• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, November 3, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Siyasa

Yanzu Dai Ta Tabbata Cewa Arewa Ta Tunibu Ce

AL'AMURAN SIYASA

Abdulaziz Abdulaziz by Abdulaziz Abdulaziz
October 26, 2026
in Siyasa
0
Yanzu Dai Ta Tabbata Cewa Arewa Ta Tunibu Ce

Tarin jama'a a taron Kaduna. A tsakiya kuma, Abdul'aziz Abdul'aziz ne

13
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Yanzu Dai Ta Tabbata Cewa Arewa Ta Tunibu Ce

Daga Abdulaziz Abdulaziz

Related posts

Gwamna Radda Ya Cancanci Maimaita Kujerarsa

Gwamna Radda Ya Cancanci Maimaita Kujerarsa

October 14, 2026
Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami

Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami

October 10, 2026
Tarin jama’a a taron Kaduna. A tsakiya kuma, Abdul’aziz Abdul’aziz ne

 

__________

Jiya a garin Kaduna, tsohuwar cibiyar siyasar Arewa, Arewa ta yi ta ƙara fito da matsayinta a matsayin ginshiƙin siyasar Najeriya. Wannan babban taro zai ci gaba da damun waɗanda suka shafe watanni suna yaɗa ƙaryar cewa Arewa ta yi watsi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Filin wasa na Ranchers Bees da ke Kaduna ya cika maƙil, har al’umma suka bazu zuwa titunan da aka ƙawata da manyan alluna da tutocin Jam’iyyar APC da hotunan Shugaban Ƙasa. Ko’ina ka duba allunan rubutu masu ɗauke da saƙon ‘Arewa for Asiwaju’ ‘Sai Tinubu’ ‘Tinubu 2 Times’ da sauransu.

Wannan taro ya kasance wani dandalin haɗuwa ne na mutanen Arewa, kama daga Hausawa zuwa Fulani, ‘yan Tibi, Idoma, Gbagyi, Yarabawa, Nupaw, da Barebari. Gwamnonin APC na Arewa gaba ɗaya, tare da goyon bayan takwarorinsu na Kudu, sun zauna kafaɗa da kafaɗa da tsofaffin gwamnoni, ‘yan majalisu, limamai, fastoci, shugabannin mata da masu sana’o’i, waɗanda suka taka kilomita da dama domin ganin mutumin da har yanzu suke kira Jagaba, wato jagora.

Wannan taro ya wuce taron al’ummar da aka biya kuɗi, domin su halarta, taro ne na gaske, mai cike da ɗimbin al’umma, kuma mai cike da shauƙi. Wasu hotuna daga taron sun bayyana hakan sosai, ka duba hoton wasu  mutane uku masu cike da farin ciki su na ɗagawa shugaban ƙasar su hannu, yayin da shi kuma ya sauke gilashin motar sa domin gaishe su. Dubi hotunan ɗimbin mutanen da su ka kwana a wurin taron domin su samu gurbi mai kyau na shaida abin tarihi, da kuma hotunan matasa maza da mata masu murna waɗanda su ka shafe yini guda a cikin rana su na kaɗa tutoci tare da rera yabon shugaban.

Wannan saƙon Arewa ne, saƙo ne da yake cewa har yanzu Arewa na tare da mai ƙaunarta. Kamar yadda na rubuta a watan Fabrairun 2023, a lokacin yaƙin neman zaɓe na baya, lokacin da wasu mutane su ka yi ƙoƙarin tunzura mutane saboda ƙabilanci domin su juya ra’ayin al’umma a kan sa, Asiwaju Tinubu da Arewa sun daɗe su na abota. Wannan abota ba ta neman cin moriya ba ce kawai. Abota ce mai tushe a tarihi. Wasu da dama basu sani ba cewa tafiyar siyasar Tinubu ba ta fara a Legas ba. Ta fara ne da Arewa.

A shekarar 1991, a farkon Jamhuriya ta Uku wadda ba ta samu nasarar kammaluwa ba, lokacin da Janar Ibrahim Babangida ya kafa jam’iyyun siyasa guda biyu, Tinubu yana da zaɓin yin siyasa da ƴan uwansa Yarabawa. Shaharraren ɗan siyasar Legas, Cif Lateef Jakande, yana cikin harkar siyasa. Duk da haka, Tinubu ya zaɓi ya haɗa kai da ƙungiyar siyasa ta Peoples Front (PF) ta Janar Shehu Musa Yar’Adua.

A ƙarƙashin jam’iyyar SDP, ta hanyar wannan ƙungiya ta PF, Tinubu ya zama Sanatan Legas ta Yamma a shekarar 1992. Lokacin da MKO Abiola ya zama ɗan takarar SDP, Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wurin matsa lamba domin Ambasada Babagana Kingibe, ɗan asalin Borno, ya zama abokin takarar Abiola a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.

Wannan zaɓin da ya yi a shekarar 1991 shi ne ya tsara salon siyasar sa tun daga lokacin har zuwa yau.

