• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, January 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Babban Birnin Tarayya Abuja: Jiya Da Yau Da Gobe

Dr. Bukar Usman by Dr. Bukar Usman
September 19, 2023
in Babban Labari
2
The Federal Capital Territory Abuja: The Past, Present and the Future

Ƙofar Babban Birnin Tarayya Abuja

45
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Babban Birnin Tarayya Abuja: Jiya Da Yau Da Gobe

Daga Dokta Bukar Usman, OON

Related posts

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

January 14, 2026
Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

January 4, 2026
Dokta Bukar Usman, OON

A rayuwata, na taɓa zama a Legas na tsawon shekara 27, inda daga bisani na dawo Abuja, inda a yau na kwashe kimanin sama da shekara 30. Ina ɗaya daga cikin jami’an gwamnati na Ofishin Shugaban Ƙasa na sahun farko da suka dawo Abuja, a ranar 12 ga Disamba, 1991; lokacin da gwamnatin ta hukunta dawo da fadar gwamnati daga Lagos zuwa Abuja. A bara, 2022 da na waiga baya dangane da wuraren da na zauna a tsawon shekaru 80 na rayuwata, na fahimta da cewa na kwashe kimanin kashi 40% na rayuwata a Abuja.

A shafi na 129 zuwa na 131 na littafin tarihin rayuwata mai taken ‘Hatching Hopes’ (Cikar Buri), wanda kamfanin Klamidas ya wallafa a 2006, na bayyana labarin abubuwan da na gani da idanuna, yadda aka gina Abuja tun daga farko, tun lokacin da mazaunin hukumomin gudanarwa da na kula da gina babban birnin yake a Suleja. Watau a can baya ke nan, kafin a dawo da su Kwanar Bega, Eriyawan, har zuwa yanzu da suke a mazauninsu a Eriya-Ilabin.

Abubuwan Tunawa Game Da Abuja:

Na samu damar zama ɗaya daga cikin jami’an gwamnati na sahun farko da suka taso daga Legas zuwa Abuja, sabon Babban Birnin Tarayyar Najeriya, a ranar 12 ga Disamba, 1991. Na kalli yadda aka gudanar da shagulgulan bikin tarewar a babbar ƙofar shiga Abuja. Babu shakka mun ji daɗin kallon waɗannan bukukuwa masu ƙayatarwa. Mun kalli yadda turakun gwamnati uku – Ɓangaren Majalisa, Ɓangaren Shari’a da Ɓangaren Zartarwa suka shiga sabon birnin cikin armashi. Ba na cikin jami’an da suka yi aikin gina sabuwar Abuja da ƙarfin jikinsu.

Sai dai kuma a kan idona wasu daga cikin ayyukan gina birnin suka gudana, a lokacin da ake kan aikin. A matsayina na ɗaya daga cikin ayarin manyan jami’an Fadar Gwamnatin Tarayya, mun riƙa ziyartar cikin birnin Abuja, muna duba yadda aikin gine-gine ke gudana, domin tantance matsayin aikin, domin ganin cewa gwamnati ta shirya dawowa Abuja.
Na tuna lokacin da muka ziyarci inda ake gina Dam Na Jabi, lokacin da aka fara haƙa shi, babu ruwa cikinsa. Haka ma na tuno ziyarar da muka kai zuwa Filin Jirgin Saman Abuja, wanda yanzu ake kira da sunan Filin Jirgin Saman Ƙasa-da-Ƙasa na Nnamdi Azikiwe. A lokacin da magina suka fara zuwa wajen, hanyar zuwa wajen ta Zuba, ƙarama ce, a lokacin ma ana kan gina hanyar tashin jirage. A lokacin nan ‘yan gidaje ƙalilan ne aka gama ginawa a Unguwar Garki kuma an nuna mana su. Mun ankara da cewa aikin bai yi kyau ba sosai kuma mun bayyana haka.

Wani abu da na lura da shi tun a lokacin shi ne, kafin zaɓen Shugaban Ƙasa karo na biyu a dimokuraɗiyya, a Mayu 1999, Abuja ta fara nuna alamar cunkoso. Wannan kuwa ya faru ne a sanadiyyar yadda aka riƙa kauce wa Daftarin Tsarin Gina Birnin. Bayan shekara biyu da zuwan sabuwar gwamnati, an samu kwararowar mutane zuwa babban birnin, wanda haka ya nuna cewa lallai akwai buƙatar a ɗauki matakin gaggawa, domin kauce wa gurɓacewar birnin kamar yadda ta faru da Legas. (Shafi na 129-131).

