• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, July 28, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Siyasa

Sanata Ahmad Babba Kaita: Ba Rabo Da Gwani Ba

Jihar Katsina Ta Yi Rashin Gwarzo A Majalisa

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 14, 2023
in Siyasa
0
Sanata Ahmad Babba Kaita: Ba Rabo Da Gwani Ba

Ahmad Kadaura

76
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Muhammad Aminu Kabir

An rantsar da Majalisa ta Goma ban da Amadu. Wannan abu bai mani daɗi ba. Na san kuma mutane da daman gaske da suka riƙa kira na suna mani jaje bisa wannan rashin da muka yi, kodayake ba ni yankin da Sanata ya fito amma alheransa sun riski mutane da dama da ba su fito daga yankin nasa ba. Wannan ne ma dalilin da ya sa suka yi kukan rashin sa, ba ma iya Jihar Katsina ba har da maƙwabtanta. Allah Ya sauya maka da alheri,  Amadu.

Related posts

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
Zaɓen 2027: Akwai Yiwuwar Farfesa Pantami Ya Yi Nasara – Farfesa Lawanti

Zaɓen 2027: Akwai Yiwuwar Farfesa Pantami Ya Yi Nasara – Farfesa Lawanti

July 8, 2026

Allah Sarki! A ko’ina ka ambaci sunan Sanata Ahmad Babba Kaita, ba wai Jihar Katsina ba duk faɗin ƙasar nan, za ka ji ana yabon shi, ana rububin samun shi. Ba don komai ba, ba sai don saboda ƙoƙarinsa wajen ganin ya samar da ayyukan alheri ga al’umma ba ma ga waɗanda yake wakilta a zauren Majalisar Ƙasa ba, a’a a kaf faɗin Jihar Katsina da ma Najeriya baki ɗaya.

Sanata Kaita ya kasance mutum mai tausayi mai kuma son taimakon jama’a. A kodayaushe burinsa ya taimaka wa al’umma da gwargwadon abin da Allah Ya hore masa.

Hausawa suka ce yabon gwani ya zama dole, sannan sakamakon alheri shi ne alheri! Muna addu’ar ayyukan alherin da wannan bawan Allah ya yi, Allah Ya yi masa kyakkyawan tanaji da su a nan duniya da kuma gobe ƙiyama.

Kowane ɗan Adam tara yake bai cika goma ba, kamar yadda Hausawa suke cewa. Ina addu’a, Allah Ya yafe wa Amadu kurakuran da ya yi a lokacin gudanar da jagorancinsa.

Nasara ko faɗuwa zaɓe dukkaninsu idan aka yi nazari, alheri ne. Na farko, yana sanya ka farin ciki, domin ka yi nasara. Allah kuma Ya ɗora maka wani nauyi na gudanar da ayyukan al’umma, wanda sai dole ka nemi taimakon Allah da al’umma su taya ka wajen sauke nauyin da Allah Ya ɗora maka.

Yayin da na biyun kuma wato faɗuwa zaɓe, za ta sanya ka ka koma baya ka yi nazarin a ina ka samu matsala ko ka yi kurakurai domin ka gyara.

Ina addu’ar Allah Ya ba ka ikon yin tunani mai kyau tare da samar da gyara a inda kake da kurakurai, Malam Amadu.

A kullum idan ina nazari a kan lamarin Amadu, abu na farko da yake faɗo mani a rai shi ne, me ya sa wasu daga cikin mutanen Kankiya suke faɗa da shi, ciki kuma har da waɗanda ya taimaka ma su? Wasu da na ji ta bakinsu ƙalilan, suna cewa ta yaya za a bai wa wasu aiki ba a ba su ba, su da suke yankin da Amadu yake? Irin waɗannan da sauran ƙorafe-ƙorafe, mafi yawa idan ka saurare su, za ka ji ƙorafin na ƙashin kaine ba na al’umma ba. Amma ba su alfahari da cewa ɗansu ya yi wa wasu alheri, har duniya tana yabon shi?

Ni dai alhamdu lillah! Ban da wakilci da Amadu yake tare da gudanar da ayyukan samar da ci gaban ƙasa da yake ƙoƙarin samarwa ta hanyar ofis ɗinsa ga lunguna da saƙon Jihar Katsina, zan tuna da Amadu a kodayaushe da yadda yake taimakon marasa ƙarfi wajen samar da lafiya ko neman lafiya, Amadu ya tallafi iyalai da daman gaske, waɗanda tun ina lissafi har ya ƙwace mani, ba ta hanyata kaɗai ba, ta hanyoyi daban-daban. Allah Ya saka da alheri. Amin.

Ina maka addu’ar fatan alheri tare da neman gafarar Allah yafiya a kan kurakuranka, Malam Amadu

Wassalamu Alaikum yallaɓai!

Previous Post

Shauƙin Son Faɗakarwa Ya Sa Na Zama Mawaƙi – ABDUL EXTRA

Next Post

Shekara 10 Baya: Tunawa Da Malam Suleiman Muhammad

Related Posts

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
Siyasa

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
Zaɓen 2027: Akwai Yiwuwar Farfesa Pantami Ya Yi Nasara – Farfesa Lawanti
Siyasa

Zaɓen 2027: Akwai Yiwuwar Farfesa Pantami Ya Yi Nasara – Farfesa Lawanti

July 8, 2026
Jaafar Jaafar Ya Buɗe Idanun ‘Yan Kwankwasiyya
Siyasa

Jaafar Jaafar Ya Buɗe Idanun ‘Yan Kwankwasiyya

June 17, 2026
Next Post
Shekara 10 Baya: Tunawa Da Malam Suleiman Muhammad

Shekara 10 Baya: Tunawa Da Malam Suleiman Muhammad

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Yau Maulidin Bilkisu Babangida

Yau Maulidin Bilkisu Babangida

September 3, 2023
Jihar Katsina Ta Samu Ministoci Biyu A Gwamnatin Tinubu

Jihar Katsina Ta Samu Ministoci Biyu A Gwamnatin Tinubu

July 27, 2023
Jihar Katsina Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Daminar Bana

Jihar Katsina Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Daminar Bana

July 9, 2023
Nigeria 2027: The Best Way to Defeat President Tinubu

Nigeria 2027: The Best Way to Defeat President Tinubu

August 10, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami’in Soja A Abuja
  • A Voice for Eternity
  • A New Dawn for NIgerian Defence: The Strategic Expansion of the Nigerian Army to 12 Divisions

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami’in Soja A Abuja

Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami’in Soja A Abuja

July 28, 2026
A Voice for Eternity

A Voice for Eternity

July 28, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.