• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, April 25, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Sarauta

Sarautar Kano: Akwai Yiwuwar Muhammadu Sanusi II Ya Dawo

Sanusi: Magajin Sanusi Da Kukuna

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 26, 2023
in Sarauta
0
Sarautar Kano: Akwai Yiwuwar Muhammadu Sanusi II Ya Dawo

Sarki Muhammadu Sanusi II

114
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Rabi’u Na’auwa

Sanusi: Magajin Sanusi Da Kukuna

Related posts

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

October 26, 2025
Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

October 22, 2025

Wani tarihi mai kyau da matuƙar muhimmanci yana neman maimaita kansa a Jihar Kano.

Sarkin Kano na talatin da biyu a Daular Hausawa, Mohammadu Kukuna Ɗan Alhaji, bayan ya zama Sarkin Kano, ya yi mulki shekara guda. Madawakin Kano na lokacin ya ƙulla maƙarƙashiyar cire shi daga Sarkin Kano, suka naɗa Soyaki. Shi kuma Kukuna ya yi gudun hijira zuwa ƙasar Zariya.

Soyaki ya yi wata uku yana sarauta sai manyan Kano suka haɗu suka yi shawara
a kansa. Gaba ɗayan manyan masu ƙarfin ikon Kano a wancan lokacin suka haɗu a ƙarƙashin Galadima Wari, da Ɗan Iya Babba tare da Makama, suka yi shawarar dawo da Sarkin Kano Muhammadu Kukuna gadon sarautarsa.

Wannan ya sa suka ɗaura ɗamarar yaƙi da Sarkin Kano Soyaki, suka fitar da shi daga Kano. Muhmmadu Kukuna ya dawo karagar mulkinsa, shi kuma Soyaki aka gina masag ida a Dukarawa, inda ya rasu a can.

Wani abin al’ajabi da mamaki shi ne, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya ɗauko tarihin Kakansa Muhammadu Sanusi na ɗaya tare da gadon duk wani
mataki da ya bi a loton sarautarsa a Daular Fulani, ta fuskar sauke dukkan nauyin da ya rataya a kan Sarki da talakawansa, a ilimance da zamanance da sauran matakai na rayuwa.

Wani tarihi da zai ƙara maimaita kansa shi ne, a jerin Sarakunan Hausawa ma,
Muhammadu Sanusi II ya ɗauko hanyar gadon Muhammadu Kukuna ɗan Alhaji,
kamar yadda aka cire Kukuna ta hanyar maƙarƙashiya, shi ma haka ta faru a kan
Muhammadu Sanusi II. Aka cire shi daga sarautarsa kamar yadda aka yi wa Kukuna.

Haka kuma kamar yadda Kukuna ya samu mafaka a Zariya kafin ya dawo karagar mulkinsa, haka shi ma Sanusi a ƙasar Zariya yake ƙarɓar gaisuwar mutanensa da ya yi wa nisa, sannan kuma a ƙasar Zariya yake gabatar da Sallar Idi.

Babban abin da zai ba ka mamaki shi ne, kamar yadda masu faɗa a ji a Jihar Kano suka ga cancantar dawowar Kukuna sarauta, haka yake a kan Muhammadu Sanusi. Shi ma mafi yawan masu faɗa a ji a Jihar Kano suna son su ga ranar da Sanusi zai dawo gadon sarautarsa. Haƙiƙa wannan ba ƙaramin abin al’ajabi ba ne.

A sarauta, dukkan wanda ya zamto Sarki, ana duba ga Sarakunan da suka gabata a
ga wa za a iya kwatanta shi da shi, ko ta fannin jarumta ko adalci ko jin ƙan talakawa da makamantansu. To amma ga Muhammadu Sanus,i shi al’amarinsa sai ya wuce dukkan yadda ake zato. Ga shi a zahiri ya yi gado ga Daular Fulani, gado irin na kwatance. Ya gama da wannan ɓangaren ya kuma tsallaka ga Daular Hausawa, ita ma ga shi zai ajiye muhimmin tarihin da ba a taɓa yin irinsa a tarihin ƙasar Hausa ba.

Haƙiƙa a idan haka ta tabbata, to Sanusi ya zama abin kwatance ko da kuwa a Daular Larabawa, domin samun gwarzon Sarki mai tagwayen tarihi yana da matuƙar wahala.

~~~~~~~

Na’auwa Marubuci ne kuma Mawallafi. Ya aiko da wannan sharhi daga Katsina.

~~~~~~~

Previous Post

Malamina Yana Sauke Alƙur’ani A Ƙasa Da Rabin Awa – Sheikh Maƙari

Next Post

ALLAHU AKBAR! YAU TAKE ARFA

Related Posts

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa
Sarauta

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

October 26, 2025
Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina
Sarauta

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

October 22, 2025
Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’
Sarauta

Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’

October 17, 2023
Next Post
ALLAHU AKBAR! YAU TAKE ARFA

ALLAHU AKBAR! YAU TAKE ARFA

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Sharhi A Kan Sharhi: Nazari da Sharhin Ayyukan Adabin Bukar Usman

Sharhi A Kan Sharhi: Nazari da Sharhin Ayyukan Adabin Bukar Usman

May 29, 2023
Ƙungiyar Marubutan Nahiyar Afirka (PAWA) Ta Buƙaci Marubuta Su Koma Yin Rubutu A Harsunan Gida

Ƙungiyar Marubutan Nahiyar Afirka (PAWA) Ta Buƙaci Marubuta Su Koma Yin Rubutu A Harsunan Gida

March 21, 2024
WATER PROJECT IN MALUMFASHI: COMMUNITY URGED TO SUPPORT GOVERNMENT

WATER PROJECT IN MALUMFASHI: COMMUNITY URGED TO SUPPORT GOVERNMENT

June 16, 2025
Nasarar Shari’ar Zaɓe: Ya Kamata Mu Mara Wa Shugaba Tinubu Baya – Janar Buratai

Nasarar Shari’ar Zaɓe: Ya Kamata Mu Mara Wa Shugaba Tinubu Baya – Janar Buratai

September 11, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.