• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, March 8, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (7)

MUƘALA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 10, 2025
in Gizago
1
ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (7)

Ƙungiyar Hausawa Zalla: Alheri Ko Sharri? (7)

46
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (7)

Daga Yahuza Malumfashi

Related posts

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

March 1, 2026
#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

February 23, 2026
Ƙungiyar Hausawa Zalla: Alheri Ko Sharri? (7)

 

Yadda Ɗanfodiyo Ya Taimaki Al’ummar Hausawa

Jama’a masu bibiyar wannan muƙala da jimiri, Assalamu alaikum; da fatan an yi hidindimun Sallah lafiya. Allah maimaita mana, amin.

A wannan muƙala kashi ta bakwai, da yardar Allah za mu duba kaɗan daga cikin muhimman gudunmowa ko taimakon da Mujaddadin Musulunci, Shehu Usman Ɗanfodiyo (RTA) ya ba al’ummar Hausawa a ɓangare ɗaya da ma al’ummar Musulmin duniya baki ɗaya.

Babban taimako mafi tasiri da Mujaddadi Shehu ya ba al’ummar Hausawa, shi ne ƙwato su daga hannun duhun jahilci da shirka. Kafin jihadinsa, tarihi ya tabbatar da cewa ƙasashen Hausa, duk da cewa sarakunansu Musulmi ne amma sun gurɓata kansu da al’ummarsu da ayyukan da suka yi hannun riga da koyarwar Musulunci.

A wancan lokaci, babu abin da ke tashe sai zalunci da ƙeta daga mulaka’u. Haka ma ta fuskar mabiya, al’umma ta fitsare ƙafarta, babu abin da ke tashe sai bori da tsafi da ashararanci da rashin kunya. Allah cikin ikonsa, a sakamakon wannan jihadi na Shehu, an samu gamsassar nasarar kafa Babbar Daular Musulunci mai ƙarfi da tasiri a faɗin Nahiyar Afirka ta Yamma.

Kamar yadda na ambato wasu littattafai a muƙala ta 6, har yanzu dai daga gare su, mutum zai iya tsinkayar sahihan hujjojin da za su tabbatar masa da wannan bayani nawa da ya gabata.

Wani abin farin ciki da alfahari, a sanadiyyar wannan jihadi, an samu nasarar ƙwato al’umma daga duhun jahilci. An dakatar da zalunci, wanda ya zama ruwan dare daga sarakunan wancan zamani. An samu nasarar dawo da al’umma bisa koyarwar Musulunci na gaskiya, kamar yadda Allah da manzonsa suka umurta.

A sakamakon wannan jihadi, Bahaushe ya samu ‘yanci, ya samu izza kuma buwayarsa ta fito sarari a duniya. Harshen Hausa ya samu ɗaukaka da kulawa ta musamman a sakamakon jihadin Ɗanfodiyo saboda yadda shi Shehu da almajiransa suka duƙufa wajen rubuce-rubuce da wa’azi, ta hanyar amfani da harshen. Kafin wannan jihadi, harkar rubuce-rubuce da harshen Hausa (Ajami) ba ta bunƙasa ba sosai.

Shehu Mujaddadi, a sakamakon jihadinsa, ya kafa tsarin shugabanci mai ƙarfi da tasiri ga al’ummar Hausawa, bisa koyarwar Musulunci. Tsarin shugabancin da ya haifar da tsarkake al’umma. Ya dawo da su bisa hanya madaidaiciya.

Bahaushen da aka sani da al’adar bori da tsafi, aka canza masa tunani da ɗabi’a zuwa kaɗaita Allah ɗaya. Jihadin Ɗanfodiyo ya canza rayuwar Bahaushe daga fitsararre zuwa mutum mai kunya, mai gaskiya, mai son zumunci da ƙarfafa ‘yan uwantaka. Bahaushe ya zama Musulmi na ƙwarai, mai son Allah da manzonsa, mai neman ilimi da bunƙasa shi; maimakon a da can baya da ya kasance matsafi kuma marar tarbiyya. Hatta tsarin tufafin Bahaushe na kamala, duk sun samu ne a sakamakon faɗakarwar da jihadin Ɗanfodiyo ya kawo.

