• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

JIDALIN KISHIYA – Labarin Uwargida Farida

TSAKURE DAGA LITTAFI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 3, 2024
in Adabi
0
JIDALIN KISHIYA – Labarin Uwargida Farida

Jidalin Kishiya

79
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

JIDALIN KISHIYA

(Labarin Uwargida Farida)
                     •••

Related posts

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Jidalin Kishiya

A lokacin da Maigida Baba da Uwargida Farida suka gama sauraren waƙar nan ta Hamisu Breaker, ba su ɓata lokaci ba suka shiga cin abincin dare, wanda da ma yake ajiye a gabansu. Maimakon kowa ya zuba nasa abincin daban, sai suka zuba a filet ɗaya suna ci tare.

Rabon da a samu farin ciki tsakanin ma’auratan nan an daɗe amma a yau abin ya yi armashi. A duk lokacin da Alhaji Baba ya kai cokali baka yana tauna abinci, babu abin da yake yi illa kallon matarsa cikin mamaki. Mamaki yake yadda rana ta koma inuwa a gidansa, yadda zafi ya koma sanyi.

A yayin da suke cin abinci suna wasa da juna cikin murmushi da raha, ba su yi aune ba suka ga lokaci ya milla. Don haka bayan sun kammala, Farida ta kau da kwanuka, sai kuma suka dawo domin ci gaba da tattaunawa, kamar yadda ta buƙata.

“Kin cika mani ciki da abinci. Na ji ma har idanuwana sun fara lumshewa, suna buƙatar barci.” Abin da Alhaji Baba ya fara faɗa ke nan, bayan ya zauna a kujerar kushin.

“Barci? Haba Daddy, ai kuwa ba dai yau ba.”

Ta faɗi haka a yayin da ta karkace ta riƙe ƙugu, ta marmasa masa daradaran idanuwanta.

“Yau ba ranar barci ba ce. Yau rana ce ta musamman ta masoya. Ranar da babu abin da ke cikinta sai farin ciki.”

Bayan ta zauna a kujerar da ke fuskantarsa, Farida ta fara bayyana masa dalilin wannan zama na musamman da ta buƙaci su yi.

“Daddy, na zauna na yi nazari a rayuwata, babu wani dalili da zai sanya mu ci gaba da zama cikin ƙunci da ƙullatar juna. Babu dalilin da zai sa mu kawar da tunaninmu daga abin da ya dace, mu riƙa aikata akasi.”

Ta ɗan tsahirta da magana. Ta kalli yadda mijinta ya yi shiru, idanuwansa suna kan fuskarta, a yayin da take magana. Ta ƙara sabon murmushi, sannan ta ci gaba da maganarta cikin kwanare.

“A yau, ina son mu zauna mu amayar wa juna dukkan tunaninmu da ƙudurorinmu game da rayuwarmu ta iyali. Mu zuba komai a faifai. Mu bakace, mu tace abin da zai amfane mu; mu zubar da duk wani abu da zai kawo mana matsala a gidan nan.”

Alhaji Baba ya yi kasaƙe yana ci gaba da kallon ta cikin shauƙi. Bai ce komai ba, sai dai ya yi mata ishara da cewa ta ci gaba.

“Da farko dai ya maigidana, ina son mu yi tariyar musabbabin rashin jituwar da ta kawo mana matsala a gidan nan.”

“To, ta ina za mu faro?”

Ya ɗaga kai kamar yana son tunano wani abu. “Ni dai a iya sani na, babu abin da ya kawo mana matsala sai batun nan na ƙarin aure da na kawo maki. Daga wannan batun akwai wani ne?”

“Daddy ke nan, gaskiya babu wani batu sai shi!”

“To ga tambaya: Don Allah me ya sanya kika ɗaga hankalinki dangane da wannan batu? Shin kina munana mani zaton ba zan yi adalci ba ne a tsakaninku?”

Farida ta yi ajiyar zuciya, annurin fuskarta ya canja zuwa yaƙe.

“Babban abin da ya tada mani hankali, ba komai ba ne illa ƙaunar ka. So da ƙauna su ne suka toshe mani komai na tunani da tsinkaye. Ba na ganin komai sai ƙaunar ka. Hakan ya sanya nake ganin ba zan lamunci kowace mace ta kusance ka ba, muddin dai ina raye.”

Muryar Farida ta fara rawa, fuskarta ta yamutse da alamar damuwa, sannan ta ci gaba da magana.

“Ni a tunanina, ni kadai na ishe ka rayuwar aure, domin babu wani abu da za ka nema na ƙa’ida da haƙƙin aure wanda ba zan iya yi maka shi ba.”

Jin haka sai ya ƙyalƙyace da dariya. Ita kuwa sai abin ya harzuƙa ta, sai ta fashe da kuka.

Shi kuwa sai ya tashi daga kujerarsa, ya dafa kafaɗarta, yana rarrashin ta.

“Ko kaɗan ban raina himma da ƙoƙarin ki ba kuma ban raina irin yadda kike kauna ta ba. Shi lamarin aure da ma kowane irin al’amari na rayuwa, muƙaddari ne daga Allah.”

