BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (5)
Bashir Yahuza Malumfashi
✓Ganawa Da Tattaunawa Da Mashahuran Mutanen Biu:
A yayin wannan muhimmiyar ziyara da na kai a karin farko zuwa Birnin Biu na Jihar Borno, na gana da wasu daga cikin mashahuran mutanen garin, waɗanda na ji daɗin gamuwa da su saboda dalilai masu yawa. Waɗannan mutane kuwa sun haɗa da Mai Martaba Sarkin Biu, Mai Mustapha Umar Mustapha II da Dokta Bukar Usman, OON, wanda na ziyarci gidansu na gado kuma na yi katarin ganawa da yayarsa, Hajiya Marabi Usman. Haka kuma na gana da Betaran Biu, Laftanan-Janar (mai ritaya) Tukur Yusufu Buratai, CFR da Birman Biu da Sarauniyar Biu. Haka kuma a ziyarar da na kai Asibiti Na Farko na garin Biu, na gana da Shugabar Asibitin. Na gana da ɗan kishin ƙasa, wanda ake wa lakabi da Ɗan Najeriya, Dibal Arhyel Wandali. Haka kuma na gana da aboki kuma amini, wanda ba zan mance da shi ba, Malam Umar Mohammed Maidala.
✓Mai Martaba Sarkin Biu, (Dokta) Mai Mustapha Umar Mustapha II, CON:
Mai Martaba Sarkin Biu, Mai Mustapha Umar Mustapha II, shi ne Sarki na 29 a Masarautar Biu kuma ya samu kansa a gadon sarauta ne bayan rasuwar mahaifinsa, Sarkin Biu Mai Umar Aliyu a shekarar 2020.

Kamar yadda ya bayyana mani a yayin tattaunawa da shi, ya ce mani kafin ya gaji mahaifinsa a gadon sarauta, sai da ya kwashe shekaru 22 a matsayin Hakimin Biu. “Bayan na gama karatu sai aka naɗa ni Hakimin Biu, inda na kwashe shekara 22. Da ma mahaifina Mai Umar, shi ya fara Hakimi a Biu, sai Hakimi Mai Madu. Daga nan aka zo aka raba Biu zuwa yankuna biyu, Biu ta Yamma da kuma Biu ta Gabas. Ni aka ba Hakimin Biu ta Gabas, an ba ni a Agusta 1999 kuma a wancan lokacin, akwai dattijanmu da suka yi haɗari. Kan haka sai aka ɗaga ni, aka ba ni hakimci na cikin gari a shekarar 2000. Na riƙe Biu ta Gabas, tsawon shekara takwas, Allah Ya yi wa babana Hakimi Mai Madu rasuwa, na riƙe Biu ta Yamma tsawon shekara 3, daga nan sai aka kawo Hakimi daga Kwaya Bura, sai aka sake mayar da ni Biu ta Gabas, inda na yi shekara biyu, sai aka sake yi mani canji, aka kai ni Biu ta Yamma. Aka kawo Ali Kachalla, ya maye gurbina a Biu ta Gabas. Nan muka yi aiki shekara biyar da shi. Daga nan Allah Ya yi masa rasuwa kuma aka sake mayar da ni Biu ta Gabas, aka ɗauko Hakimi Bello Usman, aka kawo shi ya maye gurbina a Biu ta Yamma. Iya wannan shekaru na yi a matsayin Hakimi a Biu.”
Sarkin Biu jarumi ne kuma jajirtacce a kan al’ummarsa. Manomi ne, wanda ba ya da kasala, wanda kuma a kullum yake huɗuba da jawo hankalin al’ummarsa domin su kasance masu son zaman lafiya, masu neman ilimi kuma masu aiki ko sana’a.
Na tambaye shi cewa, a cikin kwanakin nan biyu da suka gabata, an yi abin tarihi a wannan gari, inda aka naɗa wasu fitattun mutane a sarautu daban-daban. Shin wane abu kuka yi la’akari da shi wajen ba su waɗannan sarautu? Shi ne ya amsa da cewa: “Mutane uku da muka karrama a Jumu’ar da ta gabata, watau Betara da Shettima da kuma Zannah, dukkansu sojoji ne kuma sun taka rawa sosai wajen ci gaban Masarautar Biu. Misali, suna taimaka wa yaranmu wajen sama masu guraben aiki da taimaka wa al’umma. Haka kuma suna yin iyaka ƙoƙarinsu wajen gina al’umma da Masarautar Biu, duk inda suka ga wata dama ko wata hanya da za su kawo ci gaba ga yankinmu, suna yin haka da ƙarfinsu da dukiyarsu. Don haka aka ba su waɗannan sarautu, domin karrama su a idon duniya kuma domin ƙarfafa masu gwiwa, su ci gaba da yi wa al’umma hidima.”
Ana yaba wa Sarkin Biu saboda jajircewarsa wajen kula da al’ummarsa. A cikin tattaunawar da na yi da shi, na kawo masa batun irin matakan da ya ɗauka a shekarun baya dangane da ’yan Boko Haram da suka yi ta mamaye yankunan Jihar Borno. Na tambaye shi cewa, a lokacin da hare-hare suka yawaita, har ta kai ga sun halaka Sarkin Gwoza amma kai a lokacin ka tsaya tare da mutanenka, ka ce ba za ka je ko’ina ba, kana tare da mutanenka. Yallaɓai ko za ka yi mana karin bayani game da wannan mataki da ka ɗauka?

Ya amsa da cewa “Alhamdu lillahi. Lokacin da aka fara wannan matsala, mahaifina yana da rai. Ni kuma a lokacin ni ne Hakimin cikin gari kuma ni ne Magajin Gari. Duk wasu abubuwa idan sun taso, musamman waɗanda suka shafi tsaro, sai ya ce a je a samu Maidala. Kan haka, duk wani abu da ya gagari Maidala, sai ya zo ya nemi shawara a wurina. An samu kimanin shekara biyar, duk ni ke kula da waɗannan al’amura.