Ya kamata a nan gaɓar, mu sake tunasar da al’umma cewa, Ɗanfodiyo ba yaren Fulatanci ko ƙabilarsa ya jaddada ba. Musulunci da kyawawan al’adun addinin ya jaddada kuma ya ilimantar da al’ummar Hausawa da maƙwabtansu na ilahirin Afirka ta Yamma. Wannan Daula ta Musulunci da ya kafa, ta yi tasiri sosai, tun daga wancan zamani har zuwa yau. Dalili ke nan ma a lokacin da Turawan Mishan suka zo ƙasar Hausa, suka rasa yadda za su kafa tsarin addininsu na Kirista. Dole sai da suka fito da Tsarin-Bayan-Gida (Indirect Rule), sannan suka yi nasarar mulkar ƙasar Hausa. Amma duk da haka, Turawa ba su samu yadda suke so ba, idan aka kwatanta da yadda suka samu nasarar kai tsaye a Kudancin Najeriya, ta fuskar kafa addinin Kirista.

Ke nan, Shehu ba al’adun Fulani ya jaddada ba – Musulunci ya jaddada. Kuma ba yaren Fulatanci ya ɗaukaka ba amma ya ba yaren Hausa muhimmanci sosai, domin shi da almajiransa, sun yi rubuce-rubuce masu yawa da Hausa. Da a misali kishin Fulatanci Shehu ya jaddada, da ya tursasa al’umma ta koyi Fulfulde a kan dole kuma da ya sanya yaren nasa ya zama “Yaren Mulki” a daular da ya kafa. Wato kamar dai yadda Turawa suka tursasa harshen Ingilishi a Najeriya da sauran ƙasashen da suka yi wa mulkin mallaka.

Daga dukkan alamu, masu yaƙi da Musulunci ne suka jefo dasisar ruguza al’ummar Musulmi da Musulunci, musamman a Arewa, shi ne suka biyo ta hanyar makircin BAZATA; da sunan kishin Hausa da Hausawa. Babban burinsu shi ne, su haddasa gaba da ƙyamar juna tsakanin al’ummar Hausawa da Fulani, waɗanda tuni suka zama al’umma ɗaya – saboda ‘yan uwantakar Musulunci da auratayya da kuma zaman tare na tsawon lokaci.

Haka kuma, abu ne sananne cewa, a sanadiyyar jihadin Ɗanfodiyo, akasarin yawancin al’ummomin Arewacin Najeriya har zuwa wasu ɓangarorin ƙasashen Nijar da Kamaru da Chadi, duk sun zama Hausawa saboda mamayewar da yaren Hausa da al’adunsa suka yi wa nasu yarukan na asali.

Jama’a, a kashi na 8 na muƙalar nan, idan Allah ya yarda, za mu bijiro da tambayar: Shin wai ma a duniyarmu ta yau (ƙarni na 21), wane ne Bahaushe zalla?

Kafin sannan, muna maraba da sharhi, tsokaci, gyara ko tambaya game da wannan maudu’i. Haka kuma zuwa gare ku, masu ƙumajin haddasa fitina tsakanin Hausawa da Fulani, ku ci gaba da zagin bayin Allah da sunan kishin Hausa. Hakan shi ke ƙara tona maku asiri da bankaɗo mugun ƙudurinku ga al’ummar Musulmi.
_______________
Bashir Malumfashi, shi ne Editan Mujallar Taskar Gizago.

Previous Post

ƊAN BELLO: Tambarin Gwagwarmaya

Next Post

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNƘASA CIGABAN MALUMFASHI DA KEWAYE (1)

Related Posts

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)
Gizago

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

March 1, 2026
#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI
Gizago

#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

February 23, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (13)
Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (13)

February 20, 2026
Next Post
TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNƘASA CIGABAN MALUMFASHI DA KEWAYE (1)

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNƘASA CIGABAN MALUMFASHI DA KEWAYE (1)

Comments 1

  1. YUSHA, U MUHAMMAD says:
    9 months ago

    Allah yasa mudace yakuma bamu mafita ameen

    Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Dr. T.S Saulawa: Beckons to Serve

Dr. T.S Saulawa: Beckons to Serve

December 12, 2025
Sakatare Ibrahim Dasuƙi Abubakar: Al’ummar Malumfashi Ta Samu Ƙaruwa

Sakatare Ibrahim Dasuƙi Abubakar: Al’ummar Malumfashi Ta Samu Ƙaruwa

October 21, 2025
IGABI AIR STRIKE: A Call for Justice

IGABI AIR STRIKE: A Call for Justice

December 5, 2023
Ɗan'Iyan Galadiman Katsina, Alhaji Shehu Musa Ɗankano

ƊAN IYA MAI ALLAH

April 21, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • RAMADAN KARIM: 19-1447
  • FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
  • RAMADAN KARIM: 18-1447

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

RAMADAN KARIM: 19-1447

RAMADAN KARIM: 19-1447

March 8, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.