Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Har Yanzu Akwai Cutar AIDS Kuma Za Mu Taru Mu Yaƙe Ta Da Gaske – Dokta Bala Nuhu
~~~~~~~
Dokta Bala Nuhu, Sadaukin Kankiya, yana ɗaya daga cikin jajirtattun matasa masu ƙoƙarin yi wa jama’a hidima da ilimin da Allah Ya ba su. Likita ne, ɗan siyasa ne, saraki ne kuma mai jin ƙan marasa galihu ne. Shi ne Babban Sakataren Hukumar Yaƙi Da Cutar Ƙanjamau ta Jihar Katsina (SACA). TASKAR GIZAGO ta tattauna da shi, inda ya bayyana ƙudurorinsa, na yadda zai sauke nauyin da aka ɗora masa na jagorancin wannan hukuma. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
~~~~~~
Shin yaya wannan hukuma take kuma mene ne taƙamaimai aikinta a Jihar Katsina?
Dokta Bala ya amsa da cewa: Ita wannan hukuma ma, ita ce wadda ke tsaye domin tabbatar da ganin cewa an shawo kan cutar AIDS, wacce wasu ke kira Cutar Ƙanjamau ko Sida a duk faɗin Jihar Katsina kuma tana da alaƙa da sauran hukumomi na kiwon lafiya gaba ɗayansu.
Ko za ka faɗaɗa bayani dangane da aikin hukumar?
Dokta Bala ya ce: Sanin kowa ne cewa ita Ma’aikatar Lafiya da sassa da rassa daban-daban. To ita wannan hukuma tana ɗaya daga cikin sassa da suka haɗu suka yi Hukumar Lafiya ta Jihar Katsina (Ministry of Health). Aikinmu a wannan hukuma shi ne mu tabbatar da cewa mun yi duk yadda ya kamata domin ganin cewa an ɗauki matakai na kariya ga cutar AIDS da kuma ma cututtukan da suke da alaƙa da ita; musamman dukkan wata cuta da take da alaƙa da jini ko makamancin haka. Wannan hukuma tana da ikon ta tabbatar da cewa ta shiga ta fita domin ganin ta ɗauki matakan kawar da wannan cuta. Musamman ma dai matakai na kariya da kuma ba da tallafi na musamman ga waɗanda suka riga suka kamu. Kamar wajen shan magunguna da kuma ɗaukar matakan da za su sauƙaƙa masu matsalolin da suke fuskanta a sakamakon wannan cuta da suke ɗauke da ita.
Ta fuskar yekuwa da wayar da kan al’umma kuma fa, ko hukumar na da ruwa a nan?
Dokta Bala ya amsa da cewa: Lallai kam cikin ayyukanta, akwai wayar da kan al’umma domin su fahimci wannan cuta da kuma ganin yadda mutum zai kare kansa daga kamuwa da ita. Akwai kuma batun ɗaukar matakai na gaggawa a Kowane lokaci domin tabbatar da cewa an ba al’umma dukkanta kariya, domin kada wannan cuta ta kama mutum ko makamancin haka.
Mene ne alaƙar wannan da irin ta a Gwamnatin Tarayya (NACA) da sauran hukumomin lafiya na duniya?
Dokta Bala ya ce: Haƙiƙa wannan hukuma tana da alaƙa da ƙungiyoyi na duniya, musamman World Bank da Global Fund da UNAIDS. Haka kuma idan ka dawo matakin Tarayya, akwai ƙungiyoyi kamar ita kanta NACA (National Agency for the Control of AIDS), inda a nan jiha ita ce kamar ƙanwarta ke nan. Saboda haka, bayan wannan akwai ƙungiyoyi irin su Society for Family Health, Institute for Human Virology Nigeria, akwai irinsu Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da su UNICEF, da dai sauran ƙungiyoyi manya-manya a kowace ƙasa, musamman a Najeriya.
Wacce irin gudunmawa irin waɗannan ƙungiyoyin suke bayarwa?
Dokta Bala ya ce: Waɗannan ƙungiyoyi suna nan suna ba da gudunmawa domin tabbatar da cewa an kawar da wannan cuta ta AIDS. Kuma ina tabbatar maka da cewa za mu yi amfani da damarmu, domin tabbatar da cewa mun shiga mun fita, mun samu alaƙa kyakkyawa da waɗannan ƙungiyoyi da kuma ita kanta gwamnati, musamman ƙarƙashin mai girma Gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa (phD), domin tabbatar da cewa wannan hukuma ta samu kulawa ta musamman kuma ta yi aikinta yadda ya kamata. Haka kuma za mu tabbatar da cewa mun haɗa kai da masarautun gargajiya, wato sarakuna ke nan da malamanmu na addini da kuma ƙungiyoyi masu fafutukar ganin an kawar da cutar nan da kuma cutar da ke da alaƙa da ita a Najeriya da kuma Jihar Katsina baki ɗaya. Wannan shi ne a taƙaice.