Lokacin da Shugaba Obasanjo ya so murƙushe Atiku Abubakar a shekarar 2007, Bola Tinubu ne ya zama mai ceton sa. A shekarar 2011, ya taimakawa Nuhu Ribadu domin ya yi takarar shugaban ƙasw, sannan ya taimakawa Muhammadu Buhari a zaɓen 2015 da na 2019. Haka nan a shekarar 2011, ya goyi bayan Aminu Tambuwal domin zama Kakakin Majalisar Wakilai, a lokacin da jam’iyyar sa ta PDP ta yi adawa da shi.

Babu wani ɗan siyasar Kudu da ya zuba jarin siyasa mai yawa irin wannan domin tallafawa Arewa.

Haƙiƙa, Arewa ba ta mantawa da halarci. Wannan ne ya sa ƙungiyar Arewa for Asiwaju, wata ƙungiyar siyasa da ta ƙunshi manyan jiga-jigan siyasar Arewa, ta cancanci yabo saboda wannan mataki da ta ɗauka a daidai lokacin da ya dace.

A lokacin da ƴan adawa ba su da abin da za su gabatar sai tsoffin batutuwan tallafin man fetur da aka cire, waɗanda a ke iƙirarin cewa ba su dace da dokar PIA ba, tare da ƙaryace-ƙaryacen da aka ƙirƙira ta amfani da fasahar AI, waɗanda Gwamna Uba Sani ya yi gargaɗi a kan su yadda ya kamata a Kaduna, A4A tana samar da abin da Arewa ta fi buƙata, wato tattaunawa ta gaskiya cikin Hausa, Fulfulde, Tiv, Nupe, Gbagyi da Kanuri, a kowace kasuwa, tashar mota, masallaci da coci.

A4A ba wai ƙungiya ce ta yaƙin neman zaɓe ba kawai. Tunatarwa ce cewa abota tana buƙatar amana daga ɓangarori biyu, kuma Arewa tana da riƙo da aƙidunta ta na adalci, gaskiya, zaman lafiya da jituwa, da kuma haɗin kan ƙasa.

A matsayin ta na ƙungiyar siyasa, babban manufar A4A ita ce samar da haɗin kan al’ummarmu da gudanar da yaƙin neman zaɓe bisa hujjoji. Manufar ita ce a mayar da martani ga ƙaryar cewa Shugaba Asiwaju Tinubu ya yi watsi da abokansa mutanen Arewa tun bayan da ya zama shugaban ƙasa.

Ta yaya? Shin ta hanyar kafa Ma’aikatar Bunƙasa Kiwo, wadda Arewa ta daɗe tana buƙata tsawon shekaru 60? Ko ta hanyar kafa Hukumar Bunƙasa Arewa ta Tsakiya da Hukumar Bunƙasa Arewa maso Yamma? Ko ta hanyar sabbin jami’o’in tarayya a Mubi, Kachia da Kabo?

Shin mutumin da ya yi watsi da Arewa zai yi gaggawar kammala layin dogo na Kano zuwa Maradi ko kuma hanyar Akwanga–Lafia–Makurdi? Shin zai kafa cibiyoyin kula da cutar daji (cancer) tare da inganta asibitoci da makarantu da dama?

Arewa for Asiwaju tana gabatar da waɗannan tambayoyi ne tare da hujjoji masu ƙarfi. Kaduna ta samar da wata dama ta ƙara rusa hayaniyar ƴan adawa marar tushe. Arewa ta haɗu ta fito da murya ɗaya mai ƙarfi. Gwamnoni 18 daga cikin 19, jerin tsofaffin gwamnoni tun daga waɗanda su ka fara mulki a 1999 zuwa yau, ɗimbin matasan ƴan siyasa masu tasowa, da rundunar masoya jam’iyya, duk sun halarta.

Abun abin sha’awa ne. Tsawon watanni, wasu ƴan tsirarun mutane amma masu yawan surutu a Abuja da shafukan sada zumunta sun yi ta ƙoƙarin yaɗa wani labari na ƙarya cewa Arewa ta yi nadamar zaɓen Tinubu a 2023, cewa shugaban ƙasa da masu yaƙin neman zaɓen sa ba za su iya sake shiga Arewa ba, kuma an riga an yanke hukuncin zaɓen 2027 tun yanzu.

Taro ɗaya a Kaduna ya binne wannan ƙaryar. Kamar yadda Darakta Janar na Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari ya bayyana duk wani muhimmin mutum a Arewa yana filin wasan jiya. Yawancin su sun halarta da kan su, yayin da wasu da dama su ke tare da su a zuciya. Ƙalilan masu adawa waɗanda su ka watse ba su da wani tasiri da zai iya haifar da babban sauyi a siyasa.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Yari ba su zo Kaduna domin yin dogon jawabi mai cike da kalmomin siyasa ba kawai. Sun zo da tarihi da kuma hujjojin da za su tabbatar da maganganun su.

Kamar yadda aka saba, Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ya yi magana kai tsaye kuma cikin kaifin basira. Ya yi amfani da saƙo mai ƙarfi domin tunatar da masu zaɓe a Arewa zaɓuɓɓukan da su ke da su.

