Allah Ya amshi ran mawaƙin nan da ya shahara a soshalmediya, Mahmud Nadanko, a sakamakon hadarin mota.
Ga waɗanda ke bibiyar Marigayin a soshalmediya, Mahmud ya yi fice a rera waƙoƙin shaguɓe da tsokana domin nishaɗantarwa. Ɗaya daga waƙoƙin nasa, ita ce “Baba Zai Daɗa Aure”
Da yake sanar da labarin rasuwar tasa a shafinsa na Facebook, marubuci Abba Abubakar Yakubu ya ƙarƙare da addu’ar “Allah Ya ji ƙan sa da rahama. Mu ma Ya kyautata namu ƙarshen. Amin.”














Ma sha Allah
Komai sahihi, kima ingantacce.
Allah ya ƙara ɗaukaka gidan Jaridar nan ta GIZAGO.
Amin Amin Ya Allah. Muna matuƙar godiya! Allah saka da alheri.
Ma sha Allah!