Wasu na ganin kamar wannan cuta ta Ƙanjamau (AIDS) babu ita yanzu. Me za ka ce kan wannan?
Dokta Bala ya amsa da cewa: Kamar yadda aka sani dai gaskiya, a ƙididdigar alƙaluman da muke da su a nan yanzu, wannan cuta ba wai babu ita ba ne, akwai ta har yanzu. Sannan kuma tana ci gaba da yaɗuwa, musamman a jiharmu ta Katsina da kuma Najeriya gaba ɗaya. Kusan duk jihohin Najeriya babu inda ba wannan cuta. Kawai dai mutum zai yi tunanin ta ɗan yi ƙasa. Wannan kuma ya biyo bayan irin ƙoƙarin da gwamnati take yi da kuma hukumomin da ke fafutukar yaƙi da wannan cuta. Tabbas sun yi rawar gani ƙwarai da gaske kuma shi ya sa wannan cuta cikin ikon Allah ta yi ƙasa sosai kuma ana samun gudunmawa ƙwarai da gaske. Mutane suna zuwa suna awo kuma idan an tabbatar da mutum yana da ita, ana ɗora shi kan magani kuma ana tabbatar da yana shan maganin.
Mene burinku dangane da wannan cuta?
Dokta Bala ya ce: Babban burinmu shi ne, mutane su yi awon, a tabbatar da cewa ba ka da wannan cutar. Idan kuma kana da ita, za a ɗora ka a kan magani kuma in dai kana shan maganin, in sha Allahu za ka ga ka samu sauƙi ƙwarai da gaske. Za ka kasance kana hidimarka ta yau da kullum kamar ma ma ba ka ɗauke da cutar. Wannan shi ne ke faruwa kuma shi ne za mu zo mu tabbatar da mun inganta shi.
Na biyu kuma, ya kamata a sani cewa ita wannan hukuma, musamman a mu nan Jihar Katsina, tana kula ne da yadda za a tabbatar da cewa an kawar da cutar AIDS amma akwai wasu jihohinmu waɗanda muka maƙwabta da su, su sun inganta aikin wannan hukuma, da yadda cewa lallai sun ƙaro wasu cututtukan da ke da alaƙa da ita. Musamman idan ka ɗauki cutar Maleriya da cutar Tubaculosis, waɗannan cututtukan guda uku, kodayaushe suna da alaƙa saboda suna da dangantaka da jini ne ta wani ɓangare. Sh ya sanya yake da muhimmanci mu ma mu ga yadda muka inganta aiki na wannan hukuma, mun ƙara jawo waɗannan cututtuka su dawo ƙarƙashin kulawar wannan hukuma.
Haka kuma akwai cuta ta Sikila, wacce ita ma kanta ta zama ruwan dare. Don haka ƙoƙarinmu shi ne mu dawo da waɗanan cututtukan ƙarƙashin kulawar wannan hukuma, domin na ɗaya, mu rage yawan yadda gwamnati take kashe kuɗi wajen bibiyar tsare-tsare mabanbanta, nan da can. Sannan kuma na biyu, mu tabbatar da cewa mun inganta yanayin yadda ake samun taimako da gudunmawa na ƙungiyoyi, wanda wasu jihohin kamar yadda na faɗi a baya, sun yi irin wannan ƙoƙarin kuma haka suke ci gaba da yi. Wannan hukuma a matsayinta na SACA, tana kula da cututtuka waɗanda suka shafi Maleriya da Tubaculosis da Sikila da kuma sauransu. To mu ma ƙoƙarin da za mu yi ke nan a Jihar Katsina. Mu zamanto cewa mun samu dama, idan mai girma Gwamna ya ba mu dama, mu haɗa su wuri guda, mu tunkare su kai tsaye, mu tabbatar da ɗaukar matakan da suka dace, domin magance su. Na uku, za mu tabbatar da cewa mun haɗa gwiwa da manya-manyan ƙungiyoyin da ke ba da tallafi na duniya, domin tabbatar da cewa an ƙara inganta yadda ake gudanar da harkokin lafiya a Jihar Katsina baki ɗaya. Wannan shi ne ƙudurinmu kuma in sha Allahu a kansa muke kuma za mu yi ƙoƙari mu tabbatar da cewa mun kawo hanyoyi na zamani domin inganta yadda ake yaƙar cututtuka a Jihar Katsina.
