MAGANIN HASSADA DA MAHASSADA
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

•••••••
Tun da daɗewa ɗan Adam ya samu ilimin cewa haassada tana lalata zuciya kuma tana da manyan illoli ga mai yin ta da rayuwarsa gaba ɗaya.
Idan muka duba Musulunci, hassada ita ce mummunar ɗabi’a, wacce mutum yake fatan ganin gushewar wata ni’imar da Allah ya bai wa wani ko kuma ya ji zafin ganin wani ya samu wani alheri ko ci gaba. Ba nan kaɗai abin ya tsaya ba, asalin hassada ita ce son ganin an ƙwace ko an rasa wannan ni’imar daga hannun wanda ya samu.
Ita hassada tamkar wuta ce gagaruma mai cin zuciya, wacce take lalata addinin mutum da kuma rayuwarsa ta duniya da lahira, idan bai tuba ba. Hassada tana da tushe a son kai, girman kai da kuma rashin gamsuwa da rabo ko ƙaddarar da Allah ya yi wa mutum.
Hassada tana da illoli masu yawa, waɗanda suka shafi dukkan matakan rayuwar ɗan Adam. Abu na farko kuma mafi haɗari, shi ne yadda take shafar addinin mutum. Tana ƙona ayyukan alheri kamar yadda wuta take cin itace. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya yi gargaɗi mai ƙarfi game da ita. A wani hadisi na Abu Dawuda, an ruwaito Manzo (saw) yana cewa: “Ku guji hassada, domin hassada tana cinye ayyukan alheri kamar yadda wuta take cinye itace.”
Wannan yana nuna mana cewa dukkan wata lada da falalar da mutum ya tara ta hanyar salloli, azumi da sadaka suna iya gushewa saboda wutar hassada da take ci a zuciyarsa. Hakan yana nuna cewa zai tafka babbar hasara a lahira.
A fannin zamantakewa kuwa, hassada tana haifar da husuma a cikin al’umma. Mai hassada ba ya iya zama cikin aminci da jin daɗi. Yana ci gaba da ƙulla makirci da miyagun zato a kan wanda yake yi wa hassada. Hakan yana kawo gaba da rigima a tsakanin iyali, abokai da al’umma baki ɗaya. Hassada tana sace farin ciki da kwanciyar hankali daga zuciyar mai yin ta, inda take maye gurbinsu da baƙin ciki da damuwa marar iyaka. Shi ya sa aka ce mai hassada ba ya samun hutu a rayuwarsa, domin a kullum zai riƙa ganin nasara da cigaba a rayuwar wanda yake wa hassada.
Babbar illar hassada ita ce, tana raba mutum da imani da Allah, domin kuwa mai hassada yana nuna ƙiyayya da ƙaddarar Allah da kuma hikimarsa. Idan mutum ya ƙi yarda da rabo ko ni’imar da Allah ya bai wa wani, a zahiri yana nuna cewa bai gamsu da rabe-raben Ubangiji ba. Wannan kuma babban giɓi ne a cikin Tauhidi.
Allah ya yi mana gargaɗi mu guji nuna ƙyashi ga abin da ya ba wasu bayinsa na arziƙi. A Alkur’aninsa mai girma, Suratun Nisa’i, aya ta 32, Allah yana cewa: “Kuma kada ku yi gurin abin da Allah ya fifita sashenku da shi a kan sashe. Maza suna da rabo daga abin da suka tsirfanta, kuma mata suna da rabo daga abin da suka tsirfanta. Kuma ku roƙi Allah daga falalarsa. Lalle ne Allah ya kasance masani ga kowane abu.”
A addinin Kirista, hassada abin ƙyama ce. A Baibul, Surar Misalai 14 aya ta 30 tana cewa: “Zuciya mai natsuwa rayuwa ce ga jiki amma hassada ruɓa ce ga ƙasusuwa.” Wannan ayar tana nufin cewa natsuwa da gamsuwa suna kawo lafiya ga dukkan jiki, alhalin hassada tana da lahani sosai har tana iya lalata mutum gaba ɗaya, kamar yadda ruɓa take lalata ƙashi.
To, shin ina mafita daga wannan cuta ta zuciya? Mene ne maganin hassada da mahassada? Babbar mafita ita ce, mutum ya zama mai gaskatawa da Ubangiji Allah da kuma gamsuwa da rabon da ya ba shi. Mutum ya fahimci cewa Allah ne mai bayarwa kuma yana ba wanda ya so abin da ya so, bisa ilimi da hikimarsa. Idan mutum ya ga wani alheri a hannun wani, to sai ya yi masa addu’ar albarka, sannan ya mayar da hankali kan neman falalar Allah. Ya jajirce ya yi aiki ko sana’a, ba zaman banza da sanya ido ga rayuwar wasu ba.
Ta yaya za mu guje wa dukkan illolin hassada? Musulunci ya kawo mana hanya mafi dacewa ta tsarkake zuciya. Wannan hanya ita ce ta neman tsari da kuma tsarkake zuciya daga ƙazantar zargi da ƙiyayya. Surorin Alƙur’ani biyu (Falaƙi da Nasi), Allah ya saukar da su ne domin su zama garkuwa ga al’umma daga dukkan sharri, ciki har da sharrin mai hassada.
Ya kamata mu sani cewa, shi Allah (swt), faɗin falalarsa ba ta da iyaka. Kada ka yi wa wani ƙyashi, domin samunsa ba zai hana naka samun ba. Ya Allah ka kiyashe mu da hassada ga junanmu, ka sanya albarka a kan duk abin da ka raba ka ba mu. Allah ka kare mu daga sharrin dukkan mai hassada a gare mu baki ɗaya.
_______________