“Lokacin da mutanen Boko Haram suka zo Biu, har sun fara dauki-ɗaiɗai. A haka muka riƙa bin abin a hankali, har aka kame su duk. Wasu an kai su Maiduguri, wasu har yanzu ba mu san inda suke ba. Da haka muka samu aka zauna lafiya kuma kowace unguwa suka kafa ’yan-sa-kai, suka zama masu gadin unguwanninsu.
Matasa sukan samu itace su hura wuta suna gadin unguwanninsu da dare, sai gari ya waye suke barci. Har ga Allah, mutanen Biu jarumai ne, waɗanda ya kamata a yaba masu, domin sun yi ƙoƙari.”
Akwai al’amura na zahiri da suka faru amma babban abu mafi muhimmanci, ita ce addu’a. Mun roƙi Allah Ya taimake mu. Lokacin da abin ya gawurta na ce babu inda za ni, an kira ni daga Abuja, aka ce in bar garin, domin abin yana ta matsowa da sauransu. Shi ne na ce to idan na bar gari, na bar mutanena, idan abin ya wuce kuma in ce zan dawo, to a sunan me? Na ce don haka sai dai mu tashi mu yi himma, mu yi roƙon Allah. Babu shakka har sun kawo hari da bama-bamai, har sun kawo nan wajen barikin ’yan sanda amma Allah Ya ba mu nasara. Da suka zo barikin ’yan sanda, sai aka yi masu kwanton ɓauna, aka mayar da su, ma’ana aka kore su. Don haka alhamdu lillahi, mun gode wa Allah.”
✓Dokta Bukar Usman, OON:
Kamar yadda na faɗa a can baya, na fara haɗuwa da Dokta Bukar ne tun a shekarar 2006 a Abuja kuma babban abin da ya haɗa ni da shi, shi ne aikinsa na hidimar bunƙasa ilimi ga al’umma da ya saba. Shi ne jigon da ya sanya na ƙara shaƙuwa da al’ummar Biu, musamman yadda na fahimci cewa mutane ne masu ƙaunar jama’a, masu kishin ƙasa. Hasali ma, a dalilinsa ne na ɗarsu da sha’awar in ziyarci Masarautar Biu. Kuma shi ne ma ya yi uwa, ya yi makarɓiya wajen ɗawainiya da ni tun daga zuwa na garin har zuwa na kai ga dawowa. A lokacin da na je Biu, hankalina bai kwanta ba, har sai da Malam Mohammed Umar Maidala ya kai ni gidansu Dokta, ma’ana mahaifarsa. Na kuwa yi sa’ar ganawa da yayarsa shaƙiƙiya, Hajiya Marabi Usman, wacce a bana ta cika shekara 89 a duniya, kasancewar an haife ta a shekarar 1935.
Na same ta cikin ƙoshin lafiya, ga ta da fara’a da yawan murmushi. Ta bayyana mani cewa ɗan uwanta, Dokta Bukar mutum ne mai mutunci da zumunci, domin kuwa ya riƙe su da daraja da mutunci. Ba ta gushe ba sai da ta yi masa addu’a, cewa Allah Ya sa ya gama da duniya lafiya. Ni kaina, ta yi mani addu’a, sannnan ta nuna mani matuƙar farin ciki da godiya saboda wannan ziyarar da na kai mata.
Wane ne Bukar Usman? A tsawon shekara 18 da na san shi, zan iya cewa shi mutum ne kamilallen dattijo. A batun gaskiya, ban taɓa haɗuwa da mutum irinsa ba, musamman ta fuskar dattijantaka, kishin ƙasa, son jama’a, tausayin marasa galihu da kuma son ilimi da yaɗa shi ga al’umma.

An haife shi a ranar 10 ga watan Disamba, 1942. Yadda yake tafiyar da rayuwarsa tun daga tushe zuwa ɗaukakar matsayi, abin koyi ne ga al’ummar wannan zamani da ma masu zuwa nan gaba. Tun da farko ya fara aiki ne a matsayin ƙaramin jami’i a Gwamnatin Tarayya. Hazaƙarsa da himmarsa a aiki sun ba shi damar samun ɗaukaka da ci gaba, inda ya riƙa samun ƙarin girma a lokacin da ya dace. Ta kai ga sai da ya kai muƙamin Babban Sakatare a Fadar Shugaban Ƙasa, inda ya yi ritaya daga aiki a shekarar 1999.
Mutum ne shi wanda abin duniya bai dame shi ba. Ba ya da haɗama ko son tara dukiya. Dalili ke nan bayan ya yi ritaya, sai ya sadaukar da rayuwarsa wajen bincike da nazari tare da rubuce-rubucen littattafan ilimi, wanda babu shakka ta haka yake taimakawa wajen bunƙasa ilimi da faɗakar da al’umma da adana tarihi domin al’umma mai zuwa nan gaba. Ya kasance yana amfani da dukiyarsa wajen ɗaukar nauyin nazari da binciken ilimi, sannan yakan wallafa muhimman littattafai a fagagen ilimi daban-daban, musamman ma adabi da sauransu. Kuma mafi yawa daga littattafan da yake samarwa ta hanyar Gidauniyar Bukar Usman, kyauta yake raba su ga al’umma da makarantu da cibiyoyin ilimi na sassan ƙasar nan, har ma da ƙasashen waje.
