• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Za Mu Sake Dasa Wa Al’ummar Nijeriya Ɗabi’ar Yarda Da Kalaman Shugabanni – Minista Idris

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
October 18, 2023
in Labarai
0
Za Mu Inganta Rayuwa Da Ayyukan ‘Yan Jarida – Minista Idris

Alhaji Mohammed Idris, Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai

31
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Za Mu Sake Dasa Wa Al’ummar Nijeriya Ɗabi’ar Yarda Da Kalaman Shugabanni – Minista Idris

Daga Wakilinmu

Related posts

IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne

IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne

August 17, 2026
Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

August 13, 2026

~~~~~~~
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya nuna damuwar sa ganin yadda akasarin ‘yan Nijeriya sun daina yin amanna, yarda ko gaskata kalaman da ke fitowa daga bakin shugabanninsu.

Ministan ya bayyana haka a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), a Abuja.

“Abin da muke so shi ne a bar ‘yan Nijeriya su san gaskiya daga waɗanda suka wajaba su bayyana masu gaskiyar. Ina ganin muhimmin abu ne sosai a ga cewa an ɗora tsarin isar da saƙo a kan turbar faɗa ko bayyana gaskiya, ta yadda wanda ake faɗa wa gaskiyar zai yi amanna da abin da mai faɗa masa gaskiyar yake faɗa.

“Wannan haka ne, saboda mun ga irin yadda amanna da gwamnati da kuma amincewa suka gushe ko suka zaizaye a zukatan jama’a, a ƙasar nan.

“Mun kai matakin da akasarin ‘yan Nijeriya ba su yin amanna da abin da shugabannin suke faɗa masu. Kuma fa su mutanen su suka zaɓi shugabannin da hannunsu.

“Saboda haka akwai matuƙar buƙatar mu fara ganin mun kankaro wannan gwamnati daraja, ta hanyar samun amincewa da amanna daga wurin ‘yan Nijeriya.

“Za mu yi wannan aikin haiƙan, bakin ƙarfi da iyawar gwamnati, domin ganin jama’a sun dawo suna gaskata kalamai da bayanan gwamnati,” cewar Idris.

Ya ƙara da cewa faɗin gaskiya shi ne matakin farko na nagartar mutum, domin idan jama’a suka san gwamnati na faɗar gaskiya, to su ma fa masu ba da rahotannin bayanai tsakanin tilas su riƙa faɗar gaskiya.

Idris ya ce gwamnati na ƙoƙarin ƙara zaburar da jama’a cewa kowa ya kasance yana faɗar gaskiya.

“Za mu fito mu yi kamfe na daƙile masu yaɗa labaran bogi da ƙarairayi, waɗanda hatsarinsu zai iya kaiwa ga ruguza al’umma ko kawo rabuwar kai.

“Kuma za mu ci gaba da kwaɗaitar da kafafen yaɗa labarai su tsaya kan turbar bayyana gaskiya, wadda dama ita ce kyakkyawar ɗabi’ar da aka san kafafen yaɗa labarai ke kanta, kuma suke kan koyarwarta,” cewar Minista Idris.

Dangane da labaran bogi, Idris ya ce wannan matsala ba ta Nijeriya kaɗai ba ce, abu ne wanda ya game duniya. Ya ce idan aka haɗa hannu za a iya kawar da yaɗuwar su, ba tare da an take haƙƙin kowa ba.
~~~~~~~

Previous Post

Za Mu Inganta Rayuwa Da Ayyukan ‘Yan Jarida – Minista Idris

Next Post

Muhimman Ayyukan Da Shugaba Tinubu Ya Ɗora Mani – Ministan Yaɗa Labarai

Related Posts

IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne
Labarai

IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne

August 17, 2026
Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina
Labarai

Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

August 13, 2026
An Samu Sauƙin Matsalar Tsaro: Yanzu Dukkan Kasuwanninmu Suna Ci
Labarai

An Samu Sauƙin Matsalar Tsaro: Yanzu Dukkan Kasuwanninmu Suna Ci

August 12, 2026
Next Post
Muhimman Ayyukan Da Shugaba Tinubu Ya Ɗora Mani – Ministan Yaɗa Labarai

Muhimman Ayyukan Da Shugaba Tinubu Ya Ɗora Mani - Ministan Yaɗa Labarai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

HANJIN JIMINA

HANJIN JIMINA

May 27, 2025
Taya Murna Ga Manaja Isma’il A. Sanda

Taya Murna Ga Manaja Isma’il A. Sanda

October 16, 2025
Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami

Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami

July 31, 2026
Ɓarawo Ya Sakar Masa Mata

Ɓarawo Ya Sakar Masa Mata

June 7, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Katsina A Makon Jiya (17-23-08-2026)
  • Professor Bello Sa’idu: The Demise of a Literary Icon
  • Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Katsina A Makon Jiya (17-23-08-2026)

Katsina A Makon Jiya (17-23-08-2026)

August 24, 2026
Professor Bello Sa’idu: The Demise of a Literary Icon

Professor Bello Sa’idu: The Demise of a Literary Icon

August 23, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.