Daga Mukhtar Mudi Sipikin
KAMUN LUDAYIN JEMAGE
A jiya Asabar, 22 ga Yuli, 2023, na fita yawon da na saba, sai na yi kiciɓis da Malam Na Fagge. Yana gani na, sai ya gayyace ni majalisinsa. Bayan na zauna na miƙe ƙafa, sai ya miƙo mani kofin shayi. Ya ce: “SHANSHANI, amshi wannan takardar, ka ɗan duba.”
Na amshi takardar, na ƙura mata idanu. Na kai kofin shayi bakina na kurɓa, sannan na maido hankali kan takardar, na ci karo da ƙorafin da ya rubuta, mai taken:
~~~~~~~
KAMUN LUDAYIN JEMAGE
Tattabara uwar alƙawari ta nisa ta ce, “Ko yaushe jagororin dajin nan za su fara tausaya wa tsuntsaye? Shekaru da yawa muna cikin azabar mulkin Babba-Da-Jaka, yanzu kuma ga shi Jemage shi ma dai yana neman ɗorawa daga inda ya tsaya, Kaico!”
Kurciya ta yi murmurshi sannan ta ce “Da ma ai mantawa kika yi, amma dama ai Jemage ya sha nanatawa cewa zai ɗora ne daga inda Babba-Da-Jaka ya tsaya, ya ko cika alƙawarin, don ga shi nan ya fara aiki gadan-gadan.”
Kanari da ke can gefe kuwa sai ta hau waƙa tana cewa:
“Iya yawan huƙurinku da juriyarku,
Iya yawan azabar da za su yi maku.
“A zaɓe, yawan tsabar da suka watsa,
Yawan Kogin wahalar da za ku ratsa.
“Tsuntsun da a yini guda ya yi zalama,
Zai shekara ko yana cikin nadama…”
“Ke Kanari, yi mana shiru! Waƙar taki ma duk babu daɗi. Ki ƙyale mu da abin da ke damun mu na ƙarin farashin ruwan sinadiri da aka yi mana.” Kurciya ta katse ta a fusace.
Bainu ta ce: “Duk da dai babu alamun tsufa gare ni, amma na daɗe a rayuwa ban ga tashin hankali da matsi da aka shiga irin wannan lokacin ba. Yanzu ta kai ta kawo tsuntsaye da yawa haka suke kwana babu ƙoto. Tsuntsaye duk a firgice. Ni daga yanzu ma sheƙar bauta zan koma da zama, don daga dukkan alamu ƙiyama ta kusa.”
Hazbiya da tun da aka fara zancen ba ta ce komai ba, ta kaɗa fiffike ta kimtsa sannan ta ce: “Na lura ba Jemage kaɗai ke da laifi ba, akwai Majalisar Ragon-Maza, su ma da su ake haɗo baki a gana mana azaba, sannan Balbela da ‘yan uwanta, su ma da su Kullum sai a rufe ƙofa da su, sai su je jihohinsu su nuna su nagari ne. Tabbas farin Balbela na yaudara ne. Da ka bincika namanta sai ka ga baƙi ne.”
Tsattsewala ta ce: “Haka ne kam, yanzu dai Jemage dai ya ba su sulalla da yawa, don kowa ya je jiharsa ya yi bajinta sannan ya taimaki tsunsayen jiharsa da tallafi don a rage raɗaɗin da ake ciki. Yanzu ya kamata tsuntsaye su sanya idanuwa a kan Balbelu, don a tabbatar sun yi amfani da sulallan da Jemage ya ba su a hanyar da ta dace.”
Dayake dare ya yi, nan tsuntsaye suka yi sallama, kowa ya nufi sheƙarsa.
An hango Alhudahuda a ciƙin sheƙarsa a tsakkiyar wasu manyan littattafai, sanye da farin gilashi, yana ta bincike.
~~~~~~~
Malam Mukhtar Mudi Sipikin marubuci, sha’iri, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa ne a Kano-Nigeria.
~~~~~~~













