, mutanen da ban tunanin haɗuwa da su ba ko a mafarki, Alhamdu lillahi, na haɗu da su. Mu da rubutu sai dai mu ce Alhamdu lillah.

TG: A harkar rubuce-rubuce, waɗanne marubuta ne gwanayenki, da kike koyi da rubutunsu?

ZUWAIRA: Akwai irin su Rahma Abdulmajid, Maryam Kabir Mashi, Sadiya Garba Yakasai. Maimuna Idris Sani Beli, Fauziyya D. Sulaiman, KMashi da sauransu.

TG: Baya ga harkar rubutu, kin tsunduma cikin harkokin tallafa wa al’umma don inganta zamantakewar aurensu. Ta yaya kika faro wannan kuma ko za ki yi mana cikakken bayani game da babban ƙalubalen wannan aiki?

ZUWAIRA: Dama mu kullum cikin hidimar al’umma muke, musamman kasancewata ma’aikaciyar lafiya, hakan ya sa ina da alaƙa sosai da mutane. Wani yadda zai zauna ya faɗa maka matsalarsa da neman shawararka to ta hakan ake ƙoƙarin nema wa mutane mafita, wanda ta hakan ma aka fara gaskiya. Sai fatan Allah Ya ba mu dacewa.

TG: Kina daga cikin marubuta, me za ki ce game da haka?

ZUWAIRA: Na gode wa Allah da na tsinci kaina cikin marubuta, domin marubuci wani madubi ne cikin al’umma, wanda duk wanda Allah Ya yi masa wannan baiwar, yana iya samar da abin da zai iya canja al’ummar da ta kauce hanya ta hanyar rubutu.

TG: Mene ne babban burinki dangane da rubutu da kuma zamantakewar aure?

ZUWAIRA: Babban burina a rubutu, na ɗore da saƙon da nake aikawa kuma ma’auratan su ci gaba da fahimtata suna samun daidaito tsakaninsu. Ina son ma’aurata su karɓi rayuwar aure a duk yadda ya zo musu. Komai na rayuwa ɗan hakuri ne, dama kusan haƙurin ne a cikin aure.

TG: Ko kina da wani kira ga gwamnati da marubuta ‘yan uwanki da kuma al’umma masu karanta littattafanki da sauran al’ummar da kike ba shawarwari?

ZUWAIRA: Ina kira ga gwamnati, da ta dinga saka marubuta cikin ƙusoshin gwamnati, domin suna da gudunmawar da ya kamata su bai wa al’umma ta hannun gwamnati. Ga makaranta masoyanmu kuwa, ina kira da su ci gaba da haƙuri da bibiyar rubutunmu. Inda aka ga mun yi kuskure kuma a gyara mana don Allah.

Previous Post

Abdullahi Garba Faskari Ne Sabon Sakataren Gwamnatin Katsina

Next Post

SHIRIN FIM: Furodusa Nafseen Ya Shirya Taron Fitattun ‘Yan Wasa

Related Posts

Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage
Adabi

Nazari Da Sharhin Littafin Tarihin Garin Lassa

July 18, 2026
Maryam ‘Yar Aljanna (2)
Adabi

Maryam ‘Yar Aljanna (2)

June 22, 2026
Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa
Adabi

Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa

June 21, 2026
Next Post
SHIRIN FIM: Furodusa Nafseen Ya Shirya Taron Fitattun ‘Yan Wasa

SHIRIN FIM: Furodusa Nafseen Ya Shirya Taron Fitattun 'Yan Wasa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

A Yayin Da Taron Katsina Facebook Connect Ke Ƙaratowa

A Yayin Da Taron Katsina Facebook Connect Ke Ƙaratowa

October 25, 2025
Matsalolin Tsaro: Ƙungiyar ‘Yan Jarida Ta Arewa Ta Shirya Taron Neman Mafita

Matsalolin Tsaro: Ƙungiyar ‘Yan Jarida Ta Arewa Ta Shirya Taron Neman Mafita

November 7, 2025
The Bloomsbury Handbook of Muslims and Popular Culture: An Endorsement

The Bloomsbury Handbook of Muslims and Popular Culture: An Endorsement

October 19, 2023
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (2)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (2)

January 23, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today
  • Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
  • Saƙon Godiya Da Bangajiya

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

July 25, 2026
Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.