Ɗan Iyan Galadima Ya Zama Shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa Ta Arewa
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

A yau ne, Alhamis 23-12-1446 (Hijiriyya), 19-06-2025 (Miladiyya) aka rantsar da Alhaji Shehu Musa Ɗankano a matsayin Shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (Arewa Consultative Forum) reshen Jihar Katsina.
Alhaji Shehu, wanda shi ne Ɗan Iyan Galadiman Katsina, Lauya (Barista) A. A. Ahmad ne ya rantsar da shi ne tare da sauran muƙarrabansa, bayan nasarar da suka samu a zaɓen da ƙungiyar ta gudanar tun a ranar 12-5-2025.
Da yake gabatar da jawabinsa, jim kaɗan da kammala rantsuwar, sabon shugaban ya ce: “Na nemi haɗin kan sauran shugabanni da mambobin wannan ƙungiya mai albarka, domin samar da ci gaba ga al’ummarmu yadda ya kamata.
“A matsayinmu na ƙungiyar mai alƙibla, za mu yi aiki kafaɗa da kafada wajen samar da ci gaba ga Jihar Katsina da Arewa da ma Najeriya baki ɗaya.” In ji Alhaji Shehu, wanda ƙwararren manomin zamani ne a Arewacin Najeriya.
Da yake miƙa godiya ga ɗaukacin ‘ya’yan ƙungiyar da suka zabe su, Ɗan Iya Shehu ya buƙaci sauran muƙarraban ƙungiyar da aka rantsar, da su ba da haɗin kai, domin ganin sun bunƙasa ƙungiyar da kuma ciyar da ita gaba.













