• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, January 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

FAUZIYYA ƊANLADI SULEIMAN: Tattaunawa Da Uwar Marayu Da Raunana

Binta Tukur by Binta Tukur
September 3, 2023
in Adabi
0
FAUZIYYA ƊANLADI SULEIMAN: Tattaunawa Da Uwar Marayu Da Raunana

Fauziyya D. Suleiman

92
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

FAUZIYYA ƊANLADI SULEIMAN: Tattaunawa Da Uwar Marayu Da Raunana

Fauziyya tana amsar takardar naɗa ta muƙamin Mataimakiya Ta Musamman Ga Gwamnan Jihar Kano, Kan Harkokin Jin Ƙai

Daga Binta Tukur

Related posts

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

December 6, 2025

~~~~~~~
Ita marubuciya ce, mai jin ƙai ce kuma ‘yar kasuwa ce. Muna magana ne a kan fitacciyar marubuciyar Hausa da ta rikiɗe zuwa hadimar al’umma, mai gudanar da ayyukan jin ƙai da tallafa wa marasa shi. Wakiliyar Taskar Gizago ta Musamman, Binta Tukur ta tattauna da Hajiya Fauziyya D. Suleiman, wacce a kwanan nan Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa ta muƙamin Mataimakiya Ta Musamman Kan Harkokin Jin Ƙai.
~~~~~~~

TG: Kina ɗaya daga cikin manyan marubutan Hausa, ko za ki gaya mana tarihinki a taƙaice?

FAUZIYYA: Ni dai sunana Fauziyya D. Sulaiman amma dai cikakken sunan shi ne Fauziyya Ɗanladi Sulaiman. An haife ni a Unguwar Fagge, cikin birnin Kano a shekarar 1981. Aƙalla yau shekaruna 42 ke nan a duniya. Na yi karatun firamare har zuwa matakin Diploma. Na yi Diploma ce a ɓangaren lafiya, yanzu kuma ina karatun digiri a fannin Watsa Labarai (Mass Communication), wanda shi ne nake aiki a bangarensa a yanzu. Na halarci makarantu daban-daban har zuwa kan matakin da nake kai yanzu. Wannan shi ne kaɗan daga tarihina.

TG: Tun yaushe kika fara rubutu kuma mene ne ya ja ra’ayinki ga harkar rubuce-rubuce?

FAUZIYYA: E, to rubutu, ba zan iya cewa ga taƙamaimai lokacin da na fara ba, domin tun ina firamare na fara rubutun littafi. Yawan karance-karancen littattafai shi ya ja ra’ayina. Tun da na tashi ina yarinya, ban san ma lokacin da na fara karance-karance ba, kawai na tashi na gan ni ina da son karanta littattafai. Na karanta littattafai ba adadi, wanda shi ne ya ja hankalina na fara rubuce-rubuce. Amma a lokacin ban kai ga wallafawa ba. Ina ta rubutawa ina ajewa, har lokacin da na je sakandare, har zuwa lokacin da aka yi mani aure. Littafina ya fara fita kasuwa a shekarar 2002.

TG: Ya zuwa yanzu, littattafai nawa kika rubuta? Guda nawa aka buga a littafin takarda kuma nawa kika buga a intanet?

FAUZIYYA: Na rubuta littattafai guda 27 zuwa 28, duk da dai ban riƙe taƙamaimai yawan littattafaina ba saboda abin ya kwana biyu.
Batun intanet kuwa, to gaskia ban taɓa rubutu a yanar gizo ba. Saboda yanar gizo ta yara ce ‘yan zamani. Mu kuma yanzu abubuwa sun yi mana yawa, ba mu samu mun amshe ta ba, duk da dai mukan yi rubutun gajerun labarai. Tun kafin zuwan marubutan yanar gizo muke yi, wanda har littafi na wallafa na gajerun labarai. Amma dai cikakken rubutu na labari daga farko zuwa ƙarshe, ba taɓa yi a yanar gizo ba.

TG: Waɗanne irin matsaloli kike fuskanta a matsayinki na marubuciya, musamman ma a soshalmidiya?

FAUZIYYA: E, to gaskia kai tsaye ba wasu matsaloli da zan iya cewa na fuskanta a yanar gizo, a matsayina na marubuciya. Sai dai abu na yau da kullum, wanda aka saba gani, wanda wani lokacin dole a ƙalubalance ka; musamman kasancewarmu mata, dan ka zo ka yi magana a kan wani abu da ya shafi mata. Amma dai yanzu yawanci yau da gobe ta sa mabiyan namu ma sun gane, domin idan ka yi magana mutum ɗaya ya ya fahimce ka a karkace, to mutane goma za su fahimce ka a daidai. To wannan ke kaɗai zan ce ‘yar matsalar da muke samu, wacce ba wani abun damuwa ba ne, tun da mutanen da za su yaba da kai sun fi waɗanda za su kushe ka. Yanzu ta kai idan muka faɗi magana, mutane da yawa suna yarda ne saboda sun gani ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. Wani lokacin ka magance, wani lokacin kuma ka sa wasu su magance.

