• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, March 8, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Minista Ga VON: Ku Yaɗa Kyawawan Labaran Nijeriya Ga Duniya

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
December 20, 2023
in Labarai
0
Minista Ga VON: Ku Yaɗa Kyawawan Labaran Nijeriya Ga Duniya

Minista Idris (a dama) tare da Alhaji Ndache

10
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Minista Ga VON: Ku Yaɗa Kyawawan Labaran Nijeriya Ga Duniya

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya umarci gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON) da ya maida hankali wajen yaɗa kyawawan labarai da shirye-shirye game da irin gudunmawar da Nijeriya ta ke bayarwa ga cigaban duniya.

Related posts

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

February 13, 2026
Bura women Celebrate Bukar Usman at 83

Ƙungiyar Matan Al’ummar Bura Sun Karrama Dr. Bukar Usman Bisa Cika Shekaru 83

January 9, 2026

Mataimakin Daraktan yaɗa labarai a ma’aikatar, Malam Suleiman Haruna, ya ruwaito a cikin sanarwa ga manema labarai da ya bayar cewa ministan ya yi wannan umurnin ne a lokacin da hukumar gudanarwa ta gidan rediyon ta kai masa ziyarar aiki a ofishin sa a Abuja a ranar Talata,
19 ga Disamba, 2023.

Ministan ya yi kira ga VON da ta isar da saƙon damarmakin da ke akwai, da haɗin gwiwa, da ingantuwar ƙasar Nijeriya ta yadda Nijeriya za ta ci moriyar Zuba Jari Kai-tsaye daga Waje.

Ya ce idan an samar da kyakkyawan yanayin yin kasuwanci, to gwamnati za ta samun ƙarin ayyukan yi da kuma kuɗin shiga.

Ya ce: “Ku na da rawar da za ku taka wajen aikin sauya fasalin zamantakewa da gwamnatin Tinubu ta sanya a gaba a yanzu.

“Tilas ne ku riƙa isar da saƙon mu na ƙaruwar arziki da damarmakin da ke akwai, tare da jama’a ƙwararru a fannoni daban-daban don a jawo ra’ayin masu zuba jari da kuma masu yawon shaƙatawa zuwa Nijeriya.

“Nijeriya ta na kan hanyar ta ta samun martaba; tilas mu ƙarfafa gwiwar masu harkokin kasuwanci su shigo ciki a dama da su domin su amfana.”

Ministan ya ce ya na sane sosai da cewa sassa da dama na Nijeriya su na buƙatar a tallafa masu domin su shigo cikin wannan tsarin na sauya fasalin zamantakewa. Ya ce duk da hakan, gwamnatin ta na yin bakin ƙoƙarin ta domin magance matsaloli.

Akwai buƙatar gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON) ya isar da wannan saƙon ga duniya, inji shi.

Tun da farko a nasa jawabin, sai da Darakta-Janar na Muryar Nijeriya, Alhaji Jibrin Baba Ndace, ya bayyana cewa hukumar gudanarwa da ma’aikatan gidan rediyon sun kawo ziyarar ne domin su sanar da ministan irin tsarin aiki da su ka fito da shi kuma su shaida masa cewa su na bin dukkan tsare-tsaren gwamnatin Tinubu sosai da sosai.

Darakta-Janar ɗin ya ba ministan tabbacin cewa duk da yake su na watsa shirye-shirye cikin harsunan ƙasashen waje guda huɗu ne, yanzu su na da burin su faɗaɗa zuwa harsunan wasu manyan ƙasashen irin su Chaina da Indiya, waɗanda su na gudanar da harkokin kasuwanci a Nijeriya.

Previous Post

Kafafen Yaɗa Labarai Su Ne Manyan Dirkokin Da Ke Ɗauke Da Nagartacciyar Dimokiraɗiyyarmu – Minista

Next Post

SABON ZUMUNCI: KWANKWASO DA GANDUJE SUN YI SULHU

Related Posts

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina
Labarai

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

February 13, 2026
Bura women Celebrate Bukar Usman at 83
Labarai

Ƙungiyar Matan Al’ummar Bura Sun Karrama Dr. Bukar Usman Bisa Cika Shekaru 83

January 9, 2026
Sojoji Sun Ƙwato Muggan Makamai A Jihar Taraba
Labarai

Sojoji Sun Ƙwato Muggan Makamai A Jihar Taraba

January 5, 2026
Next Post
SABON ZUMUNCI: KWANKWASO DA GANDUJE SUN YI SULHU

SABON ZUMUNCI: KWANKWASO DA GANDUJE SUN YI SULHU

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (4)

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (4)

May 18, 2025
BULALAR ZUMUNCI

BULALAR ZUMUNCI

August 6, 2023
RAMADAN KARIM: 15-1447

RAMADAN KARIM: 15-1447

March 4, 2026
Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

February 13, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • RAMADAN KARIM: 19-1447
  • FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
  • RAMADAN KARIM: 18-1447

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

RAMADAN KARIM: 19-1447

RAMADAN KARIM: 19-1447

March 8, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.