Shi mutum ne mai son gaskiya da ganin an yi gaskiya. Ta hanyar ayyukansa da mu’amalarsa, mutum zai shaida haka. Dalilin ke nan duk abin da ya rubuta, ko dai a littafi ko kuma a muƙala, za ka tarar babu abin da yake nusarwa sai a yi gaskiya kuma a tsare gaskiya. Haka ma a fagen kishin ƙasa, ba ya da sanyi. A muƙalolinsa da suka shafi al’amuran ƙasa da mulki da tsaro, mutum zai nazarci yadda kishin ƙasa ya zame masa tamkar jini da tsoka. Wasu daga littattafansa da suka haɗa da Voices in a Choir…, My Public Service Journey, Hatching Hopes da A History of Biu da kuma Taskar Tatsuniyoyi da sauransu; cike suke da misalai na yadda ya sadaukar da kansa domin gina al’umma da sanya masu karsashi domin su zama cikin kishin ƙasa da tallafa wa al’umma. Ta fuskar son ilimi da yaɗa shi ga al’umma kuwa, zan shaidi Dokta Usman da cewa shi malami ne na ƙwarai. A batun koyo da koyarwa, Dokta ba ya jin nauyin ya tambayi abin da bai sani ba daga wani, koda kuwa wanin nan yaro ne ƙarami. Haka kuma ba ya da ƙyuya a yayin aikinsa na yaɗa ilimi, zai sadaukar da kansa wajen koya wa mutum abu har sai ya iya. Idan ya ga kuskure a tare da aikin wani, zai bi cikin hikima da basira domin kawo gyara. Wannan ɗabi’arsa ce ga duk wanda ya kusance shi, zai shaida haka. Ni dai na koyi ilimi mai tarin yawa daga gare shi kai tsaye kuma daga muƙalolinsa da littattafansa.
Mutum ne shi mai tsafta a zahiri da baɗini. Idan ka je gidansa, za ka shaida haka, domin tun daga muhallinsa da suturarsa da abin hawansa, mutum zai gane cewa shi mai tsafta ne kuma mai son tsaftace duk wani datti da ke muhallinsa. Haka kuma mutum ne mai tsaftar zuciya da tausayi – ba za ka same shi wajen aikata mugun abu ba. Ba ya saka kansa cikin aikin tu’annati kuma yana kiyaye kansa daga shiga shirgin da babu ruwansa a ciki. Mutum ne mai kyauta da karimci da daraja mutane. Ga shi mai kyautata wa baƙi da maƙwabta. A duk lokacin da mutum ya ziyarci Dokta Usman, koda yaro ne shi, zai shimfiɗa masa fuskar karimci, ya kyautata masa.
Wannan shi ne Dokta Bukar Usman, dattijo mai dattijantaka, karimi mai karimci, hadimin jama’a, garkuwan adabi.
✓Betaran Biu Janar Tukur Yusufu Buratai, CFR:
A rahotona a can baya, na bayyana yadda na haɗu da Janar Buratai, wanda shi ma ya kasance ɗaya daga cikin muhimman mutanen da suka ƙara sanya ni sha’awar al’ummar Babur/Bura. Haka kuma, yana daga cikin dalilan da suka sanya na ziyarci Masarautar Biu a wannan karon, musamman domin shaida naɗin da aka yi masa na babbar sarautar Betaran Biu a ranar Jumu’a 27 ga Oktoba, 2023.
Wane ne Laftanan-Janar (mai ritaya) Tukur Yusufu Buratai? An haife shi a ranar 24 ga Nuwamba, 1960 a garin Buratai, Ƙaramar Hukumar Biu, Jihar Borno. Ya yi aikin koyarwa kafin daga bisani ya shiga aikin soja. Ya samu ɗaukaka, inda ya kai ƙololuwar muƙami, ya zama Hafsan Hafsoshin Rundunar Sojojin Najeriya na 20, a ranar Litinin 13 ga Yuli, 2015. Shi ne Shugaban Rundunar Sojojin Najeriya mafi daɗewa a kan mulki, inda ya shafe tsawon shekaru shida cur. Ya yi ritaya daga aiki a Janairu, 2021.
A zamaninsa, Sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara, musamman ma a yaƙi da Boko Haram da suka addabi Arewa Maso Gabashin Najeriya. Kafin ya amshi ragamar shugabancin sojojin Najeriya, ƙananan hukumomi da yawa a Jihohin Borno da Yobe suna hannun ikon ’yan Boko Haram, kamar yadda kuma ake samun tashe-tashen bama-bamai a kusan ko’ina a Arewacin Najeriya, har ma da babban Birnin Tarayya, Abuja. Amma Allah da ikonSa, bisa himma da jajircewar Janar Buratai, an samu galaba, aka fatattaki ’yan Boko Haram, har ma aka samu nasarar kashe shugabansu, Abubakar Shekau.

Kafin hawan Buratai shugabanci, Rundunar Sojan Najeriya ta yi fama da matsaloli masu yawa, waɗanda suka haɗa da rashin ingantattun kayan aiki da rashin walwala da karsashin jami’ai. Bisa himma da ƙwarewarsa, ya samar da kayan aiki, inda ta kai ga sai da rundunar ta fara ƙera motocin sulke na Nzeogwu da kuma bindigogi. Haka kuma ya samar da karsashi ga dakarun Najeriya, musamman ta hanyar inganta albashinsu da alawus-alawus da samar masu da horo iri-iri. Saboda gamsuwa da aikinsa, bayan ya kammala shugabancin Rundunar Sojojin Najeriya, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya naɗa shi muƙamin Jakadan Najeriya a Jamhuriyyar Benin.
Janar Buratai mutum ne jarumi kuma mai kishin ƙasa, kamar kuma yadda ya samu amsuwa daga dukkan sassan Najeriya, har ma da ƙasashen waje. Sarakunan gargajiya daga dukkan sassan Najeriya sun naɗa shi sarautu iri-iri, kusan guda 30. A Masarautarsa ta haihuwa, Sarkin Biu ya naɗa shi muhimmiyar sarautar Betaran Biu, a ranar Jumu’a 27 ga Oktoba, 2023. Wasu daga cikin sarautunsa sun haɗa da Garkuwan Keffi, Baakore na Akure, Jagunmolu na Ƙasar Shaki, Are Balogun Agba na Owu-Kuta, Sadaukin Jajere, Jarman Maradun, Ochiagha Dike Eji Eja Ogu-Aguleri, a Jihar Anambara. Shi ne Garkuwan Yusufari, Majen Doma da Magayaƙin Ƙasar Hausa a Daura Jihar Katsina.
