• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, September 20, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

DUNDUFAR SAITI

WAƘEN FASAHA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
March 26, 2024
in Adabi
0
DUNDUFAR SAITI

Bashir Yahuza Malumfashi

15
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

DUNDUFAR SAITI
                   •••

Godiyar Allah na nanata,
Jallah Gwani Kai naka bauta,
Arrazaƙu ni’imto ruhina.

Related posts

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)

September 12, 2026
Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026

Manzo Muhammadu ne tutata,
Fitila mai haskaka hanyata,
Baban Fatima kai naka ƙauna.

Da uwa da uba duk kun kyauta,
A gare ni a yau kun alkinta,
Kun kyautata dukkan sashena.

‘Yan uwa na jini ga caffata,
A gare ni ku san kun cancanta,
Naku ne ni kullum na nuna.

Abokai na zumu ga shiftata,
Ku karanta don ku rabauta,
Mu guje wa dukka hiyana.

Duniya muke yau mun saba ta,
Wata rana mu mace komai rata,
Mu guje ta kar fa mu ƙuna.

Mu sani mun zo ne bauta,
Mu guje shirka don mu rabauta,
Mu gaje gidajen dukka aljanna.

Mu guje dukka ruɗin Shaiɗani,
Mai ingiza mu zuwa hairani,
Mu haɗe kai mu guje saɓani.

Ɗan uwa zo nan mu yi zance,
Mai inganci don fa mu tantance,
Shawarar kirki duk sai an zauna.

‘Yar uwa ke ma zo nan duba,
Kisan baƙi aikin gayya babba,
Ga zance mai ƙima tattauna.

A yau duniya ta lalace,
Mu ankare kar mu sakankance,
Hanyar kirki kar mu yi sauna.

Dakarun Dujjal sun yo kuwwa,
Karuwai, ‘yan daudu suna shewa,
Mu guje assha ya ku dangin juna.

Ƙofar fitina sun bubbuɗe ta,
Shoshalmidiya yau ta zama jita,
Maza da mata ana daddasa ɓarna.

An cire kunya wai su “wayewa,”
Malumanmu ana daɗa takawa,
Aikin fajirci jiddadun mummuna.

Aure sunna yau ya zama jari,
Sharholiya ake ita ce tsari,
Rayuwa ta birai dillalan ɓarna.

Mu sani ya ku dangina,
Duniya tai nisa mu tuna,
Mu zo mu riƙe babbar sunna.

Mu guje cinye amana, tozarci,
Mu daina gulma da zunɗe fajirci,
Annamimanci ciwo mu daina zina.

Mu aikata alheri shi ne hanya,
Sallah, Azumi, Zakka, Hajji sanya,
Imani ne farko sannan riƙe sunna.

Mu roƙi Allah domin dacewa,
Ya sauƙaƙa mana sauƙaƙawa,
Nasarar duniya da gobe zumuna.

Ya Allah amsa min addu’ata,
Kullum Ka ƙarfafi niyyata,
ALJANNA ta zamto ɗakina!

Mai ƙasida ya gama aiki nan,
Bashir Yahuza mai isharar nan,
Na Malumfashi garin gadona.

                •••
© Bashir Yahuza Malumfashi
Asabar, 13-09-1445 (Hijriyya)
13-03-2024 (Miladiyya)
                    •••

Previous Post

Ƙungiyar Marubutan Nahiyar Afirka (PAWA) Ta Buƙaci Marubuta Su Koma Yin Rubutu A Harsunan Gida

Next Post

BATUN WATAN SALLAH A NAJERIYA

Related Posts

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)
Adabi

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)

September 12, 2026
Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai
Adabi

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026
Alhaji Sule Lamido: Jagoran Talakawa Na Haƙiƙa
Adabi

Alhaji Sule Lamido: Jagoran Talakawa Na Haƙiƙa

August 29, 2026
Next Post
BATUN WATAN SALLAH A NAJERIYA

BATUN WATAN SALLAH A NAJERIYA

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

SATAR AZZAKARI: Gaskiya Ko Ruɗanin Tunani?

SATAR AZZAKARI: Gaskiya Ko Ruɗanin Tunani?

October 16, 2023
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
Gwamnan Katsina Ya Raba Ma’aikatar Ilimi Zuwa Gida Uku

Gov. Radda Appoints Dr. Mansir Malumfashi as General Manager

September 21, 2023
HANYAR TSIRA (SAW)

HANYAR TSIRA (SAW)

November 26, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.