A hukumance, wane kira za ka yi ga al’umma dangane da yaƙi da wannan cuta?
Dokta Bala ya ce: Kiran mu ga al’umma shi ne, kamar kodayaushe ita dai lafiya, Hausawa kan ce uwar jiki. Dole sai da lafiya ce za ka iya yin duk abin da ya kamata kayi. Saboda haka muna kira ga al’umma da su ba mu goyon baya da haɗin kai. Musamman ita wannan hukuma, alhakinta ne ta ga ta inganta yanayin mutane domin su fahimci shin mece ce ma ita wannan cutar, yaya ake kamuwa da ita, idan ka kamu, mece ce illar ta? Sannan kuma me wannan cutar za ta iya jaza maka?
Idan mutane suka fahimci wannan, to za a ga cewa abu na gaba shi ne ta yaya za su kare kansu? Idan kuma sun ɗauka, to ta yaya za su inganta hanyoyin samun magani domin mutum ya ci gaba da rayuwa da mu’amala da mutane kuma ka ga ka ci gaba da ba da gudunmawa a matsayinka na ɗan Adam.
Na biyu akwai iyayenmu, wato iyayen ƙasa, sannan kuma akwai limamai, sannan akwai kuma uwa uba, ita kanta gwamnati da kuma dukkan al’umma gaba ɗaya. Waɗannan ɓangarori guda huɗu ko biyar, duk da mu ma’aikatan hukumar ke nan, muna kira a gare su; mu tabbatar da cewa mun samu haɗin kai ƙwarai da gaske. Ta yadda yaya za mu ga mun tafiyar da wannan aiki namu? Domin burinmu shi ne mu kawo hanyoyi na zamani sababbi, waɗanda ba a san da su ba. Misali, idan ka zo maganar awo wanda ake yi yanzu haka a Arewacin Najeriya, har da ita kanta wannan jiha tamu, mun yi ƙoƙarin tabbatar da cewa, kusan duk wanda zai yi aure, ya yi ƙoƙari ya tabbatar da ya yi awo na wannan cuta. Kuma Alhamdu lillahi, ana samun ci gaba ƙwarai da gaske.
Waɗanne hanyoyi da dabaru za ku bi domin samun nasarar wannan babban aiki?
Dokta Bala ya amsa da cewa: Abin da za mu yi shi ne, idan mun zo aiki, in sha Allahu za mu haɗa kai, mu haɗa gwiwa da dukkan ɓangarori na al’umma gaba ɗaya. Ɓangaren masarautunmu da shugabanninmu da malamai na addini da ƙungiyoyin matasa da na mata da na ‘yan kasuwa da ita kanta gwamnati, domin mu tabbatar da cewa lallai mun kawo wani tsari wanda zai zamanto, cewa duk wanda zai aure, ya samu Takardar Shaidar Aure. Domin a Kudancin Najeriya ana wannan. Wannan takardar, ita za ta ba ka shaida a kan cututtuka guda uku, cutar AIDS da Sikila da kuma cutar Haifataitis. Waɗannan cututtuka uku, suna da muhimmanci a kan san matsayinka game da su, kana da su ko babu? Musamman a duk lokacin da mutum zai yi aure, ya tabbatar da cewa ya yi awo game da su, domin sanin matsayinsa.
Sannan idan Allah Ya sa mun samu dama a wannan hukuma ta SACA, za mu fito da wani tsari, na wani satifiket da za mu riƙa bayarwa a duk faɗin Jihar Katsina, a manya da ƙananan asibitocinmu, duk wanda zai yi aure, a tabbatar da cewa an yi masa ko mata wannan awo, idan ba su ɗauke da waɗannan cututtuka, to za a ba su Takardar Shaida, wacce za ta tabbatar masu da cewa sun samu damar su je su yi aure, ba tare da wata shakka ko fargaba ba.
Wannan zai zama wata ɗanba in sha Allahu. A tabbatar da cewa an inganta al’amarin, yadda abin zai zama doka domin maslahar al’umma bisa fahimta. Wannan zai taimake mu ƙwarai da gaske. Saboda haka muna kira ga al’ummar Jihar Katsina, a ba wannan hukuma goyon baya, yadda ya dace, domin mu zo mu tabbatar da cewa mun ba da gudunmawarmu wajen inganta lafiyar al’umma na Jihar Katsina.













