NASIHARMU TA YAU (18)

__________
Ya kai ɗan uwa, ga wani abu da ya kamata ka sani, game da RAYUWA da KUƊI. Kada ka rataya dukkan al’amuran rayuwarka kacokan a kan kuɗi kawai.
Idan ka sanya dukkan al’amuranka a sikelin KUƊI, to babu shakka za ka dawwama cikin nadama a rayuwa. Muhimmin abin sani a RAYUWA shi ne, MUTUNCI ya fi KUƊI.
__________













