• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, April 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

BATUN SULHU DA ‘YAN TA’ADDA A JIHAR KATSINA: Abin Da Ya Kamata A Fahimta

Abdulhadi Ahmed Bawa Faskari by Abdulhadi Ahmed Bawa Faskari
September 19, 2023
in Gizago
0
BATUN SULHU DA ‘YAN TA’ADDA A JIHAR KATSINA: Abin Da Ya Kamata A Fahimta

Tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari da muƙarrbansa, yayin ƙoƙarin sulhu da 'yan ta'adda, a shekarun baya

171
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

BATUN SULHU DA ‘YAN TA’ADDA A JIHAR KATSINA: Abin Da Ya Kamata A Fahimta

Daga Abdulhadi Ahmed Bawa Faskari

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari da wasu muƙarrabansa, yayin sulhu da ‘yan ta’adda a shekarun baya

~~~~~~~
A da, nikan zauna har bayan Isha’i kana in bar Kaduna zuwa Faskari. Wani lokacin ma daga Faskari sai in wuto Katsina kuma duk hankali kwance. Zullumi ɗaya nike yi, na kada mota ta ba ni matsala ko wata dabba ta gitta mani.

Yanzu kuwa daga Katsina zuwa Faskari sai na yi shiri da tsarin yadda zan yi tafiyar. Ba dai zan buga wa kowa waya in ce gani nan tafe ba, ballantana kuma idan na isa.. Ko ina da kuydi, na fi son in hau motar haya, domin ta fi sauƙin zullumi.

Mai karatu, ina son tabbatar maka da cewa duk wani mataki ko shiri da zai dawo mana da wancan zaman lafiya da kwanciyar hankali, Wallahi muna son shi. Za kuma mu goyi bayansa, idan har muka fahimci da gaske ake, ba domin biyan wata buƙata ba ta daban.

Ban so a ce sai na ɗauko dogon tarihi ba amma haƙiƙa hareharen da aka kai wa al’ummarmu a watan Maris na shekarar 2014 (wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka sama da dyari), su suka buɗo wannan shafi na ta’addanci da ake ta fama da shi a yanzu. Kuma shi ya tabbatar da cewa maganar ta wuce rikicin Fulani da Makiyaya da muka saba gani kusan duk da kaka.

Sabon salon da wannan lamari ya ɗauka ya sa gwamnatin da ta gabata, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta yi ta bin hanyoyi daban-daban domin shawo kanta. Wannan ya haɗa har da sulhu da sasanci tsakanin al’ummomin.

A shekarar 2016 aka gayyato shuwagabannin Fulanin nan har gidan gwamnati aka tattauna kuma suka yi alƙawarin ba za su sake wannan ta’asa ba. Da wannan har aka je Ƙanƙara aka yi taron miƙa makamai, wanda marigayi Buharin Daji ya jagorance su.

Ba a jima ba suka karya alƙawari, abubuwa suka jagule fiye ma da da. A 2019, Gwamna Masari ya ƙara jagorantar wani yunƙurin, wanda aka bi shuwagabannin Fulanin nan cikin ƙauyuka ko wuraren da suka zaɓa, aka ƙara tattaunawa da su a karo na biyu.

Kalamai na ban tausayi da nadama, ba wanda ba su yi ba. Ƙananan Hukumomi takwas muka je domin ganin an samu nasara.

A wannan karon ma suka ci amanar wannan sulhu da sasanci, wanda hakan ta sa tsohon Gwamna Masari ya yanke shawarar ba zai sake zama da su ba da sunan sulhu. Idan suna buƙatar hakan to su miƙa makamansu ga hukuma kuma su nemi yafiya da shiri daga al’ummar da suka gallaza ma wa.

A hakan aka tafi har ya zuwa lokacin da aka fara yaƙin neman zaɓen 2023, a inda shi ma Gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya tabbatar da aniyar ta yaƙar su ko da kaf a kan haka kuɗin jihar za su ƙare.

Tun a lokacin na yarda da gaske, domin shi ma ya san raɗaɗin wannan fitina, domin ta rutsa da ‘yan uwansa.

