• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, September 20, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tinubu Za Ta Fifita Amfani Da Na’urorin Zamani A Gidajen Rediyo Sa Talabijin – Minista

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
October 26, 2023
in Labarai
0
Gwamnatin Tinubu Za Ta Fifita Amfani Da Na’urorin Zamani A Gidajen Rediyo Sa Talabijin – Minista

Ministan Watsa Labarai, a yayin jawabinsa

14
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Gwamnatin Tinubu Za Ta Fifita Amfani Da Na’urorin Zamani A Gidajen Rediyo Sa Talabijin – Minista

~~~~~~~
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa amfani da kayan aiki na zamani a gidajen rediyo da talbijin na da muhimmanci ga Gwamnatin Bola Tinubu.

Related posts

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026

Haka kuma ya jaddada alwashin gwamnati na bai wa harkokin bunƙasa kayan aikin rediyo, talbijin da shirya finafinai goyon baya saboda muhimmancin su ga bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce suna a sahun gaba wajen samun nasarar inganta tattalin arziki a ƙarƙashin ajandar Farfaɗo da Martabar Nijeriya ta ‘Hope Agenda’ da Gwamnatin Tinubu ta himmatu a kai.

Da ya ke jawabi wurin taron AFRICAST na 13 a ranar Talata, otal ɗin Marriot da ke Ikeja, Legas, Ministan ya nuna farin cikinsa, ganin yadda taron ya kasance ƙasaitacce, duba da yadda yake tafiya bisa kyakkyawan shugabanci, ake baje kolin ilmi da kuma samun damarmakin bunƙasa kasuwancin fasaha da na’urorin zamani.

Ya ce Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NBC) ta ƙirƙiro AFRICAST ne ganin yadda ake samun yawaitar kafa gidajen rediyo, talbijin da bunƙasar harkokin finafinai da sauran kafafen isar da saƙo.

Idris ya yaba wa masu shirya taron, wanda aka shirya tare da haɗin gwiwar NIFS, ya ce taron ya samar da wani dandalin da ƙwararru a harkokin finafinai da talbijin za su samu dama da lasisin bayyana hajar su.

Ya bayyana muhimmancin rawar da masu ƙirƙiro shirye-shirye, furodusoshi da masu yaɗa shirye-shirye ke takawa wajen nishaɗantarwa a duniya.

Sai ya nuna muhimmancin a riƙa samar da shirye-shirye masu nagarta wajen nishaɗantarwa da ilmantarwa.

Ministan ya jaddada ƙoƙarin da gwamnati ke yi domin komawa amfani da tsarin DSO wajen yaɗa labarai, tare da himma wajen rungumar duk wata hanyar yaɗa labarai ta zamani da ake amfani da ita a duniya.

Ministan, wanda ya riƙa bi yana duba kayayyakin na’urorin yaɗa labarai da watsa shirye-shirye na zamani waɗanda aka baje kolin su a wurin, ya yaba da irin ci gaban da aka samu ta hanyar ƙirƙiro sababbin na’urorin sauƙaƙa ayyukan yaɗa labarai da shirye-shirye.

Ya ce Shugaba Tinubu zai kasance jagora wajen rungumar shirin amfani da na’urorin zamani a kafafen yaɗa labarai a gidajen rediyo da talbijin na Gwamnatin Tarayya.
~~~~~~~

Previous Post

Organized Crime: AANI Calls for Enhanced Collaboration to Combat the Menace in Africa

Next Post

PHOTO GALLERY: Hajia Rabi Attends UNICEF Training

Related Posts

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin
Labarai

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda
Labarai

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026
Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)
Labarai

Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)

August 31, 2026
Next Post

PHOTO GALLERY: Hajia Rabi Attends UNICEF Training

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Jan Hankali Ga Matasan Soshalmidiya

Jan Hankali Ga Matasan Soshalmidiya

July 11, 2023
RAMADAN KARIM: 03-1447

RAMADAN KARIM: 03-1447

February 20, 2026
Ni Bazawara Ce: To Kuma Sai Me?

Ni Bazawara Ce: To Kuma Sai Me?

September 14, 2023
Kwamishina Saulawa Jajirtacce Ne – Dr. Bala Nuhu

Kwamishina Saulawa Jajirtacce Ne – Dr. Bala Nuhu

August 10, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.