A tattaunawar da na yi da shi a gidansa da ke Biu, na ƙara tabbatar da cewa lallai Janar Buratai mutum ne mai kishin al’umma da Najeriya gaba ɗaya. Ya nuna damuwarsa game da yadda matasa suke rayuwa a musamman Arewacin Najeriya, dangane da rugujewar tarbiyyarsu. Ya nuna damuwa yadda suke zaman kashe wando, wasu kuma suke jefa rayuwarsu cikin shaye-shaye da sauran munanan ayyuka. Na tambaye shi ko wace shawara zai bayar domin ganin matasan sun samu saiti a rayuwa? Ya amsa da cewa:
“Lallai ne iyaye su sanya ido sosai ga ’ya’yansu, musamman ma yadda suke tu’ammali da kafafen zamani a soshalmidiya. Haka kuma Hukumar Wayar da Kan Al’umma, wato National Orientation Agency (NOA) tana da aiki sosai a gabanta. Dole ne ta sanya ido, ta yi aiki tuƙuru ta hanyar kula da al’adu da addinanmu wajen faɗakarwa da cusa wa matasanmu tarbiyya.”
Ko yaya yake kallon rayuwa? Janar Buratai ya ce: “Al’amarin rayuwar duniya sai haƙuri da juriya. Ba a samun biyan buƙata sai da haƙuri, domin shi ne muhimmi a dukkan al’amura.”
Na tambayi mai Martaba Sarkin Biu, Mai Mustapha Umar Mustapha II game da dalilin da ya sanya ya amince da naɗa Janar Buratai sarautar Betaran Biu. Shi kuma sai ya bayyana cewa: “To, alhamdu lillahi. Misali game da shi Janar Buratai, ya yi mana rawar gani a Masarautar Biu. A can baya babbar makarantar da muke da ita, ita ce College of Education. Baya ga ita, babu wata babbar makaranta sai a Maiduguri kuma ba kowa ne zai iya samun gurbin karatu a Jami’ar Maiduguri ba, ba kuma kowa ne yake da kuɗin da zai tura ɗansa ko ’yarsa karatu a can kuma ya jure ɗawainiyar zaman birni ba. Lokacin da Allah Ya ba shi dama, sai ga shi ya yi sanadin kawo mana Jami’ar Sojoji a Biu. Ga shi an yaye ɗalibai na zangon karatu na farko kuma dalili ke nan ya sanya muka haɗa da naɗinsa, saboda yaba masa dangane da abubuwan alheri da dama da ya yi mana a wannan Masarauta ta Biu.
“Game da sarautar Betara da aka ba shi kuwa, to ba kowace sarauta ce take lallai sai ɗan gado ba. Ita sarautar Betara, tana cikin rukunin waɗanda suke zaɓen Sarki. A yarenmu, Kokuna Kamba, wato Kisawa, masu zaɓen sarki ke nan. Don haka mutumin da ya kawo maku abubuwan alheri haka, ai kuwa ya cancanci a karrama shi da muƙami. Kuma wannan cikon wasiyyar mahaifina ce, domin a lokacin da yake raye, kullum yana cewa me ya kamata mu yi wa Buratai? Na ce lokaci yana nan zuwa. Don haka ya ce mani in yi masa alƙawari, ko ba ya da rai, zan ba Buratai sarauta. Allah da ikonSa, ga shi na cika alƙawari.
“Haka kuma Betara tamkar Jakada ne,’ da zan iya tura shi ko’ina ya wakilce ni, idan an gayya ce ni. Don haka ba a ba kowa wannan sarauta ta Betara sai fitaccen mutum mai kishin ƙasa da kishin al’umma. Dalili ke nan aka ba Janar Buratai wannan sarauta ta Betara, domin kuwa lallai ya nuna mana halacci.”
✓Birman Biu, Barista Ibrahim Shehu:
Birman Biu, Barista Ibrahim Shehu, shi ma jigo ne a Masarautar Biu. Masanin Shari’a ne mai matuƙar ilimi. Baya ga Sarki, shi ne mai riƙe da sarauta mafi girma a Masarautar Biu. Za a iya cewa shi ne a mataki na biyu daga Sarki. Yana ɗaya daga cikin masu zaɓe da naɗa Sarki, idan buƙatar haka ta taso. Haka kuma shi ne mashawarcin Sarki na kusa-kusa. Shi ne ke jagorar duk wani taron tattaunawa tsakanin fadawa a masarauta.
A tattaunawata da shi, na tambaye shi cewa shin idan za ka kwatanta jiya da yau, waɗanne bambance-bambance ke akwai a wannan Masarauta? Ya ce “Bambance-bambance tsakanin sarakunan jiya da yau, a da sarakuna suna shari’a, su ne ke da gwamnati, su ke da komai. Da Bature ya zo, ya rage masu girma, Kwansitushen ya zo ya amshe masu iko da sauransu. To mu a wajenmu, waɗannan abubuwa ne da zamani ya kawo amma dai masarauta tana nan a masarautarta, babu wani canji. Babu inda za ka ga an ɗauko wani a saka shi a sarauta, ma’ana a ce ya yi haye, shi ba jinin sarauta ba. Don haka mu nan babu abin da ya canja na sarauta. Sai dai a ce gaba ɗaya a yankin Najeriya ta Arewa. Canjin da aka samu na tsarin mulki na zamani, wanda za a ce an ji daɗin shi kuma an ji zafin shi. Amma duk da haka, idan abu ya taso sai ka ji ana cewa a koma ga al’adunmu na gargajiya kuma shi ne zai iya fidda mu.”

Birman Biu ya buƙaci al’umma su kula da rayuwa, su daina zaman banza, kowa ya kama aiki ko sana’a domin samun rufin asiri da zaman lafiya da juna. “Mu ci gaba da riƙe noma da ilimi, domin kuwa waɗannan su ne muhimman turakunmu a wannan yanki. Muna da ƙasar noma mai kyau, wanda idan ka duba dukkan yankunan nan, har zuwa wasu sassa na Jihar Yobe, duk daga nan ake kai wasu kayan abinci. Biu Allah Ya hore mana yanayin ƙasa mai kyau, ga mu a kan tsauni kuma muna tsakiyar dukkan Jihohin Arewa Maso Gabas.”