Ya karkata bakinsa daidai kunnenta na dama, ya ɗan hura iska a hankali, sannan ya ci gaba da maganarsa ta lallashi da nasiha.

“Kamar yadda masu iya magana suka ce, tun ran gini ran zane. Duk abin da zai faru a rayuwar ɗan Adam, Allah Ya gama tsara masa shi kuma babu makawa sai ya faru. Babu yadda mutum ya iya.”

A lokacin da bakinsa ke kusa da kunnenta na dama, sai kuma ya sanya babban yatsansa na hagu a gefen ɗaya kunnen nata na hagu, yana shafawa a hankali. Sannan ya ci gaba da batunsa.

“Shi ya sanya ake son mutum ya kasance mai yawan roƙon Allah a kowane lokaci, domin ya dace da alheri. Ina son ki kwantar da hankalinki. Ki yi tunani irin wanda ya dace da addini da ilimin da kike samu daga Islamiyya. Ki fitar da son rai. Ki fitar da son kai daga zuciyarki. Ki fuskanci gaskiya kawai. Idan kin yi haka sai ki tambayi kanki, shin abin nan da mijinki zai yi, mene ne matsayinsa a shari’ar Musulunci?”

Farida ta daina kukan, ta natsu tana sauraren mijinta; inda shi kuma ya ci gaba da bayaninsa.

“Akwai dalilai da dama da kan sanya namiji ya ƙara aure fiye da dalilan da kika kawo. Ni dai babban dalilina shi ne, ina sha’awar raya sunnar Manzon Allah (saw). Ina son a matsayina na namiji wanda Allah Ya hore wa dukiya daidai gwargwado, wanda ya ba ’ya’ya maza da mata, ina son in zama cikin masu taimaka wa mata ta hanyar aure, musamman ganin yadda suke ƙara yawa. Ina son yadda na auri ’ya’yan wasu, ni ma a zo a auri nawa ’ya’yan.

“Haka kuma ina son ki gane, shi fa aure babban zumunci ne. Babban alheri ne kuma babban arziƙi ne. Al’amuran rayuwa suna yin daɗi ne daga yadda al’umma suka kasance cikin zumunci da zaman lumana da juna. Haka kuma ina yi maki albishir da cewa, da kyakkyawar niyya zan yi auren nan, ba domin in wulaƙanta ki ba. Zan ƙara aure ne domin yauƙaƙa zaman tare tsakaninmu. Na yi maki alƙawarin bin dokoki da sharuɗɗan Musulunci dangane da aure sau da ƙafa tare da kare mutuncinki da nata da kare haƙƙoƙin da suka wajaba a kaina. Ina son ki kwanktar da hankalinki. Ki taya mu da addu’a, Allah Ya albarkaci al’amarin.”

Yana ɗiga aya a zancensa sai Farida ta yi zambur ta amsa da cewa: “Ina kyautata maka zato amma ni babban abin da ke ban tsoro shi ne, wace ce za ka aura? Ya kamata ka yi bincike sosai. Kada ka ɗauko mana kara da kiyashi.”

Haka suka yi ta musayar zantuka. Ba su ankara ba ashe dare har ya tsala. Lokacin da Alhaji Baba ya duba agogo, ƙarfe biyu da rabi na dare. Ba su kwanta ba sai da suka samu fahimta sosai. Ya yi mata gamsasshen bayani game da Saratu, inda ya ce mata bai gama yanke ƙuduri a kanta ba. Ya ce zai ci gaba da bincike domin samun matsaya mai kyau dangane da batun.

Uwargida Farida dai ta sha alwashin goya masa baya ɗari bisa ɗari.

“Idan Allah Ya yarda, za ka same ni mai biyayya da dukkan matsayar da ka ɗauka. Zan ci gaba da yi maka duk abin da na saba a ibadar zamanmu na aure. Haka kuma kamar yadda ka nusar da ni, zan ci gaba da ƙoƙarin roƙon Allah Ya zaɓa mana mafi alheri.”

Da wannan kalami na Farida suka tashi daga hirar, suka shiga barci.
_______________
© Bashir Yahuza Malumfashi

Previous Post

KADA Honours Ambassador A. Y Shehu with Excellent Award

Next Post

Horror and Terror

Related Posts

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza
Adabi

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Let’s Speak Our Mother Tongue
Adabi

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

March 6, 2026
Next Post
Horror and Terror

Horror and Terror

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

SHAWARA TA FI MUHAWARA

SHAWARA TA FI MUHAWARA

August 15, 2024
TALAUCI: Yadda Matasan Arewa Ke Gararamba A Legas A Wulaƙance

TALAUCI: Yadda Matasan Arewa Ke Gararamba A Legas A Wulaƙance

October 4, 2023
KAMUN LUDAYIN JEMAGE

KAMUN LUDAYIN JEMAGE (26-08-2023 da 02-09-2023)

September 2, 2023
RAMADAN KARIM: 06-1447

RAMADAN KARIM: 06-1447

February 23, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.