• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, July 28, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Gwamnan Katsina Ya Raba Ma’aikatar Ilimi Zuwa Gida Uku

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 1, 2023
in Babban Labari
1
Gwamnan Katsina Ya Raba Ma’aikatar Ilimi Zuwa Gida Uku

Gov. Malam Dikko Umar Radda

92
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Gwamnan Katsina Ya Raba Ma’aikatar Ilimi Zuwa Gida Uku

A ƙoƙarinsa na bunƙasawa da farfaɗo da darajar ili cemi a Jihar Katsina, Gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya raba Ma’aikatar Ilmi ta jihar zuwa gida uku.

Related posts

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

July 15, 2026
Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

July 11, 2026

Wannan bayani yana ƙunshe ne a wata takardar manema labarai da ta fito daga ofishin Ibrahim Kaula Mohammed, Jami’in Watsa Labarai na Gwamnan.

Baya ga Ma’aikatar Ilimi, sauran ma’aikatun biyu da za a ƙirƙiro su ne, Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, Ƙere-Ƙere Da Koyar Da Sana’o’in Hannu da kuma Ma’aikatar Kula Da Ilimin Firamare Da Sakandare.

Gwamna Raɗɗa ya tabbatar da haka a yayin da yake amsar baƙuncin shugabannin Jami’ar Umaru Musa ‘Yar-Adua, bisa jagorancin Shugabanta Farfesa Shehu Salihu Mohammed da suka kai wa Gwamnan ziyarar girmamawa.

Gwamnan ya ce an ɗauki wannan mataki ne da kyakkyawar niyya, da nufin inganta ilimi mai zurfi, wanda ke da matuƙar muhimmanci. Don haka ya ce, an raba ma’aikatun ne domin kawo sauƙi a gudanar da harkokin ilimi a jihar cikin inganci.

Gwamna Dikko ya yaba wa Farfesa Salihu da kuma sauran shugabannin gudanarwa, ta yadda suke tafiyar da harkokin jami’ar. Haka kuma ya yaba da kyakkyawar dangantakar da take tsakanin jami’ar da Gwamnatin Jihar Katsina.

Gwamnan ya tunatar da da cewa an kafa jami’ar ce bisa ingantaccen ginshiƙi, don haka ya buƙaci shugabannin da su yi aiki tuƙuru, domin dawo da martabar jami’ar, ta hanyar ɗaukar ƙwararrun malamai da ma’aikata haziƙai.

“Na shiga damuwa da na samu labarin cewa akwai wasu makarantu a jihar nan, inda wasu malamai ke koyar da ɗalibansu ta amfani da harshen Hausa. Wannan gaskiya abin takaici da abin kunya ne. Daga yanzu ba za mu lamunci haka ba.

“A matsayin gwamnatinmu mai kulawa, a shirye muke mu tabbatar da cewa dukkan manyan makarantunmu suna yaye ingantattun ɗalibai da za su yi gogayya da na ko’ina a faɗin duniya,” in ji Gwamna Raɗɗa.

Gwamna kuma ya jaddada albishir da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da haɗa hannu da Jami’ar Umaru Musa’ Yar-Adua, domin samar da ingantaccen ilimi abin koyi ga sauran Jihohin ƙasar nan.

Previous Post

Gwamna Namadi Ya Ladabtar Da Shugabannin Babban Asibitin Gumel

Next Post

An Yi Gangamin Addu’o’in Godiya Ga Allah A Katsina

Related Posts

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista
Babban Labari

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

July 15, 2026
Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo
Babban Labari

Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

July 11, 2026
ACF Endowment Fund Sets Agenda for Transparency, Education and Empowerment in Northern Nigeria
Babban Labari

Asusun Tallafi na ACF Ya Tsara Sabuwar Hanyar Bunƙasa Ilimi da Ƙarfafa Al’ummar Arewa

June 25, 2026
Next Post
An Yi Gangamin Addu’o’in Godiya Ga Allah A Katsina

An Yi Gangamin Addu'o'in Godiya Ga Allah A Katsina

Comments 1

  1. Nasir Abdullahi says:
    3 years ago

    Ma Sha Allah

    Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

December 24, 2024
Ya Zama Wajibi A Ɗauki Mataki A Kan Minista Wike

Ya Zama Wajibi A Ɗauki Mataki A Kan Minista Wike

November 12, 2025
KWANKWASO BAI CIKIN WAƊANDA SUKA KAFA APC

KWANKWASO BAI CIKIN WAƊANDA SUKA KAFA APC

September 22, 2025
RAMADAN KARIM: 26-1447

RAMADAN KARIM: 26-1447

March 15, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • A Voice for Eternity
  • A New Dawn for NIgerian Defence: The Strategic Expansion of the Nigerian Army to 12 Divisions
  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

A Voice for Eternity

A Voice for Eternity

July 28, 2026
A New Dawn for NIgerian Defence: The Strategic Expansion of the Nigerian Army to 12 Divisions

A New Dawn for NIgerian Defence: The Strategic Expansion of the Nigerian Army to 12 Divisions

July 27, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.