✓Sarauniya Hajiya Larai (A’isha) Mai Umar:
Na ziyarci Sarauniyar Biu, Hajiya Larai (A’isha) Mai Umar, inda ta amshi baƙuncinmu cikin karimci da murna. Da take bayyana mana tarihinta a taƙaice, ta ce: “An haife ni a shekarar 1967. Na yi Biu Central Primary School, bayan nan na je GGSS Minna, Jihar Neja. Mu ne ma ɗalibai na farko a wannan makaranta. Daga nan na wuce zuwa Jami’ar Maiduguri, har Allah Ya sa na kama aiki a nan Ƙaramar Hukuma ta Biu.”
Na tambaye ta cewa, a matsayinta na Sarauniyar Biu, ko yaya ayyukanta suke a masarauta? “Alhamdu lillahi. Abin da ake nufi da Sarauniya a Masarautar Biu shi ne, ana nufin kamar Sarkin Mata, wato shugabar mata ta fannin sarauta a Masarautar Biu (Queen Mother). Ta fuskar aikina, ni ce mai ba da shawara, musamman dangane da abin da ya shafi mata da sauran al’amuran rayuwa da suka shafi masarauta kuma a yi aiki da su.”
Ko akwai muƙamai ko sarautu da suka shafi mata a ƙarƙashinta? “Akwai su, kuma ana ce masu Magira. Musamman a ƙauyuka, Magira tana kusa da Hakimi. Tana da ayarin mata, misali kamar lokacin bikin Salla, sukan rako mata su zo su yi gaisuwa ko su rako dawakai idan za su fito daba,” in ji ta.

Ta fannin muƙamai ko sarautu, misali irin waɗanda ake naɗa maza, ko ana naɗa mata a ƙarƙashin naki ikon na Sarauniya? “Tsarin ba iri ɗaya ba ne da na Sarki, wanda shi ne uban ƙasa gaba ɗaya. Amma ta fuskar haka, hakimai na neman shawara da izini ta wajena, a lokacin da yake son naɗa Magira.”
A tsarin Sarautar Biu, ko akwai yiwuwar ke ma ki zama Sarki a babbar fada, tun da ke ma ɗiyar Sarki ce a bisa gado? Ta amsa da cewa: “A’a, wannan ba zai yiwu ba. Ba haka tsarin yake ba a Masarautar Biu. Iyakar mu dai wannan Sarauniya da Magira.”
Ko za ki ba mata masu tasowa shawara, yadda za su zama masu amfani ga kansu da al’umma baki daya? “Babbar shawarar da zan ba mata iyaye, ita ce su tsaya kai da fata su ga sun ilimantar da ’ya’yansu mata, domin kuwa ilimi shi ne komai na rayuwa. Idan mutum bai da ilimi, bambancinsa da dabba kaɗan ne. Ilimi garkuwa ne na rayuwa. Idan ka ilimantar da mace ɗaya, kamar ka ilimantar da al’umma ne gaba ɗaya. Kowace mace ta tsaye sosai ta ga cewa ’ya’yanta sun yi karatu sun samu ilimi.”
Sarauniyar kuma ta shawarci ɗaukacin al’umma da cewa: “Ina kira ga al’umma da su kula da rayuwa, su zama masu haƙuri a dukkan al’amura, domin kuwa ita rayuwa sai an haɗa da haƙuri sannan ake samun nasara. Haka kuma a sanya juriya, domin muddin aka ce mutum yana da haƙuri da juriya, to babu abin da zai gagare shi a rayuwar duniya. Idan ka yi haƙuri, abin da za ka samu, za ka fi jin daɗinsa. Da haƙuri da juriya suna tafiya tare ne da juna, domin duk tsawon tsanani, to akwai ƙarshensa. Na biyu kuma sai sana’a, ina kira ga mata da matasa, su rungumi sana’a. Sana’a abu ce babba, domin gwamnati, ko mutum ya yi karatu ba za ta iya ɗaukar kowa aiki ba amma idan kana da sana’ar yi, a ƙarƙashinka har za ka iya ɗaukar wasu su yi maka aiki. Kuma idan ka riƙe sana’a, ka yi gaskiya a ciki, to za ka samu biyan buƙata. Don haka a kullum shawarata ga mata da matasa shi ne, a rungumi sana’a, a jajirce, a yi gaskiya, sai Allah Ya sanya albarka a ciki.”
✓Shugabar Asibiti Na Farko a Biu, Malama Maimuna Ahmed:
Na samu zuwa kai ziyara Asibiti na farko a garin Biu, inda na tattauna da shugabar asibitin, wanda yanzu aka mayar da shi ɗakin shan magani (Primary Health Care), kasancewar an gina babban asibiti na zamani a yanzu. Tun a shekarar 1954 aka gina shi kuma har yanzu yana nan yadda yake, duk da cewa an ɗan yi masa kwaskwarima domin dacewa da zamani.
Malama Maimuna ta ce har yanzu suna gudanar da aikin asibiti kowanne, duk da cewa an samar da Babban Asibiti a Biu. “Idan an rubuta wa mutum magani a asibiti, yawanci a nan zai zo ya same shi. Haka kuma a nan ne ake kula da masu cutar kuturta (leprosy). Nan ake ba su magani tare da kulawa da su, musamman kuma da masu cutar tarin fuka (Tuberculosis) da na HIV. Haka kuma babu wani aiki da ba mu yi a wannan asibiti. Misali, muna amsar haihuwa, muna yin awo, muna kwantar da marar lafiya, kodayake a can baya, magani kawai muke bayarwa idan an rubuto wa mutum daga likita. Muna da isassun ma’aikata daidai gwargwado,” in ji shugabar asibitin.
Na tambaye ta cewa, ko al’ummar Biu za su so a ce an ɗaga darajar asibitin nan ya zama babba? Malamar ta amsa da cewa: “A gaskiya idan haka za ta samu, za mu ji daɗi, domin kuwa muna samun mutane da yawa da suke zuwa nan neman magani, musamman ma daga ƙauyuka. Wasu ma sukan mance da cewa akwai babban asibiti a Biu, nan suke zuwa da buƙatunsu na magani. A wata ɗaya, mukan samu marasa lafiya 500, idan ba mu samu ba shi ne mu samu 300 a wata, amma ba mu samun marasa lafiya ƙasa da haka.”

