Gasar Kano-2024: Nasarar Da Na Samu Ta Canja Mani Tunani Game Da Rubutu
– Zakariyya

~~~
Ƙwararren Akanta ne shi. Ƙwararren mai ilimin kwamfuta ne shi kuma marubuci ne na gani na faɗa. Zakariyya Ɗanladi shi ne ya lashe matsayi na biyu a Gasar Rubutun Gajerun Labarai da Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta gudanar a bara (2024). A tattaunawarsa da Mujallar Taskar Gizago, ya bayyana yadda ya fara rubutu. Haka kuma ya bayar da shawarwari ga marubuta da gwamnati da ma al’umma dangane da rubutu da adabi. Haka kuma ya bayyana ƙufurinsa na ci gaba da yi wa al’umma hidima ya hanyar rubuce-rubuce da bunƙasa adabin Hausa.
~~~
TG: Ka fara da gabatar da kanka, wato tarihinka a taƙaice.
Zakariyya: Assalamu alaikum. Sunana Zakariyya Haruna amma ana min alkunya da Ɗanladi saboda sunan kakana ne na samu. An haife ni a unguwar Gyaɗi-Gyaɗi Kano amma daga bisani mun koma Hausawa ta Gidan Zoo, inda a nan na taso na yi karatu tun daga firamare har zuwa jami’a; inda a halin yanzu nake da mallakin digiri na biyu a Fannin Dabarun Kasuwanci da Mulki. Kuma ina da ‘yan takardu a kan Aikin Akawu da na Sarrafa Kwamfuta.
A halin yanzu, ni marubuci ne mai sha’awar rubuta labarai dogaye da gajeru, musamman waɗanda ke ɗauke da darussa masu faɗakarwa da nishaɗantarwa. Wannan sha’awa ce ta kai ni ga shiga gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, inda na samu nasarar zuwa na biyu.
TG: Tun yaushe ka fara harkar rubutu kuma me ya ja hankalinka zuwa wannan harka ta rubutu?
Zakariyya: Rubutu kam na soma shi da jimawa tun ina ƙaramina nake yawan karance-karance da burin yin nawa rubutun. Kuma na soma jin ƙaunar yin rubutu ne ganin yadda rubutu ke zama wata hanya ta bayyana tunanin mutum da isar da saƙo mai amfani ga jama’a. Na kuma ga rubutu a matsayin wani kayan aiki na raya al’adu, adana tarihi da nishaɗantarwa, musamman a cikin harshen Hausa. Wannan ƙaunar rubutu da sha’awar isar da saƙo ne suka ƙarfafa mini gwiwa wajen ci gaba da rubuce-rubuce har zuwa yau.
Hakan ya sa nake rubutu tun ana mini dariya har ya zame mini sabagiji, nake yin sa a yau da kullum. Rubutuna yana bisa dogaye da gajerun labarai da fassara da kuma sharhin al’amuran yau da kullum da labarai da rahotanni ga kafafen yaɗa labarai da jaridu da sauransu.
TG: Ko za ka bayyana mana sunayen wasu daga littattafan da ka wallafa?
Zakariyya: Na rubuta littattafai da dama amma daga ciki ƙalilan na iya wallafawa da suka haɗa da, Saura Ƙiris, Tekun Labarai na 1 da na 2 da kuma Ɓarayin Zamani. Amma da yardar Allah, a wannan shekarar littatafaina za su bayyana masu yawa da suka haɗa da Taskira, Tekun Labarai na 3, Maganin Ƙarya, Zuciyar Marubuci, Cikin Duhu da sauransu.
TG: Ga shi ka samu nasarar zama na biyu a wannan gasa ta Hukumar Tace Finafinai Da Ɗab’i Ta Jihar Kano. Yaya ka ji da wannan nasara?
Zakariyya: Alhamdu lillahi, babu abin cewa sai godiya ga Ubangiji Maɗaukakin Sarki. Na sha kasancewa na sahun gaba a gasar rubutu da aka yi sau da dama, amma wannan zan iya cewa ta daban ce, yadda al’umma suke ta taya ni murna da nuna farin cikinsu. Kusan kullum nakan samu kiran taya murna sau 15 zuwa sama, ga kuma waɗanda ke tasowa har inda nake su yi mini murna. Ga saƙonni barkatai. Haka kuma wannan gasa ta sake sauya mini tunani dangane da Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i. Ta nuna cewa jagorancin yanzu ba irin na da ba ne, marubuta sun samu gata a yanzu saɓanin a baya da aka mayar da su ‘ya’yan bora. Babu shakka yanzu muna iya cewa kakarmu ta yanke saƙa a Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, kuma a yanzu muna daga cikin jakadun wannan hukuma wajen bayyan kyawawan ayyukanta da manufofin da ta sa gaba.

