• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, March 5, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (8)

MUƘALA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 10, 2025
in Gizago
0
ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (8)

Ƙungiyar Hausawa Zalla: Alheri Ko Sharri? (8)

65
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (8)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

March 1, 2026
#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

February 23, 2026
Ƙungiyar Hausawa Zalla: Alheri Ko Sharri? (8)

 

__________

Shin Wane Ne Bahaushe Zalla A Yau?

Jama’a masu bibiyarmu a wannan muƙala, a wannan karon za mu duba wannan tambaya ta sama mai cewa, shin a wannan zamani da muke ciki na ƙarni na 21, bisa la’akari da gamewa da dunƙulewar duniya zuwa wata ‘yar tsukakkiyar da’ira, wane ne za a duba, tashi ɗaya a kira shi da Bahaushe zalla?

Me ya kawo wannan tambaya? Babban dalilinta, shi ne yadda a yau muka wayi gari da ɓullowar wata bahaguwar ƙungiya, mai zimmar dawo da hannun agogo baya, wacce ta ɓoye da kishin Hausawa amma a gefe ɗaya kuma take ƙunshe da wani mugun nufi mai haɗarin gaske ga zamantakewar al’umma.

A yau dai, duk inda ka duba al’ummar Arewacin Najeriya, aƙalla za a iya cewa cikin mutum goma, guda tara da Hausa suke magana (sosai) duk kuwa da cewa asalinsu ba Hausawa ba ne, suna da yarukansu na asali. Kada mu mance, a Arewacin Najeriya, akwai yaruka iri daban-daban fiye da 300.

Wani abin da zai ba ka mamaki shi ne, wasu yarukan ma, tuni Hausa ya haɗiye su. Masu yaren, musamman ‘ya’yansu da jikoki, ba su iya ko gaisuwa ba da yaren nasu na gadon asali – sai dai Hausa. A Arewa, kusan kowa BAHAUSHE ne ta fuskar yare na zahiri. Idan da za ka samu Bafillace ko Babarbare ko Buzu da sauransu, waɗanda kakanninsu ba su iya Hausa ba, amma a yau da ka tambaye su batun yare, za su ce maka su HAUSAWA ne – saboda ba su da wani yare da suka iya idan ba Hausar ba.

Haka al’amarin yake a ƙasashe da dama, musamman a Afirka ta Yamma, ƙasashe kamar Nijar, Ghana, Kamaru, Chadi da makamantansu. Kusan duk wanda ka ji yana magana da Hausa, aƙalla yana da wani yare nasa na gado – amma bai iya ba, Hausa ta ƙwace shi.

To, a nan za mu dawo kan batun baya, shin me ya sa masu ƙumajin HAUSAWA ZALLA suke ƙulafuci da kafa ƙahon zuƙa ga Fulani kawai, har ma suna aibata Shehu Ɗanfodiyo? A nan za mu fahimta da cewa, da biyu, wai an bugi biri da rani. Kada mu manta, idan dai don kishin Hausawa ne, to ai kamar yadda lamarin yake a zahiri – kusan kowa Bahaushe ne a yau, musamman a Arewa. Amma me ya sa ake taƙaita batun tsakanin HAUSAWA da FULANI? Amsa guda ɗaya ce – ana son hargitsa al’ummar Arewa. Ana son dasa gaba da ƙiyayya masar dalili tsakanin al’ummar Arewa.

Haka kuma idan dai domin samar da haɗin kai da taimakon al’umma ne ya sa suke wannan haƙilo, to ai a wannan zamanin ba da makamin ƘABILANCI za a bi ba, domin kuwa akwai wani babban jigo mai matuƙar tasiri, wanda tun farko shi ne ya haɗa kan al’umma kuma shi ne ma ya haɓaka da inganta ɗabi’un Hausawa da Fulani da ma duk wanda ya rungume shi, wato ADDININ MUSULUNCI.

Me ya sa na ce Addini ya fi Ƙabilanci tasiri? Tun farko kusan duk Bahaushen da ka samu a Arewacin Najeriya, Musulmi ne – ƙalilan ne suke cikin wani addini na daban. Haka kuma kusan duk Bafulatanin da ka gani, Musulmi ne, sai ƙalilan su ma da suke cikin wasu addinai na daban. Don haka Musulunci, bisa ga tsarinsa mai kyau, ya haramta ƘABILANCI amma ya ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da zamantakekeniya mai kyau a tsakanin al’umma. Don haka Hausawa da Fulani, sun zama ‘yan uwa na har abada ta fuskar MUSULUNCI. Sun yi auratayya, sun kafa iyali masu tsawon tarihi. Don haka, raba su a wannan zamani da sunan ƘABILANCI, abu me mai matuƙar wuya, tamkar dai ɗaukar Dala ba gammo. Haka kuma, al’amarin – ƘABILANCI – Abu ne mai matuƙar haɗari, wanda zai haifar wa al’umma alkaba’in da ba mu da mizanin auna muninsa. Allah ya kyauta – Amin.

Masu bibiyar wannan muƙala da haƙuri, a nan za mu tsaya, amma in sha Allahu a muƙala ta gaba, za mu bijiro da maudu’in: Ƙabilanci Sam, Zaman Lafiya Maraba.

Kafin sannan, muna maraba da ƙarin bayani ko tambaya a Comment Section. Kuma masu kushe ko zagi da cin mutuncin magabatanmu, musamman Sheikh Usman Ɗanfodiyo (RTA), Allah ya ganar da ku gaskiya. Mu huta lafiya.
_______________
Bashir Malumfashi, shi ne Editan Mujallar Taskar Gizago.

Previous Post

KTSTA: HARKAR SUFURI A HANNUN GWANI (1)

Next Post

Kwankwaso’s Return to APC: Between the Devil and the Deep Blue Sea

Related Posts

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)
Gizago

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

March 1, 2026
#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI
Gizago

#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

February 23, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (13)
Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (13)

February 20, 2026
Next Post
Kwankwaso’s Return to APC: Between the Devil and the Deep Blue Sea

Kwankwaso’s Return to APC: Between the Devil and the Deep Blue Sea

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

RAMADAN KARIM: 02-1447

RAMADAN KARIM: 02-1447

February 19, 2026
ƊANLADI HARUNA

ƊANLADI HARUNA

July 12, 2024
Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci

Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci

January 3, 2026
Shekara 3 Baya: Tunawa Da Majidaɗin Galadiman Katsina

Shekara 3 Baya: Tunawa Da Majidaɗin Galadiman Katsina

June 8, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Injiniya Tukur Hassan Tingilin (1978-2026)
  • RAMADAN KARIM: 16-1447
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (7)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

RAMADAN KARIM: 16-1447

Injiniya Tukur Hassan Tingilin (1978-2026)

March 5, 2026
RAMADAN KARIM: 16-1447

RAMADAN KARIM: 16-1447

March 5, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.