Yaya maganar kayan aiki da magunguna kuwa, kuna samun wadatattu kuma ingantattu daga gwamnati? “E, to gaskiya daga gwamnatin sai dai a hankali, ana samu amma ba sosai ba. Idan gwamnati ta ba mu sai muka ga ba zai isa ba, mukan sayo da kanmu domin amfanin al’umma. Amma idan za mu sayar, mukan karya farashinsa, ta yadda zai bambanta da na ’yan kasuwa a waje. Kuma daga yadda mutane ke tururuwa nan, suna nuna gamsuwa, domin a lokacin da mutum ya zo bai samu maganin da yake nema ba, yakan nuna rashin jin daɗi. Ma’ana, mutane suna son zuwa nan sayen magani fiye da waje. Suna son maganin da ake bayarwa a nan, domin suna da tabbacin cewa ba jabu ba ne, mai kyau ne,” a cewar Malama Maimuna.
✓Dibal Arhyel Wandali: Ɗan Najeriya:
Na samu kai ziyara gidan wani muhimmin mutum a Biu, wanda ake wa laƙabi da Ɗan Najeriya. Sunansa Dibal Arhyel Wandali. Mutum ne shi mai kishin ƙasa da son ganin Najeriya ta ɗaukaka, an samu zaman lafiya da ci gaba. Wannan mutum, saboda kishin ƙasa, komai nasa launin tutar Najeriya ne, Kore-Fari-Kore. Wannan kuwa ya haɗa da suturarsa, motarsa, kujerun zamansa, fenti ciki da wajen gidansa, agogonsa, hankici da sauransu, duk launin tutar Najeriya ne. Na tattauna da shi sosai kuma ga yadda tattaunawar ta gudana:
Da yake bayyana tarihinsa a taƙaice, ya ce: “An haife ni a wani ƙauye mai nisan kilomita 27 daga Biu mai suna Wandali. A can aka haife ni a shekarar 1963, na yi karatun firamare a 1970, inda na kammala a 1977. Daga can na fara da Community Secondary School. A lokacin mahaifina yana Bama, ya ce in je in same shi a can. Da na je Bama, kasancewar akwai ɗalibai manya, shi kuma yana malami ne a makarantar. Ni kuma sai aka mayar da ni wanda zai riƙa yi masu shara ko wanki. Na ce ba zan iya wannan makarantar ba. Daga nan aka kai ni Konduga, a dai wannan shekara. Na je Konduga na yi shekara biyu, a zangon farko na aji uku sai muka yi tawaye saboda akwai rashin ruwa da rashin gaskiya. A lokacin ina Mai Unguwa (Prefect), sai aka ce za a kore mu. Daga nan sai aka samo mani gurbi a Government College Maiduguri. A can na samu na gama karatun sakandare a shekarar 1982.
“Na yi abubuwa, domin na shiga Ramat Polytechnic domin nazarin kwas ɗin Injiniya amma ban zo na samu wannan ba. Daga nan gwamnati ta yi kira za a yi intabiyu domin a je koyon aikin lafiya a ƙasar waje. Na shiga intabiyun kuma na samu nasara, muka je ƙasar Bulgeriya. Na je can na yi ’yan shekaru, a shekarar 1987 na kammala kuma na dawo gida Najeriya.”

Bayan ka dawo gida sai ga shi ka zo da wata ɗabi’a ta nuna kishin ƙasa, ta yadda komai naka kana saka shi zuwa launin tutar Najeriya, kore-fari-kore. Shin ina ka samu wannan yanayi na kishi har ka ɗabbaƙa shi haka?
Dibal ya amsa da cewa: “Gaskiya tun ina yaro ƙarami na samu sha’awar kishin Najeriya. Ka san shugabanninmu na wancan lokacin, irin su Tafawa Balewa, idan an zo maganar Ranar ’Yancin Ƙasa ko Ranar Yara, za ka ga an sanya mu a layi, ana ba mu tuta ƙarama muna ɗagawa sama. Wannan tuta sai ta riƙa ba ni sha’awa kuma na ci gaba da bibiyar halayen waɗannan shugabanni na dauri. Tun daga nan na sanya wa zuciyata cewa ina son in zama irin waɗannan dattawa. A lokacin nan duniya tana da kyau. A can inda muka je karatu sai mu ga ana raina mana ƙasa, sai su riƙa tambaya ta, shin kuna da ruwa, kuna da kaza da kaza? Dalili ke nan na ɗauki niyyar wannan kamfen, domin in nuna wa duniya cewa wannan ƙasa fa muna kishin ta. A kan haka wata rana na dawo hutu, sai na sayi Katin Saƙo (Postcard), wanda ke ɗauke da hotunan Cocoa House da Hamdala Hotel ina aika wa abokaina a can ƙasar waje, domin su gane cewa ƙasarmu ma mai kyau ce kuma muna da wayewa. Kan haka na ɗauki niyyar cewa zan mayar da Najeriya ta zama takwara, domin karrama ta. Shi ne nake yin waɗannan abubuwa ta amfani da launin tutar Najeriya. Kamar sutura, fentin mota, kujeru, labule, fentin gida da sauransu.”
To, yaya batun iyalinka, ko su ma suna yin irin wannan ɗabi’a ko kuwa kai kaɗai ne? “To akwai wasu daga ciki suna ɗan kwaikwayyona amma ba dukkansu ba. Ka san su ’yan zamani ne sai abin da suka sanya kansu, suke sha’awa. Amma dai a gaskiya suna da kishin ƙasar a jikinsu, domin idan mun zauna sukan tambaye ni abubuwa da suka shafi ƙasa. Amma dai a ce su riƙa sanya sutura mai launin tutar Najeriya kamar yadda nake yi, sai su ce baba kaya iri ɗaya babu canji kullum?”