Haƙiƙa na yi matuƙar farin ciki da wannan nasara, kasancewar zama na biyu a gasa irin wannan, babbar nasara ce a gare ni. Wannan ya tabbatar min da cewa rubutuna na bisa gwadaben da ake marari kuma na sake samun ƙwarin gwiwar ci gaba da rubuce-rubuce tare da samar da labarai masu tasiri ga al’umma.
Wannan nasara ta kuma zama wata dama ta musamman gare ni, yadda zan yi aiki tuƙuru domin hidimta wa adabin Haus ta yadda zan gina wata katafariyar farafajiyar sayarwa da musayar littatafan Hausa tsakanin marubuta da masu karatu. Haka kuma nasarar ta sa na fahimci cewa akwai mutane da yawa da ke jin daɗin rubuce-rubucen da nake yi.
Ina fatan wannan zai zama wani mataki a gare ni na bunƙasa rubutun Hausa a ƙasarmu da kewaye da kuma ɗaga martabar harshen Hausa a fagen adabi.
TG: Yaya sunan labarin da ka shiga gasar da shi? Ka ɗan yi mana bayani game da jigon labarin da kuma darussan da yake koyawa.
Zakariyya: Da farko dai gasar an gina ta ne a kan tambihi kan kyawawan al’adun Hausawa na gargajiya da kuma irin tasirisu a zamantakewar yau da kullum. Don haka na gina labarina mai taken ‘Gadon Gida Sai da Horo’ ne bisa doron buƙatar wannan gasa.
Labarin ya mayar da hankali ne kan muhimmancin haƙuri, ƙoƙari, da rungumar gadon al’adu da sana’o’in gida wajen cin ma nasara. Yana bayyana yadda son hanzarta samun nasara ba tare da aiki ba ke jefa mutum cikin matsala.
Inuwa, jarumin labarin, ya guji gadon iyayensa na noman gargajiya da kiwo da kuma laftun jakai. Burinsa kurum ya samu kuɗi ko dukiya ta hanya mafi sauƙi. Don haka yake ta karakaina tsakanin ƙarya da gaskiya da neman jalabi daga ‘yan tsibbu. Sai dai duk abin da ya sa hannu sai ya zama tamkar tafiyar kura – watau idan an yi gaba sai a yi baya. Ƙarshe dai ya tari aradu da ka ya shiga wasan dambe, wanda bayan sa-toka-sa-katsi aka rafke shi’ bai tsinci kansa ba sai a gadon asibiti.
Ta hanyar rarrashi da nuni da nasiha, mahaifinsa ya jawo hankalinsa kan komawa sana’ar gida wadda ke koyar da juriya haƙuri da kuma jajircewa. Inuwa ya gane cewa ashe kowa ya bar gida, gida ya bar shi. Ya naƙalci cewa hatta gadon gidan nasu ma da ya raina ba zai iya tsinana komai ba sai an ba shi horo. Ke nan ba gaskiya ba ne da ake cewa gado kaɗai ya isa mutum ya shahara koda bai yi aiki tuƙuru ba.
Wasu daga darussan labarin sun haɗa da: 1-Muhimmancin dogaro da kai da aiki na gaske wajen samun nasara. 2-Kada mutum ya raina gadon iyayensa ko sana’ar al’ummarsa. 3-Babu nasara mai ɗorewa da za ta zo ba tare da haƙuri, horo, da ƙoƙari ba. 4-Kyautata wa al’umma yana ba da gudunmuwa wajen gina rayuwar jama’a baki ɗaya.
Wannan labari yana da nufin jan hankalin matasa su fahimci cewa nasara tana buƙatar haƙuri, nutsuwa da kuma rungumar abubuwan da ke kusa da su. An yi amfani da kalmomi da muhallin gargajiya sosai domin neman dacewa da abin da gasar ta ƙunsa.
TG: Wace shawara za ka ba marubuta, waɗanda ke son shiga irin wannan gasa ta rubutu?
Zakariyya: Shawarata, ba a yin rubutu domin a shiga gasa a rana ɗaya kuma a yi nasara. Idan kana son yin nasara ga kowacce irin gasa sai kana jarrabawa yau da kullum. Yana da kyau mutum ya riƙa yin rubutu yau da kullum babu dare babu rana, babu tsayawa ballantana yada zango. Da haka idan buƙatar gasar ta taso sai kurum ka ɗauka ka yafa yadda ake buƙata. Mai son duwatsu sai ya shiga maliya, mai neman suna sai ya ɓata hankalin dare, haka kuma mai neman zomo sai ya jure wa gudu domin zomo ba ya kamuwa daga zaune ko da kiwon gida ne.
