Sabuwar Kwalejin Ilimin Noma A Ƙafur/Malumfashi Za Ta Bunƙasa Ilimi a Jihar Katsina
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

A wani mataki mai muhimmanci na inganta ilimi da ƙerekere a yankunan Malumfashi da Ƙafur, Jihar Katsina da ma Arewacin Najeriya baki ɗaya, an ƙaddamar da Hukumar Gudanarwa ta sabuwar Kwalejin Noma da Fasaha ta Tarayya a Nabanje, da ke Ƙaramar Hukumar Ƙafur a Jihar Katsina.
Taron ƙaddamarwar, wanda aka gudanar jiya, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ciki har da Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Said Ahmad da kuma Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa da sauransu.
A jawabin da ya gabatar a wurin taron, Alhaji Kabir ya bayyana kafuwar kwalejin a matsayin “muhimmin ci gaba na tarihi, ba kawai ga Ƙafur da Malumfashi ba, har da Jihar Katsina da Najeriya gaba ɗaya.” Ya ce kwalejin za ta taimaka wajen samar da ingantaccen ilimi, haɓaka ƙereƙere ta fuskar noma da kiwo da kuma ɗora yankin kan turbar ci gaba mai ɗorewa.
Kwalejin, wacce aka kafa ta ne sakamakon haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki da kuma ƙoƙarin Majalisar Dokoki, ta samu cikakken goyon bayan Gwamnatin Tarayya. Alhaji Ibrahim Masari ya nuna godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu saboda hangen nesa da goyon bayan cigaban ilimi da na ƙasa baki ɗaya. Ya kuma jinjina wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin da kuma Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Umar Dikko Radda, waɗanda suka taka gagarumar rawa wajen tabbatar da kafuwar wannan kwaleji.
“Wannan nasara ce ta kowa da kowa — mu kiyaye ta, mu bunƙasa ta, mu kuma gina kan alƙawuranta,” in ji Masari cikin ƙarfafa gwiwa ga al’ummar da suka halarta.
Waɗanda aka naɗa a matsayin mambobin hukumar gudanarwa ta kwalejin sun haɗa da Farfesa Oluwagbemi Tai, a matsayin Shugaban Hukuma da Dokta Muktar Habib, a matsayin Shugaban Kwaleji (Provost) da Injiniya Abdussamad Umar Jibiya da Farfesa Inuwa Shehu Usman da Labiru Musa Ƙafur mni, a matsayin mambobi.
Alhaji Ibrahim Masari ya bayyana gamsuwarsa da ƙwarewar mambobin kwamitin, yana mai cewa za su jagoranci kwalejin zuwa tudun mun tsira ta fuskar bunkasa ilimi mai inganci da bunƙasa ci gaban ƙasa.
Kwalejin za ta kasance cibiyar koyarwa da bincike kan harkar noma da kiwo da fasaha, inda za a horar da matasa da ƙwararru domin bunƙasa harkokin noma da kwo a Najeriya.
Al’ummar Ƙafur da Malumfashi da kewaye sun karɓi wannan ci gaba da farin ciki, suna kallonsa a matsayin mafita ga rashin aikin yi da kuma hanyar bunƙasa rayuwar al’umma.
Ana sa ran Kwalejin Noma da Fasaha ta Tarayya, Nabanje, za ta taka muhimmiyar rawa wajen sauya tsarin tattalin arziƙi da ci gaban al’ummar Ƙafur, Malumfashi da Jihar Katsina da ma Najeriya baki ɗaya.