Daga hawan shi kuma zuwa yanzu, ya ɗauki matakan da suka tabbatar da cewa da gaske yake. Dalili kuwa, an ɗauki ma’aikata a hukumance, waɗanda za su riƙa sa ido kan tsaro a cikin al’umma tare da kafa hukumar da za ta riƙa kula da su. An sayo motoci masu sulke (APC) guda goma da Hilux sama da guda 60, sai kuma babura sama da 700, duk domin samar da tsaron.

Kwatsam! Tun daga jiya kuma sai nike ta ganin fayafayan bidiyo da hotuna, da ke nuna cewa wai an yi zaman sulhu da Fulani a ƙauyen Fankama, na ƙaramar hukumata ta Faskari.

Na yi ta neman fayafayan a kan intanet, domin in fahimci yadda abin yake, domin duk wanda na tuntuɓa su ma iyakar abin da aka yaɗan nan shi suka sani.

Saboda haka sai na yi ta sauraren fayafayan nan a tsanaki, kuma har zuwa yanzu ban sami inda wani ya ce shi wakili ne na Gwamnatin Jihar Katsina ko Ƙaramar Hukuma ko Masarauta ba.

Wannan tare da neman ƙarin bayani da na yi, ya sa na tabbatar da cewa Gwamna Raɗɗa bai sani ba kuma babu yawunsa ko na Gwamnatin Jiha, a cikin wannan sabon shiri na sulhu.

Shi jagoran sabgar, ya ce daga Abuja ƙololuwa aka turo su kuma wannan sulhu da suke shiri ba a nan kaɗai ya tsaya ba, duk Najeriya ne. Kuma duk wanda bai yarda ba sai dai ya bar ƙasar. Kuma wannan zaman shi ne na uku, domin sun riga sun yi biyu a Zamfara.

Kamar yadda na faɗi a sama, muna maraba da duk abin da zai kawo mana dawwamammen zaman lafiya amma abin tambaya kawai shi ne; mutanen da Gwamna ya kira su Gidan Gwamnati, ya roƙe su suka ƙiya. Suka zaɓi wuraren da suke so a ƙara zama, ya kuma je aka zauna. Ya roƙe su tare da lallashi, ya kuma shaida masu ba don sun fi ƙarfin gwamnati ba, sai don a taƙaita zubar jini amma suka ƙi. To ta ina za su mutunta maganar da ba a ma fito fili aka ce ga wanda ya aiko a yi sulhun da su ba?

A kaf jawaban da na ji, babu inda aka ambaci wanda ko waɗanda suka yo aiken a yi sulhun. Sai dai kawai aka ce “daga can ƙololuwa, Abuja.”

Za mu yi masu kyakkyawan zato tare da addu’ar Allah Ya watsa duk wani asirin da aka iya saƙawa ko ɓoyewa a cikin wannan shiri.

Muna ci gaba da roƙon Allah Ya sa taimakonSa a cikin shirin da Gwamnatin Jihar Katsina, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa take yi, na kawo ƙarshen ta’addanci a wannan jiha tamu mai albarka.

~~~~~~~~
Malam Abdulhadi, ɗan siyasa, marubuci kuma tsohon Mataimaki Na Musamman ta Fuskar Soshalmidiya ne ga tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari. Ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Faskari, ya aiko da wannan tsokaci daga Katsina.
~~~~~~~

Previous Post

Babban Birnin Tarayya Abuja: Jiya Da Yau Da Gobe

Next Post

Lost Heritage Series #1 – Mazari [Spindle]

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
Lost Heritage Series #1 – Mazari [Spindle]

Lost Heritage Series #1 – Mazari [Spindle]

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Unguwar Tumbu-Madallah

Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Unguwar Tumbu-Madallah

July 14, 2023
Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

October 22, 2025
Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da Peter Obi ya ce ƙaramin kasafin ƙarshen 2023 ba shi da amfani

Shirin Rage Tsadar Rayuwa: Za A Fara Biyan Sabon Tsarin Albashi Daga Afrilu 2024 – Minista

December 3, 2023
RAMADAN KARIM: 10-1447

RAMADAN KARIM: 10-1447

February 27, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.