Na ƙarƙare da cewa:

…waɗanda suke tunanin za a bar komai ya gudana a Abuja, ba tare da bin Daftarin Tsarin Gina Birnin ba, ba tare da aiwatar da gyare-gyare da kula da gine-gine da muhimman kayan gwamnati ba kuma ba tare da kula da ɗabbaƙa dokar kiyaye ɗabi’ar al’umma ba, Abuja za ta zama mai kyau da tsari kamar yadda ake buƙata, lallai ne su canja tunani (Shafi na 131).

Babu shakka hukumomin da ke da alhakin kula da bunƙasar garin sun yi ƙoƙari wajen kiyaye martabar Daftarin Tsarin Gina Birnin. Sai dai kuma alama ta nuna cewa tumbatsar da birnin yake da mutane na neman kawo masu cikas. Kayayyakin more rayuwa sun yi kaɗan, babu wani taƙamaiman tsarin motocin sufuri. Idan aka zo maganar wutar lantarki kuwa, abin ya zama kwan-gaba-kwan-baya, kodayake al’amarin bai tsaya ga Abuja kawai ba, ya shafi dukkan ƙasa.
Daga abin da ya bayyana a yayin tantance sabbin ministoci da ya gudana a Majalisar Tarayya, a watan Agustan bana, ta tabbata cewa za a ɗau lokaci mai ɗan nisa, kafin a shawo kan wannan matsala. Ana ɗora matsalar lantarki bisa ƙarancin iskar gas da za ta tayar da manyan injinan samar da lantarki da kuma gazawar kamfanonin rarraba lantarkin da ake wa laƙabi da “DisCos” a taƙaice. Haka kuma akwai matsalar ingantattun layukan rarraba hasken na lantarki.

Dukkan waɗannan matsaloli da ƙalubale an kasa shawo kansu, saboda abin da wasu mutane ke alaƙantawa da gazawar Hukumar Kula Da Al’amuran Lantarki ta Najeriya, wacce Dokar Gyara Al’amuran Lantarki ta 2005 ta kafa, musamman domin wannan aiki na kawo gyara a harkar.

Saita ginin Babban Birnin Tarayya Abuja bisa gwadaben Daftarin Tsarin Farko, kamar an makara. Tun da farkon assasa ginin birnin, akan share gari, a samar da abubuwan kyautata rayuwa, kafin daga bisani a ba kamfanonin gine-gine masu zaman kansu da sauran al’umma damar su shigo. A yanzu ba haka al’amarin yake ba, komai ya canja. Wuraren da aka tanada domin shaƙatawa da shuka furanni, an mayar da su wuraren shagulgula na jeka-na-yi-ka. A halin yanzu, mutum zai yi wuya ya bambance unguwannin zaman jama’a masu cunkoso da marasa cunkoso ko kuma ya bambance su da unguwannin da aka ware domin gudanar da kasuwanci.

A can baya, sai ka ga wurin da aka ware domin gidajen zama, sai a mayar da su wuraren kasuwanci. Wannan yana haifar da karya tsarin birnin tare da haifar da cinkoson ababen hawa da takura wa rayuwar mutane. Duk da cewa an ɗauki wasu mutane aikin share tituna, ta amfani da tsintsiya, aikin nasu bai wadatarwa; kodayake wannan ma wata hanya ce ta samar da aikin yi. Amma yau da kullum mutum zai ta cin karo da ƙasa a gefen titi da sauran kayan datti. Murafun ƙarfen da ake rufe ramukan magudanan ruwa kuwa, sace su ake yi ɗaiɗai da ɗaiɗai.

Haka ma aikin kwashe shara da ake yi da motoci, shi ma bai gamsarwa, musamman ma yadda mutane suka sangarce da ɗabi’ar zubar da shara a ko’ina. Wannan ne ya sanya ya zama abu mai wahala a raba birnin da datti, musamman ma yadda al’umma ke ƙaruwa cikin sauri. Sai dai kuma da a ce hukumomin da abin ya shafa za su zage damtse, su yi aiki tuƙuru, za su iya samun nasarar magance waɗannan matsaloli da aka ambata a baya.

