• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, July 27, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Shanshani

Sheikh Abduljabbar Ya Kusa Samun ‘Yanci

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 5, 2023
in Labarai, Shanshani
0
Sheikh Abduljabbar Ya Kusa Samun ‘Yanci
100
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Ni Shanshani ina zaman zama na aka iske ni da tsegumi. Wai saura kaɗan shugaban ‘yan kogo, Sheikh Abduljabbar ya samu ‘yanci.

A cikin ruɗu na waigo na ce wane ne zai ba shi rigar ‘yancin? Shin ba ka san cewa Shari’a ce ta garƙame shi ba?

Related posts

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karrama Tsofaffin Dakarunta

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karrama Tsofaffin Dakarunta

July 7, 2026
Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

April 19, 2026

Mai ba ni labarin ya ce, “ashe ba ka san bidirin da ake ciki ba? Ba ka san cewa an samu sabuwar gwamnati ba?”

Ni kuwa na ƙuta, na haɗiye wani yau da ya ɗan taru a bakina, na ce masa, ai kuwa ni na san an samu gwamnati sabuwa. Na san an rantsar da Abba Kabir Yusuf a matsayin sabon Gwamnan Jihar Kano. To me ya haɗa sabon Gwamna da batun gidan yari ko kuma sha’anin Abduljabbar?

Mutumin ya kalle ni sheƙeƙe haka, ya yi wata ‘yar dariya mai kama da yaƙe. “Haba Shanshani, ashe ba ka san Shaikh Abduljabbar cikakken mai goyon bayan gwamnatin Abba ba ne?”

Ni ma sai na yi murmushi, na ce masa “kana nufin Gwamna zai yi wa Shari’a ƙarfa-ƙarfa? Kuma shi ke nan an gaya maka shi Gwamna da ka zai yi mulkin?”

Nan da nan mutumin nan ya yi fuuu cikin fushi kamar tsohuwar kububuwa, ya harzuƙo ni da hayagaga.

“To, ka saurara ai muna nan da kai, za ka gani. Muddin muna da rai, nan da ‘yan kwanaki za ka ga Sheikh Abduljabbar a bisa ingarman doki, cikin kwalliyar ƙasaita, tare da dubban ‘yan rakiya, ya keto garin Kano daga jarun, har zuwa gidansa.”

Ni kuwa na yi shiru da bakina, na ce ba zan biye wa mutumin nan ba, don kar tsautsayi ya ɗebe shi ya ce zai bige ni. Kawai sai na ga mutumin ya sauko daga fushin nasa, ya ɗaga hannuwa sama kamar ƙauran da ke shirin shiga daji, ya wuce yana cewa:

“Na fito yawo gabagaɗi babu mai iya jijjiga ni!”

 

Previous Post

Daura Birnin Bayajidda: Janar Buratai Da Ayarinsa Sun Ziyarci Buhari Da Sarki

Next Post

Rusau A Kano: An Fara Kama Ɓarayin Kayan Mutane

Related Posts

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karrama Tsofaffin Dakarunta
Labarai

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karrama Tsofaffin Dakarunta

July 7, 2026
Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi
Labarai

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

April 19, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Labarai

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Next Post
Rusau A Kano: An Fara Kama Ɓarayin Kayan Mutane

Rusau A Kano: An Fara Kama Ɓarayin Kayan Mutane

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Yau Maulidin Bilkisu Babangida

Yau Maulidin Bilkisu Babangida

September 3, 2023
A Harkar Rubutu: Na Fi Fuskantar Matsala Daga Mata – Uwa Idris

A Harkar Rubutu: Na Fi Fuskantar Matsala Daga Mata – Uwa Idris

July 4, 2023
Jinjina Da Yabo Ga Nagartaccen Shugaba: Malam Labiru Musa Ƙafur, mni

Jinjina Da Yabo Ga Nagartaccen Shugaba: Malam Labiru Musa Ƙafur, mni

October 29, 2025
RAMADAN KARIM: 17-1447

RAMADAN KARIM: 17-1447

March 6, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today
  • Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
  • Saƙon Godiya Da Bangajiya

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

July 25, 2026
Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.