• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, May 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

An Ƙarfafa Ƙawance Tsakanin Jigawa Da Zinder

Don Bunƙasa Noma Da Kiwo

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 9, 2023
in Labarai
0
An Ƙarfafa Ƙawance Tsakanin Jigawa Da Zinder

Gwamnan Jihar Jigawa

216
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Wakilinmu

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya bayyana cewa ƙarfafa dangantaka da zumunci tsakanin maƙwabtan ƙasashen Afirka ta Yamma zai bunƙasa tattalin arziƙin juna, musamman abin da ya shafi harkokin noma da kiwo.

Related posts

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

April 19, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026

Gwamnan ya bayyana haka ne a Larabar da ta gabata, a yayin bikin ƙaddamar da taron ƙara wa juna sani dangane da shige da fice tsakanin Jihar Jigawa da Jihar Zinder ta Jamhuriyar Nijar. Taron ya gudana ne a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.
Gwamnan, wanda mataimakinsa, Injiniya Aminu Usman ya wakilta, ya jaddada muhimmancin wannan ƙawance tsakanin jihohin biyu, da ma ƙasashen Nijar da Najeriya, wanda ya ce zai taimaka matuƙa wajen tabbatar da zumunci mai ƙarfi da ya shafi al’adun juna, kamar kuma yadda zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziƙin juna ta fannin noma da kiwo.
A cewarsa, “yauƙaƙa zumunci da haɗin kai wasu hanyoyi ne sahihai na bunƙasa jituwa tsakanin mabanbantan al’ummun ƙasashen da ke maƙwabtaka da juna.”
“Babu shakka, ƙawancen zai saukaƙa harkokin kasuwanci, musamman shige da fice da kayayyaki da mutane. Nijar da Najeriya a haɗe suke a tarihi, kuma al’adunsu da yanayin rayuwarsu duk iri ɗaya ne tun taletale,” in ji gwamnan.
A yayin taron na kwana biyu, an kafa wani tsari na musamman na kula da zirga-zirgar mutane tsakanin maƙwabtan ƙasashen biyu. Haka kuma ya samu wakilci daga masu ruwa da tsaki da suka haɗa da Gwamnan Zinder da Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arziƙin Afirka ta Yamma (ECOWAS), sarakunan gargajiya, masana daga hukumomin noma da kiwo da shugabannin ƙungiyoyin manoma da makiyaya daga ƙasashen biyu.

Previous Post

Attajiran Arewa Ku Zuba Jari A Arewa

Next Post

HAMISU GUMEL: Dacewarsa A Muƙamin Sakataren Watsa Labaran Gwamnan Jihar Jigawa

Related Posts

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi
Labarai

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

April 19, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Labarai

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina
Labarai

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

February 13, 2026
Next Post
HAMISU GUMEL: Dacewarsa A Muƙamin Sakataren Watsa Labaran Gwamnan Jihar Jigawa

HAMISU GUMEL: Dacewarsa A Muƙamin Sakataren Watsa Labaran Gwamnan Jihar Jigawa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Army, other operatives bust criminal conclaves

Army, other operatives bust criminal conclaves

September 9, 2023
Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
COMMENDATION: Essence of Loyalty to a Principal

COMMENDATION: Essence of Loyalty to a Principal

August 20, 2025
DARASIN JUMU’A DAGA SHEIKH GAMAWA

DARASIN JUMU’A DAGA SHEIKH GAMAWA

September 29, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • POSITIVE COMRADE
  • BUKAR USMAN: The Human Library
  • Sule Lamido’s Theme of Authenticity

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

POSITIVE COMRADE

POSITIVE COMRADE

May 20, 2026
BUKAR USMAN: The Human Library

BUKAR USMAN: The Human Library

May 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.