TG: Tun daga fara rubutu, waɗanne irin nasarori kika samu ko kuma akasin su?

FAUZIYYA: To ai tun da na fara rubutu, Astagfirullah, ni kullum cikin nasara nake. Ni ban taɓa samun rashin nasara ba. Wato nasarori misali, su ne nasarorin da mutum zai samu a cikin rayuwarsa. Tun da na fara rubutu har zuwa yanzu, tun farko-farko da muke sayar da litttafi har kawo yanzu da muka fara bugawa da kanmu, har zuwa yanzu da nake a zaune, duk sana’a ta rubutu ce. Wato ina nufin inda nake aiki a Arewa 24, sana’ar rubutu aka ɗauke ni, a kan rubutu ake dauke ni, wandan rubutu ne da ya shafi ɓangaren fim. Mu ne ke rubuta shirin fim mai dogon zango, watau Daɗin Kowa da Kwana Casa’in. To su ma dai rubutu ne saboda haka har yau a cikin nasara muke kuma duk wani ci gaba da muka samu a rayuwarmu, a sanadiyyar rubutu ne. Ko a yanar gizo, sanin da aka yi mana duk a kan rubutu ne, har zuwa taimakon da muke yi na al’umma; dukkansu ta dalilin rubutu ne ya jawo su, ta sanadiyar rubutu da aka san mu. Ta haka muke rubutawa, muna nema wa al’umma taimako. Saboda haka mu rubutu ya ba mu nasara kuma har zuwa yanzu muna kan nasarar kuma muna fatan in sha Allahu har mu mutu muna cin albarkacin rubucen-rubucen da muke yi.

TG: A harkar rubuce-rubuce, waɗanne marubuta ne gwanayenki, da kike koyi da rubutunsu?

FAUZIYYA: To kusan zan iya cewa gaskiya gwanayena da yawa a rubutu, domin ba za su iya faɗuwa a nan ba. Domin ni kamar yadda na faɗa, tun farko da na tashi duk wani littafin wata marubuciya kusan ina iya lissafa maki tsoffin marubuta nan maza da mata, babu kusan littafin wanda ban karanta ba; musamman lokacin da ake ganiyar rubutun ke nan na manyan marubutanmu da suke gabanmu. To kusan kowane idan ka lissafo mani, ka ce wane, to zan iya lissafa maka littattafansa daga na ɗaya har zuwa inda ya tsaya, haka ma mata. To saboda haka kusan gwanayena suna da yawa, waɗanda idan na ce zan kama suna, sai in cika filin hirar da su. Don duk sai na lissafo su amma dai Allah Ya sani, ina son marubuta sosai da rubutu.

TG: Baya ga harkar rubutu, kin tsunduma cikin harkokin tallafa wa al’umma domin inganta zamantakewar aurensu. Ta yaya kika faro wannan kuma ko za ki yi mana cikakken bayani game da ƙalubalen wannan gagarumin aiki?

