SHIRIN GWAMNA ABBA GIDA-GIDA NA RABA TALLAFIN AWAKAN KIWO YANA KAN DAIDAI
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

A ‘yan kwanakin nan ne labari ya cika kafafen soshalmidiya, wasu suna suka da caccakar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf saboda ya ƙaddamar da shirin bayar da tallafin dabbobin kiwo ga matan karkara, da nufin bunƙasa noma da kiwo a hannu ɗaya da kuma rage raɗaɗin talauci da ƙarfafa ƙananan sana’o’i ga mata a karkara da ɗaukacin jihar, a ɗaya hannun.
Kamar yadda labari ya tabbatar, Gwamna Gida-Gida ya kashe Naira biliyan 2.3 wajen ƙaddamar da shirin, inda aka raba adadin awakai 7,158 ga mata 2,386.

Haka kuma, kamar yadda Daraktan Watsa Labarai na Gwamnan, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana, ya ce akwai kuma shiri na gaba, inda gwamnan zai raba shanu guda 1,342 da raguna 1,822 ga wasu rukunin matan daban.
Maimakon sukar wannan shiri, kamata ya yi mu duba manufarsa da sakamakon da zai haifar wajen gina rayuwar al’umma.
Ɗauki misalin rayuwar mutanen karkara, musamman mata, yadda suke cikin talauci da ƙuncin rayuwa. Ta wace hanya za ka iya sauƙaƙa kaifin matsalolinsu? Shi ne ta hanyar inganta sana’arsu. Kamar yadda wata azancin maganar mutanen China take cewa,
“Ka koya wa mutane yadda ake kamun kifi, shi ya fi alheri da ka riƙa kama kifin kana raba masu.”

Yanzu misali, an raba wa mata fiye da 2000 awakai sama da 7000. Idan suka kiwata su kuma Allah ya albarkace su, kafin shekara ta kewayo guda nawa za su koma? Babu mamaki, cikin matan nan daga nan wata za ta tara garke. Daga nan wata za ta zama attajira, saboda sun saba da kiwo kuma za su ririta abin yadda zai yaɗu.
Nan fa ake ta kukan cewa gwamnoni sun ƙyale mutanen karkara, suna ta gina gadoji a manyan birane. Idan ba ta wannan ƙaramar hanyar ba, ta yaya ake zaton mutanen karkara za su amfana da tallafin gwamnati?
Wasu kuma suna zargin wai akwai aringizo wajen sayen dabbobin. Ni kuwa nake ganin a wannan yanayin da muke ciki, idan ɗan siyasa ya ga damar ɗibar kuɗi, zai ɗiba ne ko nawa ya ga dama, koda bai shigo da wannan tsarin ba. Don haka Ni na fi kallon tasirin tsarin, fiye da yawan kuɗin da ake ikirarin an kashe.

Ni a ganina, maimakon wasu da suke ta sukar shirin, kamata ya yi a yaba wa Gwamna kuma a ƙarfafa masa gwiwa, sannan a buƙaci ya faɗaɗa shirin ya shafi ƙanana da matsakaitan ‘yan kasuwa da masu sana’o’in hannu. Haka kuma, ya kamata su ma sauran gwamnonin Arewa su ɗauki wannan salo na ƙarfafa noma da kiwo da ƙananan sana’o’i ga talakawa, musamman na karkara.
Ni dai a nan, ina yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan shiri na bunƙasa tattalin arziƙin talakawan karkara. Ina fatan zai ci gaba da gudanar da tsarin a kowace shekara, yadda al’amarin zai isa ga mutane masu yawa. Allah Ya sa mu dace, Amin.