Matasan Da Ke Gararamba A Titi:

A ranar Asabar, 2 ga Satumba, 2023 da tsakiyar rana, a Unguwar Wuse Abuja, a daidai wata hanya kusa da babbar hanya; a gaban idanun mutane na ga wasu yara matasa suna dambe da juna. A kusa da su, akwai wasu yaran su shida suna kallon su, ba tare da sun raba su ba. Na ga wani mai gadi da yake cikin yunifom ya tsaya kusa da wajensu, yana ba su haƙuri da su daina faɗan amma ba su kula shi ba. Sauran abokansu kuwa suna ta zagaye-zagaye suna ta hayaniya tare da zuga su. A daidai lokacin ne na gan su, don haka sai na je wajen da suke faɗan, na lallashe su, na ce su daina faɗan. A yayin da suka ga cewa ga dattijo da hurhura ya zo yana ba su haƙuri, sai suka amince suka daina faɗan. Ganin haka sai na tambaye su dalilin da suke yin wannan rigima.
Ɗaya daga cikinsu ya ce mani suna rigima ce saboda wasu kuɗi da aka ba su kyauta domin su raba. Shi ne na yi masu nasiha, na ce masu ai bai kamata su riƙa faɗa saboda kuɗin ba, domin idan suka ji ciwo, kuɗin da suke faɗa a kansu ba za su iya saya masu magani ba.

Saboda in raba rigimar sai na fito da wani adadin kuɗi, na riƙa ba su ɗaya bayan ɗaya. Ina cikin raba masu kuɗin nan, sai suka lura da cewa adadin da suka rage a hannuna ba za su isa kan wasu ba, sai suka fizge sauran da ke hannun nawa. Na yi farin ciki, ganin cewa na sasanta su, don haka sai na kama hanya na tafi zuwa harkar gabana.
A kullum za ka ga matasa suna gararamba a wuraren kasuwanci da manyan shagunan zamani suna bara. Sai mutum ya gama sayayya zai shiga motarsa, sai su baibaiye shi suna barar kuɗi. Ko’ina haka za ka ga irin waɗannan matasa. Da irin wannan yanayi, mutum ba zai iya tantance yadda rayuwar matasan nan na Abuja za ta kasance a gaba ba.
Daga yadda al’amura suke, yadda suke gudanar da rayuwarsu, akwai matsala da haɗari ga su kansu da kuma al’umma. Abu ne mai sauƙi matasan nan su zama ‘yan daba, musamman ma ganin cewa da yawansu ba su yi makaranta sun samu ilimin zamani ba. Haka kuma ba su da tunanin yadda za su koyi wata sana’a koda noma ne.

Matsalolin ‘Yan Fashi Da Makami:

A dai wannan rana ta Asabar da maraice, na tattauna da wata mata, wacce take sayar da abinci a wani wuri a Unguwar Matana. Matar tana zaune ne a Unguwar Mpape, wajen garin Abuja. A yayin tattaunar tamu, na tambaye ta yadda rayuwa take a can unguwarsu ta Mpape. Ta ce a kullum suna zaman zullumi, domin a kullum suna iya ganin hukumomi daga Abuja ɗauke da takardar rusau, kasancewar zaman wucingadi suke. A kowane lokaci idan hukuma na son gina wurin, tana iya tada su. Da na tambaye ta batun ruwan sha kuwa, sai ta shaida mani cewa suna sayen ruwa ne daga hannun ‘yan-ga-ruwa amma kasancewar yanzu ana cikin damina ne, sukan tarbi ruwan sama daga rufin kwanon gidajensu.

Matar nan ta shaida mana cewa suna da babbar matsalar da ta fi ta ruwa, watau matsalar tsaro. Ta ce a garin Mpape, matsalar fashi da makami ta zama ruwan dare. Ta shaida mani yadda ita kanta a kwanakin baya, ‘yan fashi suka fasa ɗakinta suka kwashe tukunyar girki da janareta. Ta ce ta yi sa’a, a lokacin tana cikin uwar ɗaki amma da wataƙila sun naƙasa ta ko ma ta rasa rayuwarta.