FAUZIYYA: To kamar yadda na yi bayani a ɗan taƙaice a baya, cewa ita wannan harkar tallafin da ake yi ta ƙungiya, duk rubutu ne ya jawo, domin rubuce-rubucen da muke yi a yanar gizo na jan hankalin mutane. A haka muka gano wani bawan Allah, wanda ɗan unguwarmu ne Fagge, wani matashi mahaddacin Alƙur’ani, wanda shekarunsa ba su kai ashirin ba. Allah Ya jarabce shi da ciwon ƙoda kuma sai dai kuma an rasa kuɗin da za a yi masa wankin ƙodar. Ana ta sakawa a yanar gizo ya fi mako, kullum ina gani ana ta nema masa taimako. To a lokacin kuma feji na da nake rubuce-rubuce a kai ya yi ƙarfin da ina da mabiya da yawa, wanda mutane da yawa suna bibiya ta. Saboda haka sai na yi amfan i da wannan damar na yi rubutu na wallafa a kan cewa, ace a jiha kamar Kano da muke da manyan masu kuɗi, da kaza da kaza, a ce ga wani mai lalura amma an kasa taimaka masa. To daga nan sai mutane suka riƙa tambayar a ina yake, waye shi, a wane asibiti yake? Na zo na ce a Asibitin Nassarawa. Nan fa mutane aka yi ta zuwa aka yi ta zuwa ana ba shi taimako.
Wannan ya je ya ba shi, wannan ya je ya ba shi, wasu kuma su ce in tura lambar banki, su saka taimako, sai in tura lambar bankin na ‘yan uwansa, wansa da yayarsa. Tun lokacin ake saka taimako har Allah Ya sa maganar ta je kunnen Mai Martaba Sarkin Kano na wancan lokacin, Malam Muhammadu Sanusi II, ya shigo ya ɗauki nauyin mara lafiyar, a kan zai fitar da shi ƙasar waje. To kafin a kai ga hakan sai Allah Ya ɗauki rayuwarsa.
To, daga nan sai mutane suka farga, suka gane cewa idan na yi rubutu a shafina ana samun taimako, sai mutane suka fara turo mani, suna cewa don Allah ki wallafa, ki samar mana taimako. To sai nake ta yi, daga baya sai muka fara samun ‘yan matsaloli waɗanda wasu da muka ba su kuɗin sai suka cinye.
Akwai wani magidancin da muka ba shi kuɗi ya cinye, wanda ba mu farga ba sai da matar ta kusa mutuwa aka ƙara kiran mu. Muka tambayi ina kuɗin da muka bayar, aka ce wai aure mijin ya yi da kuɗin. Sannan shi ma na biyu da muka ba shi ya kusa guduwa da kuɗin, da ƙyar muka samu kuɗin suka dawo.
To waɗannan abubuwa da suka faru, su suka ja hankalina na ga cewa mu daina saka lambar makusanta, tun da ɗaya mijinta ne ɗaya kuma babanta ne. Tun da na ga idan muka sa suna yi mana ba daidai ba me zai sa ba za mu saka lambar bankinmu ba, mu ga abin da aka tara? To a lokacin sai muka fara saka akawun ɗinmu muna tarawa muna ganin abin da ake samu, duk wanda ya sako za mu ce wane ya sako Naira kaza, har muka zo muka ga cewa abin ya yi yawan da ba za mu iya jero sunayen mutanen ba. Abin ya zo ya zama duk abin da muka samu za mu zo mu ce an sami kaza, ga abin da ya faru ga kuma abin da muka yi.
To mutane suka fara ba mu shawara cewa, tun da wannan abin ya amsu, kullum ana wallafawa kuma ana samun taimako,me ya sa ba za mu maida abin ya zama ƙungiya ba? Kiraye-kiraye daga ko’ina, da haka har muka karɓi shawara muka je muka yi rijista da Hukumar Yi Wa Kamfanoni Rijista ta Nigeria (CAC), muka yi kungiya mai suna “Creative Helping Needy Foundation.”

TG: Ko za ki ƙara bayani game da wannan ƙungiya ko mu gidauniya taki?

FAUZIYYA: Ita wannan ƙungiya, ita ce har zuwa wannan lokaci ake ci gaba da tallafa wa mutane. A wannan ƙungiya tamu, kafin a yi mata rijista da bayan an yi mata rijista, ba zan iya lissafa yawan adadin mutanen da aka taimaka ma wa ba. Ba zan iya lissafa adadin mutanen da aka cire a cikin ƙangi da tsanani ba. Idan na ce zan ce mutane dubu ko dubu biyu ko dubu biyar, duk ba zan iya faɗi ba. Kawai sai dai waɗanda suke ba da taimakon suna ganin ayyukan, al’umma ma suna ganin ayyukan. Wani abin ma ka manta sai an tuna maka. Wannan shi ne sanadiyyar tafiyar tamu. Alhamdu lillahi.
~~~~~~~

Previous Post

Yau Maulidin Bilkisu Babangida

Next Post

Wasu Mutane Sun Kitsa Tayar Da Hargitsi A Najeriya – DSS

Related Posts

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)
Adabi

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine
Adabi

Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

December 6, 2025
Yau Take Juma’a: Allah Ka Albarkace Mu
Adabi

Yau Take Juma’a: Allah Ka Albarkace Mu

December 5, 2025
Next Post
Wasu Mutane Sun Kitsa Tayar Da Hargitsi A Najeriya – DSS

Wasu Mutane Sun Kitsa Tayar Da Hargitsi A Najeriya - DSS

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

ALLAH JI ƘAN AMINU DOGO

ALLAH JI ƘAN AMINU DOGO

June 29, 2025
Dr. T.S Saulawa: Beckons to Serve

Dr. T.S Saulawa: Beckons to Serve

December 12, 2025
CANJIN ZAMANI: Rayuwar Mata A Ƙarni Na 21

CANJIN ZAMANI: Rayuwar Mata A Ƙarni Na 21

January 7, 2025
Yau Ne Maulidin Likitar Ma’aurata

Yau Ne Maulidin Likitar Ma’aurata

July 28, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation
  • Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco
  • Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026
Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

January 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.