Na tambaye shi cewa, yadda ka yi suna a wannan ɗabi’a ta kishin ƙasa, ko ka taɓa samun ƙarfafa gwiwa daga gwamnati ko wata hukuma? Ya ce: “A’a, sai dai yara kamar ƙungiyoyin ɗalibai na Arewa sun karrama ni, sun ba ni kambi na karrramawa da kuma kungiyoyi masu kishin ƙasa suna yaba mani. Amma batun gwamnati babu abin da na taɓa samu, koda irin lambar yabo ba a ba ni ba. Ina tunanin irin wannan sai wanda yake da kuɗi ake ba.”
Ta ɓangaren aiki fa, wane irin aiki kake yi? “Ni ina aikin asibiti ne, a matsayin Jami’in Kiwon Lafiya. Kuma babu shakka in dai a fagen aiki ne, na riga na yi suna. Ta fannin aikin nan nawa, jihohi da yawa an san ni a ƙasar nan, balle kuma a nan Biu, zan iya ce maka babu inda ba a san ni ba kan aikina na kiwon lafiya.”
Na tambaye shi ko yana da sha’awar shiga harkokin siyasa? Ya amsa da cewa: “A’a, siyasa babu gaskiya a cikinta, duk da cewa ina sha’awarta, domin na fahimci cewa ta hanyar siyasa mutum zai iya kawo canji. Misali, hatta wannan aiki da nake gudanarwa na kiwon lafiya, Allah ne Ya ba ni kam, to amma ta sanadiyyar siyasa na samu. Akwai gwamnanmu, marigayi Mohammed Goni, wanda duk ya san shi, to ya san cewa ya yi aiki. Shi ne fa a lokacin da aka yi juyin mulki a 1983, yana ƙasar Saudiyya. Aka ce masa ana kama gwamnoni, sai ya ce a jira shi yana nan zuwa. Ya san ya yi gaskiya, sai kuwa ya dawo. A cikin ayyukan ci gaba da ya kawo, har yanzu muna amfana. Mu ’yan ƙauye ne a lokacin da aka yi intabiyu, sau uku fa ana yin intabiyun nan sai ya ga babu sunayen ’yan kauye, sai sunayen ’ya’yan attajirai, sai ya ce intabiyun ba tayi ba. Aka sake wata, aka kai ma shi, ya ga babu sunan mutanen ƙauye da karkara, ya ce ba ta yi ba. Daga nan ya ce a ba shi ƙimar nawa za a kashe domin Turawan su zo da kansu su zaɓi ɗaliban da suke so. Haka ya biya kuɗin jirgi, Turawan suka zo, aka sauke su a Lake Chad Hotel, a lokacin nan shi ne babban otel a Maiduguri. Mutanen nan suka zauna, suka yi mana intabiyu. Ta haka mu ’yan ƙauye muka samu shiga. To yanzu kuwa, ko ƙwallon nan da muke kallo, yaro ko ya iya, idan bai da wani da ya tsaye masa, ba zai samu shiga ba. Batun siyasa wataƙila nan gaba ta gyaru amma yanzu kam…”
A matsayinka na ɗan kishin ƙasa da ka ga jiya da yau, wace shawara za ka ba matasa na yau domin ɗora rayuwarsu bisa hanya mai kyau? “Gaskiya shawara kaɗai ba za ta yi aiki ba, sai ka gwada masu da misalai. Idan ina gaya wa matasa yadda ya kamata su yi kishin ƙasa, sai su ƙalubalance ni, cewa ni don na amfana ne da ƙasar, shi ya sa nake faɗin haka. Kuma wannan kamar gaskiya ne. Yaran da aka haifa daga 1980 zuwa yau, ba su ji daɗin ƙasar nan ba. Kuma ga shi ƙasar nan muna da dukiya amma babu wani ci gaba. Don haka idan za ka gaya wa matashi ya yi kaza, sai dai ka nuna masa da misali a aikace. Misali matashi zai ce maka ya gama jami’a amma bai samu aiki ba, babansa ya biya kuɗin makaranta, ya sha wahalar karatu amma babu aikin yi, to wane daɗi ya sha a ƙasar? Mu fa a lokacin muna yara, za ka ga hatta masu gyaran bishiya a bakin hanya, ana biyan su, aikinsu ke nan amma yanzu fa, me zai hana a riƙa ba matasan nan aikin sharar hanya da kula da muhalli? Koda Naira dubu biyar a riƙa biyan su a wata, za su yi farin ciki maimakon su riƙa zama haka nan ba aikin yi ba sana’a.
“Kai ni ina ganin manyanmu ba su son ƙasar nan. Babu kishin ƙasa, yanzu za ka ga ana buga taken Najeriya amma sai ka ga wani yana goge motarsa ko yana yin wani abu. Na taɓa gani a ƙasar waje, gunkin wani babban mutum aka yi amma wani Balarabe ya je ya buga kansa, da ƙyar ’yan sanda suka ƙwace shi. Amma kai kana ƙasarka ba za ka yi kishin ta ba?
“Yanzu mu duba muna da Hukumar Wayar Da Kan Al’umma (NOA) amma babu wani aiki da suke yi na faɗakar da mutane don kishin ƙasa. Ko ma’aikatu a garin nan, wasu wuraren za ka ga tutar Najeriya ta yage ko ta yi dauɗa, ba a kula ba. Wani ba zai iya cire kuɗi daga aljihunsa ya bayar don a gyara ba. Ni da kaina, sau da yawa nakan ɗinka tuta in sanya a asibiti inda nake aiki. Wani lokacin nakan ɗinka su da yawa, idan na ga inda ake buƙata sai in bayar. Yanzu a ce ko lokacin murnar ’Yancin Kai, mutane za su je sitadiyom amma gwamnati ba za ta iya ɗinka ƙananan tutar nan kamar guda miliyan ta raba wa mutane ba. Yanzu za ka ga matasa sun fi kishin kulob ɗin ƙwallon ƙafa na Turawa fiye da tutar Najeriya. Za ka ga sun sanya kuɗi sun sayi rigar kulob ɗin Turai da kayan sha’awa na kalar kulob ɗin amma ba za su iya yi kan Najeriya ba. Yanzu a ce har ƙwallon waje ta fi Najeriya?”