Don haka ba zai yiwu marubuci ya zauna sai an fito da wata gasa ko neman wallafa littafi ba sannan zai motsa. Dole rubutu ya zama ana yin sa kodayaushe kuma ana nazari da bincike gami da tunani. Zan iya cewa marubuta a yanzu suna da gata gami da tagomashi, domin kuwa ga shi nan ana ta fito da gasanni na rubutu da dama kuma ana raba kyaututtuka da girmamawa da karramawa, saɓanin lokutan baya kaɗan da marubuta suka zama tamkar ungulu ko ‘ya’yan bora ko burtuntuna, yadda ake la’anarsu ake kware musu baya, ake jifar su da alkaba’i da mugun nufi. Yanzu kuwa sai jan su ake yi a jiki, ana martaba su, ana mutunta su. Ashe ke nan wajibi su ma marubuta su nuna halin yakana da tunani ta hanyar yin rubutu a kan kari kuma mai ma’ana ta hanyoyin da suka dace.
Don haka, taƙaice bayan nacin rubutu da kuma aniya ta gaskiya, marubucin da ke son yin nasara cikin gasar rubutu yana da kyau ya bi waɗannan matakan kamar haka:
1-Yin bincike mai zurfin kan jigo da batutuwan da gasar ta buƙata. Kada ana cewa ka yi rubutu a kan sarauta, ka ɓuge da rubutu a kan farauta. Nazari yana taimakawa wajen rubuta labari mai ƙayatarwa.
2-Mayar da hankali wajen amfani da harshe mai tsabta, wanda zai iya jan hankali tare da isar da saƙo ga masu karatu cikin sauƙi.
3-A yi komai cikin nutsuwa da tsari, ban da gaggawa ko wuce gona da iri kan buƙatar da gasar ke da ita. Kuma kada su zarce lokacin da aka ce a kai rubutun ga inda aka tanada.
4-Marubuci ya kasance da niyya ta ƙwarai wajen yin rubutu domin ilmantarwa da faɗakarwa da kuma nishaɗantarwa ba kawai domin samun kyauta ba.
5-Marubuci ya nemi shawarwari daga gogaggun marubuta ko masu ilimi a fagen adabi don inganta labarinsa tun kafin ya tura inda aka buƙata na gasar.
A ƙarshe dai ina nanata cewa, ya kamata marubuta su kasance masu haƙuri da jajircewa, domin duk nasara tana buƙatar sadaukarwa. Gasar rubutu dama ce mai kyau amma ba ita ce ainihin silar da ke sa wa a yi rubutun ba.
TG: Wane kira za ka yi ga gwamnati da al’umma dangane da harkar rubutu da adabi?
Zakariyya: Kiran da zan yi ga gwamnati shi ne, ta yi ƙoƙarin ci gaba da tallafa wa harkar rubutu da adabi, ta hanyar samar da cibiyoyin nazari da bincike da kuma ba wa marubuta tallafi da kuma ci gaba da shirya gasar rubutu don ƙarfafa ƙwazon matasa.
Gwamnati na iya ware kuɗi don wallafa littattafan Hausa da kuma ɗaukar nauyin fassara wasu littattafan na ilimi zuwa Hausa. Na ga irin wannan a ƙasashen Yarabawa, inda Gwamnatin Jihar Osun a 2008-2010 ta ɗauki nauyin fassara littafan ilimin lissafi da kimiyya zuwa Yarabanci, wanda haka ya kaifafa ƙwaƙwalwar ɗalibai suka samu nasara a jarrabawarsu da kammala sakandare. Wannan kuma zai tallafa wa marubuta wajen shiga kasuwannin duniya.
Ga al’umma kuwa, yana da muhimmanci su fahimci rawar da adabi ke takawa wajen gina al’ada da tunani. Ya kamata jama’a su riƙa sayen littattafai domin karantawa da ajiyewa a laburare. Kuma hakan zai tashi kafaɗun marubuta da ƙasusuwansu suka yi rauni.
Bugu da ƙari, ya dace iyaye su riƙa ƙarfafa wa yara gwiwar karatu da rubutu tun suna ƙanana, domin su zama manyan marubuta nan gaba.
Dukkanmu ya kamata mu fahimci cewa harkar rubutu da adabi wata hanya ce ta adana tarihi, da ilmantarwa da kuma jan hankalin duniya kan abubuwan al’ummarmu ke ciki. Duk wani ci gaba zai kasance ne idan kowa ya taka rawar gani wajen gina wannan muhimmiyar al’umma ta Hausawa mai daraja.