Da na tambaye ta batun jami’an tsaro kamar ‘yan sanda, sai ta ce mani akwai ƙaramin ofishin ‘yan sanda a garin Mpape, kuma wani lokaci mutum zai riƙa jin jiniyar motarsu suna faturun. Sai dai ta ce mafi yawan lokaci sukan iso wurin da ake aikata laifi a makare, bayan ɓarayin sun gama aika-aikarsu sun gudu. Ta ce ɓarnar da matasan ‘yan fashi da makami ba ta tsaya ga gidajen mutane kawai ba. Ta ce sukan uzura wa mutane a kan hanya, musamman waɗanda ke dawowa daga aiki ko sana’a daga sassan Abuja. Ta ce akan samu wasu gurɓatattun da ke fashi da motar haya, da ake kira da suna “Wancans.” Irin waɗannan masu yaudarar mutane su shiga motarsu, sai sun raba tsakiya su yi wa fasinjoji fashin kayansu, kamar waya da kuɗi, sannan su turo su ƙasa daga cikin motar, su wuce.

Ta ci gaba da shaida mani cewa, wasu lokutan ‘yan fashi kan afka wa motocin haya. Ta ce sun taɓa afka wa fasinjojin wata mota suka amshe masu dukiya, inda ɗaya daga cikinsu ya yi wa ‘yan fashin turjiya. Su kuma suka sassare shi da wuƙa, suka fasa masa ciki. Ta ce irin wannan na faruwa a cikin mutane, wani lokacin ma har kusa da inda ‘yan sanda suke. A cewar ta, wannan dalili ya sanya zirga-zirga zuwa Mpape ta zama wani abu na kasada da tsoro. Sai dai duk da haka, ta ce ita ba ta fasa zirga-zirgar fita da shiga zuwa Mpape ba a kullum, domin ya zamar mata wajibi ta fito neman abinci, zuwa Unguwar Maitama, inda take sana’ar sayar da abinci. Watau daidai wurin da na same ta kuma muka tattauna. Ta ce a nan wurin ma tana fuskantar takurawa daga jami’an duba-gari, waɗanda suke sintiri, domin tsaftace gari.

Matar nan ta ce daga lokaci zuwa lokaci, jami’an duba-garin nan sukan kwashe mata abinci. Wasu lokutan kuma sai daga baya su maido mata da kwanuka da tukwanen girkinta, bayan sun “zubar” da abincin, kamar yadda suke faɗa. Wani abin da zai ba mutum mamaki da jami’an duba-garin na Abuja, shi ne yadda suna gani ƙofofin magudanan ruwa na zubar da ƙazanta a manyan tituna saboda cunkushewa, maimakon su maida hankali kan gyara wannan sai suka gwammace su riƙa uzura wa masu ƙananan sana’o’i.

Matsalolin Naƙasassu Da Mabarata:

Matuƙa motoci a Babban Birnin Tarayya Abuja suna ganin abin tausayi da takaici a kullum, musamman a bakin manyan hanyoyin birnin da wuraren turakun fitilun bada hannu. Da zarar an ce maka jar fitila ta kunna, motoci sun tsaya, nan da nan za ka ga ƙananan yara suna tura naƙasassu a cikin keken guragu da mabarata za su yi ta tururuwa zuwa ga motocin da suka tsaya da nufin bara. Akwai irin waɗannan wuraren da dama a Abuja, musamman ma dai da Yankin Wuse.
A can baya zamanin mulkin Obasanjo, an kawar da naƙasassu da mabarata daga titunan Babban Birnin Tarayya Abuja, amma a yanzu sun dawo. Ga dukkan alamu, hukumomin Abuja sun ankara da dawowar wannan matsala, wanda haka ya sanya suke ta sanarwa a kafafen watsa labarai, cewa mutane su daina ba su sadaka. Sai dai kuma wannan matakin na lallashi ba zai iya magance matsalolin mabarata ba, domin kuwa mutane suna bayar da sadaka ne bisa imani da addininsu ko wata fahimta ta ƙashin kansu. Ke nan akwai buƙatar a ɗauki matakai ƙwarara da suka dace, domin magance wannan matsala.