Ya ce, “Ba don mun fi kowa hikima ko arziƙi muka yi nasara a shekarar 2023 ba, sai don kun duba zaɓuɓɓukan da ke gaban ku, ku ka fahimci cewa ɗaya zaɓin zai jefa ƙasa cikin masifa. Mun zo ne domin mu roƙe ku ku sabunta wa APC wa’adin mulki na biyu, daga sama har ƙasa.”

Sanata Yari, wanda ya bayyana farin cikinsa a fili ya tabbatar da cewa: “Da yardar Allah, Arewacin Najeriya tana goyon bayan ka, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu,  100 bisa 100, kuma mun ƙuduri aniyar cika alƙawarin mu a ranar 16 ga watan Janairu, 2027.”

Ya kuma ƙara da cewa ya kamata Shugaba Tinubu ya kwanta ya huta, ya jira nasara.

Wani abin sha’awa shi ne Shugaba Tinubu bai je Kaduna domin neman ƙuri’u ko nuna yawan magoya bayan sa ba kawai. Ya je ne tare da ayyukan da aka aiwatar.

A wani abu da ba a saba gani ba a tarukan yaƙin neman zaɓe, Shugaba Tinubu ya yi amfani da wannan dama wurin ƙaddamar da ɓangaren hanyar Kaduna zuwa Abuja mai tsawon kilomita 81, ta hanyar yanka ƙyalle a matsayin alamar ƙaddamarwa.

Wannan ɗaya ne kawai daga cikin ɗimbin alherin da Kaduna ta samu daga gwamnatin Tinubu. A jawabin sa na maraba, Gwamna Uba Sani ya lissafa fa’idoji da dama da jihar Kaduna ta samu daga gwamnatin Tinubu, waɗanda su ka haɗa da hanyoyi, layin dogo, jami’o’i da cibiyoyin kiwon lafiya.

Kamar yadda Gwamna Sani ya tabbatar, Arewa ba ta taɓa samun irin wannan alheri ba a baya.

Shugaba Tinubu yana mayar da martani ga amincin da aka nuna masa ta hanyar ayyukan raya ƙasa, gine-gine masu ɗorewa da kulawa da al’umma.

Daga Peoples Front a shekarar 1991 zuwa Arewa for Asiwaju a shekarar 2026, Shugaba Tinubu ya kasance yana tafiyar da siyasa a matsayin aboki na gaskiya.

Kaduna ta tabbatar da hakan a jiya. A ranar 16 ga watan Janairu, 2027, akwatin zaɓe zai tabbatar da hakan da murya mafi ƙarfi.

__________

Abdulaziz Abdulaziz shi ne Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a kuma Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa na Arewa for Asiwaju.

Previous Post

NASIHARMU TA YAU (33)

Next Post

Yadda ‘Yan Mata Suke Tsunduma Cikin Karuwanci A Arewa

Related Posts

Gwamna Radda Ya Cancanci Maimaita Kujerarsa
Siyasa

Gwamna Radda Ya Cancanci Maimaita Kujerarsa

October 14, 2026
Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami
Siyasa

Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami

October 10, 2026
Fati Muhammad ‘Yar Fim Ta Taro Fushin Mabiya Atiku
Siyasa

Fati Muhammad ‘Yar Fim Ta Taro Fushin Mabiya Atiku

October 8, 2026
Next Post
Yadda ‘Yan Mata Suke Tsunduma Cikin Karuwanci A Arewa

Yadda 'Yan Mata Suke Tsunduma Cikin Karuwanci A Arewa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Taya Ni Mu Gyara: Kisan Baƙi Sai Gayya

Taya Ni Mu Gyara: Kisan Baƙi Sai Gayya

November 1, 2025
Abin Da Ya Sa Muka Karrama Jami’an Tsaro A Malumfashi

Abin Da Ya Sa Muka Karrama Jami’an Tsaro A Malumfashi

October 5, 2025
Review of AJN Tremearne’s Publication   Hausa Superstitions and Customs

Review of AJN Tremearne’s Publication  Hausa Superstitions and Customs

February 21, 2026
An Samar Da Maslaha A Takaddamar Sheikh Idris Da Gwamnatin Bauchi

An Samar Da Maslaha A Takaddamar Sheikh Idris Da Gwamnatin Bauchi

July 29, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Sarkin Kano Sanusi Zai Jagoranci Ƙaddamar Da Littattafan Da’awa
  • Babban Saƙon Injiniya Muntari Sagir Ga Al’ummar Malumfashi
  • NASIHARMU TA YAU (36)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Sarkin Kano Sanusi Zai Jagoranci Ƙaddamar Da Littattafan Da’awa

Sarkin Kano Sanusi Zai Jagoranci Ƙaddamar Da Littattafan Da’awa

November 1, 2026
Babban Saƙon Injiniya Muntari Sagir Ga Al’ummar Malumfashi

Babban Saƙon Injiniya Muntari Sagir Ga Al’ummar Malumfashi

October 29, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.