Na tambaye shi cewa, mene ne babban burinka a rayuwa? Ya amsa da cewa, “Gaskiya ba ni da buri wanda ya wuce in zauna lafiya da jama’a. Idan na samu ɗan abincin da zan ci da suturar da zan saka shi ke nan. Amma in ce wai in ɗauko wata babbar mota ko ina son zama wani babba a wuri kaza, wannan duk Allah ne ke tabbatarwa. Ai ga shi mun haɗu da kai a yau, kai ba ka sani ba, ni ma ban sani ba, amma Allah Ya tabbatar da haɗuwar mu. Yanzu shekara nawa ina irin wannan rayuwa ta nuna kishin ƙasa amma babu wanda ya taɓa yin magana duniya ta sani, sai da Janar Kukasheƙa ya zo. Allah Ya nufa ya shigo gidan nan, ga shi ya wallafa a jarida kowa ya san ni a duniya. Cikar buri daga Allah ne, idan ka samu, alhamdu lillahi, idan bai zo ba, haka Allah Ya tsara. Allah Ya riga ya rubuta duk abin da za ka zama, ba ka da wani iko.”
Daga ƙarshen tattaunawarmu, na tambaye shi cewa, ko akwai wani abu da za ka faɗa wa jama’a? Ya bayyana cewa: “A yi kishin ƙasa kuma a kwatanta gaskiya domin a zauna lafiya. Rashin gaskiya shi ke kawo mana tashin hankali a ƙasar nan. Idan da a ce manya shugabanni za su kwatanta gaskiya ko yaya ne, wallahi jama’a tafi za a yi masu. Amma ka ce sai ka tara dukiya…Yanzu a lokacin Bikin ’Yancin Kasa, idan ka zo gidan nan mutane ke cika shi kuma ba kuɗi zan ba su ba. Haka za su riƙe tutarsu, su zo nan. Ka ga ai misali suka gani a aikace. Ni abin da ke ɓata mani rai da shugabannin zamanin nan shi ne, babu kishin al’umma a tare da su.
“Yanzu a bana Taiwo Akintunmi, wanda ya zana mana tutar ƙasar nan ya mutu. Babu wanda ya ji labarin a ƙasar nan. Ni ban ma sani ba sai da Janar Kukasheƙa ya kira ni, ya sanar da ni, sannan na sani amma ƙasa babu komai na sanarwa. Ya kamata a ce an sa ranar ta zama hutu ko a yi wani abu da zai zama alamar cewa ya mutu. Idan da a ƙasar waje ne irin wannan mutum ya rasu, da a ƙasar sai an yi hutun mako ɗaya ko makamancin haka. A matsayinka na ɗan Najeriya duk inda ka je, kana gadara da taƙama da tutar nan ta kore-fari-kore amma a ce wanda ya tsara ta ya mutu amma kamar ɓera ne ya mutu ba mutum mai muhimmanc ba? Ba a sassauto da tuta ƙasa ba, ba a saka ranar ta zama ta hutu ba? Lallai wannan al’amarin ya ɓata mani rai sosai.”
✓Mohammed Umar Maidala:
Tun da farko, na fara sanin Malam Mohammed Umar Maidala ne ta hanyar Dokta Bukar Usman kuma mun daɗe muna zumunci da shi ta hanyar intanet da waya amma ba mu taɓa ganin juna ba sai sanadiyyar wannan ziyara da na kai garin Biu. Hasalima, tun kafin ranar da zan je garin, na samar da shi cewa rana kaza zan taho. Kuma tun da na taso daga mazaunina muke magana ta waya, har na isa garin Biu. Koda na iso, shi ne ya tarbe ni, shi ne kuma mai masaukina da yi mani jagora a dukkan wuraren da na ziyarta.
Wane Umar Maidala? Babu shakka mutum ne mai karimci da mutunta mutane. Na fahimta da haka ne daga yadda yake haba-haba da ni cikin kyautatawa. Haka kuma duk inda muka je, nakan lura da yadda mutane ke girmama shi. Sunan mahaifinsa Alhaji Muhammad Ɗankano, mahaifiyarsa kuwa, ita ce Hajiya Zara Kachalla. An haife shi a Unguwar Bakin Gada, Fadar Sarkin Biu. Ya yi karatun Alƙur’ani a Tsangayar Malam Tijjani, Filin Jirgi Biu. Ya yi karatun firamare a Biu Central Primary School, daga 1982 zuwa 1988. Ya yi karatun gaba da firamare a Government Day Secondary School Biu daga 1989 zuwa 1994.

Malam Umar ya fara aiki a Sakatariyar Ƙaramar Hukumar Biu a ranar 6 ga Nuwamba, 1996. Ya ci gaba da karatu a Ramat Polytechnic Maiduguri, daga shekarar 1999 zuwa 2001, inda ya samu shaidar difiloma a fannin Ayyukan Gayya da Gudanarwa. Daga nan ya ci gaba da aiki a Ofishin Magajin Garin Biu har zuwa shekarar 2003, inda ya koma aikin koyarwa a ƙarƙashin Hukumar Ilimi ta Ƙaramar Hukumar Biu. Yana kan aikin koyarwa ne ya samu gurbi a Jami’ar Maiduguri, inda ya samu digiri a kwas ɗin Hikimar Gudanar da Al’amuran Al’umma. Yana auren Malama Ruƙayya Isah Aliyu kuma Allah Ya albarkace su da ’ya’ya biyu – Damcida da Umar Farouk.
✓Kammalawa:

Babu shakka na ji daɗin ziyarar da na kai zuwa garin Biu. Na isa garin a ranar Laraba, 25 ga Oktoba, 2023 da farkon dare. A yayin da kuma na kwashe kwanaki bakwai cur a Birnin Biu. Na baro garin a safiyar Laraba, 01 ga watan Nuwamba, 2023 kuma na isa gidana da dare. Na samu ilimi mai yawa a wannan tafiya, na ga abubuwan al’ajabi kuma na haɗu da mutane masu mutumci da karimci. Lallai Biu birni ne a kan tsauni – tsaunin alheri mai mutanen alheri da albarka!