Kammalawa:

Har yanzu ba a makara ba, madamar ana son sake ɗora ginin Babban Birnin Tarayyar Najeriya bisa daftarin tsarin gininta na asali. Hakan mai yiwuwa ne idan aka yi koyi da yadda aka gina wasu manyan biranen wasu ƙasashen duniya. Misali, kamar birnin Washington na Amurka (shekarar 1800), birnin Canberra na Austaralia (shekarar 1927), birnin Brasilia na Brazil (shekarar 1960) da kuma birnin Dodoma na Tanzania ( shekarar 1996). Hukumomin ƙasashen nan sun yi tsayin daka wajen samar da gine-gine da abubuwan more rayuwa a biranen, ta hanyar bin ƙa’idoji da daftarin tsarin ginin na asali.

A Babban Birnin Tarayya Abuja ma za a iya kawo gyara a tsarin ginin, idan aka tunkari gyara matsalolin da ke akwai yanzu, sannan a sanya matakai masu ƙarfi na hana sake afkuwar su a gaba. Idan aka sanya niyya kuma aka ɗauki gyaran da gaske, nan da shekara 30 mai zuwa, birnin Abuja zai zama ƙayataccen birnin da ‘yan ƙasa za su yi alfahari da shi.

~~~~~~~
Dokta Bukar Usman, marubuci, masanin harkokin tsaro, tsohon Babban-Sakatare a Fadar Shugaban Ƙasa ne. Ya rubuta wannan muƙala a ranar 14 ga Satumba, 2023.
~~~~~~~

Previous Post

CURRICULUM VITAE OF RASULULLAH (صلي الله عليه وسلم)

Next Post

BATUN SULHU DA ‘YAN TA’ADDA A JIHAR KATSINA: Abin Da Ya Kamata A Fahimta

Related Posts

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna
Babban Labari

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

January 14, 2026
Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin
Babban Labari

Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

January 4, 2026
Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci
Babban Labari

Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci

January 3, 2026
Next Post
BATUN SULHU DA ‘YAN TA’ADDA A JIHAR KATSINA: Abin Da Ya Kamata A Fahimta

BATUN SULHU DA 'YAN TA'ADDA A JIHAR KATSINA: Abin Da Ya Kamata A Fahimta

Comments 2

  1. Yakubu Muhammad Rigasa says:
    2 years ago

    Na karanta wannan maƙala tsaf! Abin da na lura da shi lallai akwai jan aiki a gaban hukumomi da bai kamata suyi sako-sako da shi ba matuƙar suna son mayar da tsarin Birnin Tarayya Abuja bisa daftarin ginin sa na asali.
    Babban abin da ke haifar da cunkoso a manyan biranen ƙasar nan ciki kuwa har da Abuja shi ne, tsananin rayuwa da ƙaruwar talauci musamman a garuruwan da ke nesa da birane. Hakan ya faru ne saboda rashin bai wa ƙananan hukumomi cikakken ikon gudanar da kason kuɗaɗen su daga asusun tarayya (LG financial autonomy). Da za a rinƙa ba su kuɗaɗen su kai-tsaye, da kuwa tabbas da yawan mutane ba za su dinga yin hijira zuwa cikin birane ba. Amma rashin yin hakan ya haifar da talaucin da ke ƙaruwa tare da bunƙasar yawan jama’a.
    Idan aka sami damar rage yawan cunkoson jama’a, to za a sami sauƙin gudanar da tsare-tsaren da za su maido da Abuja bisa turbar daftarin tsara ginata na asali. Sannan rage cunkoson zai rage barazanar rashin tsaron da birnin ke fuskanta da kuma rashin tsaftace shi kamar yadda ya kamata.

    Reply
    • Bashir Yahuza Malumfashi says:
      2 years ago

      Madalla da wannan sharhi. Muna godiya sosai.

      Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Bakan Gizo

August 27, 2023
Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

December 27, 2025
TA’AZIYYAR PAPAROMA FRANCIS: SHIN INA LAIFIN PANTAMI?

TA’AZIYYAR PAPAROMA FRANCIS: SHIN INA LAIFIN PANTAMI?

April 22, 2025
TASKAR GIZAGO Adds category

TASKAR GIZAGO Adds category

September 8, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation
  • Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco
  • Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026
Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

January 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.