• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 17, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Tun Asali Jami’ar Gwamnatin Tarayya Ta Malumfashi Ce

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 7, 2023
in Gizago
0
Tun Asali Jami’ar Gwamnatin Tarayya Ta Malumfashi Ce

Gwamna Malam Umaru Raɗɗa

564
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Abdullahi Ibrahim Mahuta

Federal University of Medical Sciences Malumfashi/Funtua: Yadda Lamarin Yake

Related posts

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026

Tarihin Wannan Jami’a.

Da farko dai, a kwai bukatar al’umma su fahimci cewa wannan Jami’a, ta na daya daga cikin jamioi irin su guda goma sha takwas (18) wadanda Senate president na lokacin, Sen. Ahmed Lawal, ya gabatar da kudirin su a gaban majalisar dattawa.

Senate sun gabatar da karatuttukan wannan kudiri a wadannan ranaku:

1st reading Wednesday, 21/4/2021
2nd reading Wednesday, 19/1/2022
3rd reading Tuesday, 5/4/2022

Kamar yadda na fada a sama, da farko wannan qudiri ya na dauke da jam’io’i uku a kowane zone. A Northwest zone akwai su kamar haka

1. Katsina state…….Malumfashi
2. Sokoto state………Dange
3. Kano state…………Kabo.

Daga baya ne senatoci su ka zauna su ka fahimci cewar kirkiro sababbin jami’o’i har guda 18 a kasan nan abin zai yi wahala. Saboda haka aka rage su zuwa guda daya a kowane zone. Shine a zone din mu aka zabi Malumfashi a jahar katsina.

Bayan da su ka zama guda shidda, sai Senate President na lokacin ya yi shawarar bari ya je ya samu shugaban kasa Buhari ya sanar da shi irin tunani da kuma shirin da Senate su ke yi game da wadannan jam’io’i. Shugaba Buhari ya yi farin ciki ya kuma yi na’am da wannan shawara. A dalilin haka ne ma ya nuna shaawar shi ta taking over wannan shiri daga hannun majalisa ya maida shi wani shiri na bangaren executive. Wannan dalilin ne ya sa qudirin ya tashi daga tsarin na doka wanda ke bukatar majalisa ta yi passing din shi shugaban kasa ya kuma sa ma shi hannu, ya koma shirin gwamnati wanda baya bukatar wancan dogon process din.

A wannan dalilin ne ma ya bukaci a yi hanzarin ganin wannan kyakkyawan shiri ya tabbata ta hanyar zama na musammam da jami’an ma’aikatar ilimi da ta lafiya. A lokacin wannan zama ne, jami’an ma’aikatar lafiya su ka ba da shawarar a chanza ma wadannan jamioi su na daga “..Medical Sciences…” zuwa “…Health Sciences…” which , according to them, is all encompassing…. A halin da ake ciki, yanzu haka wadda aka Kai Azare har sun fara karatu kasancewar ministan ilimi na lokacin dan Azaren ne.

Tarihin Zuwan Wannan Jami’a Malumfashi Tun Farko.

A lokacin da Senate President, Ahmad Lawal, ya zo da wannan qudiri, ya nemi shawarar Sen. Bello Mandiya akan ina ya ke ganin ya kamata akai wannan Jami’a a Jihar Katsina?. Sen. Bello Mandiya ya ba da shawarar cewa kasancewar yankin Funtuwa zone ne kadai babu Jami’a a jahar Katsina, to ya na neman alfarmar a kai ta a Malumfashi.

Ya kuma zabi Malumfashi ne domin kamar yadda kowa ya sani, shi Sen Bello Mandiya ya gabatar da wani qudiri wanda ya samu amincewar majalisu biyu na tarayya akan kirkiro jam’iar noma, Federal Universality of Agriculture, wadda ya ce a Kai ta a garin Funtuwa, a matsayin headquarter ta wannan zone din. To ganin cewa already a akwai wannan University da ya ke kokarin ganin ai kafa ta a Funtuwa, shi ya sa ya ce ita wannan ta medical sciences din a kaita Malumfashi. Musammam ganincewa a garin Malumfashi akwai school of Midwifery wace ana iya upgrading din ta kawai.

Na yi mamaki kwarai da gaske yadda na ga manyan dattijai daga Funtuwa sun tafi har Abuja wurin mai girma gwamna da rokon su na son a dauke wannan Jami’a daga Malumfashi zuwa Funtuwa. Ganin cewa mutanen Malumfashi ba su taba nuna wani kyashi ko rashin goyon baya ba ga abinda zai kawo ci gaban Funtuwa ba a matsayin ta na headquarter na wannan yankin. Ina da yakinin cewa da sun tuntubi mutanen Malumfashi akan wannan bukata ta su, da a tsakanin mu ma, cikin yardar Allah, mun cimma matsaya. Mu kuma je ma mai girma gwamna da murya daya, kamar yadda mu ka saba yi ma su kara a baya.

Misali, Sen Bello Mandiya, duk da kasancewar shi Dan Malumfashi, da ya gabatar da qudirin University of Agriculture, Funtuwa ya ce akai ta ba Malumfashi ba. Hakanan lokacin da za a dauke federal medical center daga Katsina zuwa Daura, Hon. Babangida Ibrahim Mahuta, dan Malumfashi, shi ne dan majalisar da ya tashi a gaban majalisar ya yi kira da akai wannan asibiti zuwa garin Funtuwa ba Daura ba. Bai ce akai ta Malumfashi ba.

Nema, halal ne; ya halarta. Neman abin wani; kokarin kwace abinda har ya zo hannun wani, wannan shine haramun. Shine rashin daidai a musulunce; shine kuma rashin daidai a kyakkyawan tsari na zamantakewa.

Daga karshe ina mai addu’ar Allah ya sa albarka a cikin wannan Jami’a. Allah kuma ya sa ta amfani dukkan al’ummar jihar Katsina gaba dayan su, a duk inda Allah ya hukunta za a kafa ta…..

Wannan shine gaskiyar abinda ya faru. Shi ya sa na yi attaching official document as proof.

Previous Post

Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Tumbu-Madalla

Next Post

Gidauniyar Qatar Foundation Za Ta Gina Katafariyar Makaranta A Jigawa

Related Posts

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso
Gizago

Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso

March 29, 2026
Next Post
Gidauniyar Qatar Foundation Za Ta Gina Katafariyar Makaranta A Jigawa

Gidauniyar Qatar Foundation Za Ta Gina Katafariyar Makaranta A Jigawa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

SASSANYAN AMINCI (5)

SASSANYAN AMINCI (5)

September 12, 2025
Matsalolin Tsaro: Ƙungiyar ‘Yan Jarida Ta Arewa Ta Shirya Taron Neman Mafita

Matsalolin Tsaro: Ƙungiyar ‘Yan Jarida Ta Arewa Ta Shirya Taron Neman Mafita

November 7, 2025
Shugaba Tinubu Ya Yi Wa Emefiele Tatas

Shugaba Tinubu Ya Yi Wa Emefiele Tatas

June 24, 2023
IGABI AIR STRIKE: A Call for Justice

IGABI AIR STRIKE: A Call for Justice

December 5, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Mu Ji Tsoron Allah
  • Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
  • Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Mu Ji Tsoron Allah

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.