• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, January 22, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

SHERIF ALMUHAJIR: JAMA’A YA KAMATA MU MUTUNTA JUNA

NASIHA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 3, 2024
in Gizago
0
SHERIF ALMUHAJIR: JAMA’A YA KAMATA MU MUTUNTA JUNA

Dokta Sherrif Almuhajir

47
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

SHERIF ALMUHAJIR: JAMA’A YA KAMATA MU MUTUNTA JUNA

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)

January 17, 2026
Dr. Sherrif Almuhajir

Na wayi gari da safiyar yau, na ga yadda ake ta kwarmato tare da yamaɗiɗi da suna tare da keta mutuncin Dokta Sherrif Almuhajir.

Daga bisani ma sai na ga shi da kansa ya fito yana bayyana ba’asi tare da barranta kansa da wannan ƙazafi da aka ƙaƙaba masa.

Ya kawo hujjoji da suke tabbatar da cewa “wani” ko “wasu” ne suka shiga rigar sunansa da hotonsa, suka yi amfani da fasahar takanolaji, suka shirya wannan tattaunawa, tsakaninsa da “wata.”

A cewar sa, sun yi haka ne domin cin zarafi da neman tozarta shi a idon duniya. Bisa kan haka, har ya nuna cewa ya shigar da ƙorafi ga hukuma, domin ɗaukar matakin da ya dace.

Na bibiyi da dama daga cikin waɗanda suka zaƙalƙale wajen kururuta al’amarin tare da yaɗa shi. Na fahimci cewa da yawa daga cikinsu, har ga Allah sun san cewa al’amarin nan ba gaskiya ba ne, amma saboda suna da wani “SAƁANI” da shi, shi ya sanya suka ara suka yafa da nufin huce haushi.

Ni a gani na, ba daidai ba ne domin kana da saɓani da wani amma ka fito kana tozarta shi bisa ƙarya da ƙage, kawai domin ka daɗaɗa wa zuciyarka.

Tabbas, duk wanda ya san Almuhajir, ya san shi da shiga al’amuran wasu gaba-gaɗi, sannan kuma bai da juriyar suka ko kaɗan. A kan haka ya ɓata da mutane da dama, ya yi bulokin mutane da dama (ciki har da ni, a shekarun baya). Amma duk da haka, wannan ba hujja ba ce, mutum ya maida mugunta da wata muguntar.

Kuma tabbas, ina da tabbacin lallai za a iya ƙirƙirar chatin na bogi ta hanyar WhatsApp ko Facebook Messenger da suna da hoton duk wanda ake so. Ba chatin kaɗai ba, a wannan zamanin hatta hotunan bidiyon bogi, za a iya ƙirƙira a kan wani ko wata.

SHAWARA:
Abin da duk ba ka so a yi maka, don Allah ka daure, kada ka yi wa waninka. Domin idan yau shi aka yi wa haka, akwai yiwuwar gobe kai ma a yi maka ko kuma wani naka. Shin idan haka ta faru da kai, yaya za ka ji?

Kada fa mu manta, mu ‘YAN ADAM ne, cike muke da ayyukan assha na zahiri da na ɓoye. Idan Allah Ya rufa mana asiri, to me zai sa mu mu shiga tona wa waninmu asiri?

Daga ƙarshe, don Allah mu daure mu riƙa danne zukatanmu wajen huce takaicin junanmu, domin gaba ta fi baya yawa. Za ka iya saɓani da mutum a yau, gobe kuma ya zama amininka. BABU ABIN DA YA GAGARI ALLAH!

ALLAH YA SA MU DACE – AMIN!

__________
Bashir Yahuza Malumfashi,
Babban Editan Mujallar Taskar Gizago (online)

Previous Post

KIRA NA MUSAMMAN GA JAMI’AN TSARO A MALUMFASHI

Next Post

VENOM

Related Posts

My 83rd Birthday and the Kindred Spirit
Gizago

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)
Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)

January 17, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (8)
Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (8)

January 13, 2026
Next Post
VENOM

VENOM

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Kuskure Kan Ingilishi: Wane Ne Ke Son Wulaƙanta Gwamnan Kano?

Kuskure Kan Ingilishi: Wane Ne Ke Son Wulaƙanta Gwamnan Kano?

June 3, 2023
TSOKACINMU NA YAU (15)

TSOKACINMU NA YAU (15)

March 15, 2025
A.B.U Graduate Builds Motorcycle with ₦200K

A.B.U Graduate Builds Motorcycle with ₦200K

September 15, 2023
SASSANYAN AMINCI (3)

SASSANYAN AMINCI (3)

September 6, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)
  • Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya
  • Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.