• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Wednesday, April 15, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Siyasa

Najeriya 2027: Yadda ADC Za Ta Murƙushe APC

SIYASA

Aminu Lawan Hassan by Aminu Lawan Hassan
April 9, 2026
in Siyasa
0
Najeriya 2027: Yadda ADC Za Ta Murƙushe APC

Wasu daga cikin jigogin Jam'iyyar ADC

19
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Najeriya 2027: Yadda ADC Za Ta Murƙushe APC

Daga Aminu Lawan Hassan

Related posts

2027: SABUWAR GUGUWAR SAUYIN SIYASA A KANO

2027: SABUWAR GUGUWAR SAUYIN SIYASA A KANO

February 24, 2026
Komawar Kwankwaso Zuwa APC: Gaba Kura Baya Sayaki

Abubuwan Da Za Su Iya Faruwa Idan Kwankwaso Ya Koma APC

September 28, 2025
Wasu daga cikin jigogin Jam’iyyar ADC

 

__________

A yayin da ake tunkarar kakar zaɓe a baɗi, tuni jam’iyyu da ‘yan siyasa suka fara shirye-shirye, domin ganin sun cin ma nasara a muƙaman da ke akwai, tun daga na Shugaban Ƙasa, Majalisun Tarayya, Gwamnoni da sauransu. Kan haka ake ganin cewa jam’iyyu biyu ne za su fi gwada ƙwanji – jam’iyya mai mulki ta APC da kuma mafi ƙarfin adawa ta ADC.

Ɗan kasuwa kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Malam Aminu Lawan Hassan ya zayyano wasu shawarwari da dubaru, waɗanda yake tunanin cewa idan Jam’iyyar Adawa ta ADC ta bi su, to za ta iya wujijjiga Jam’iyya mai mulki ta APC, ta kafa gwamnati a Najeriya.

Malam Aminu, ya bayyana shawarwarin nasa ne a shafinsa na Facebook, inda ya buɗe da cewa: “ADC, ita ce jam’iyyar da ake wa kallon za ta iya ƙalubalantar Jam’iyyar APC mai mulki amma sai ta yi da gaske saboda APC ba ta shirya barin  mulki ba. Za ta yi duk mai yiwuwa, domin ta ga ta ci gaba da mulki ko ta halin ƙaƙa.”

Ya ci gaba da cewa, “daga cikin shirye-shiryen da take yi, akwai ƙoƙarin ta ga ta mayar da Nigeria tsarin jam’iyya ɗaya, wanda tana  dab da cin ma burinta; domin ta bi duk wata hanya ta mayar da gwamnonin jam’iyyun adawa nata, wanda ‘yan adawa suke zargin amfani da kuɗi da tsoratarwa.”

A cewarsu, “abu na biyu shi ne, ƙoƙarin rufe bakin ‘yan adawa ta hanyar cinna masu hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa kuma ana zargin ta da haɗa rikicin cikin gida wajen amfani da Wike a PDP da Nafi’u a ADC. Sannan za ta yi amfani da ƙabilanci da addini wajen hilatar masu zaɓe.

“Hakazalika, za ta yi amfani da halin talauci da ƙuncin rayuwa da ta tsunduma ‘yan Nijeriya a ciki, wajen raba shinkafa da taliya da sauran kayan masarufi, har ma da kuɗi.”

A nazarin nasa, Malam Aminu ya ce, “ita kanta Hukumar Zabe wato INEC, abar zargi ce, domin tun yanzu ‘yan adawa da ƙungiyoyi sun fara kiraye-kiyayen a sauke shugabanta.”

Ya ce, “idan Jam’iyyar ADC tana so ta kuɓuta daga waɗannan makirce-makircen na Jam’iyyar APC, to ga shawara: A sani fa, ADC babu wani abin da za ta faɗa wa ‘yan Najeriya da za su yarda da ita, domin mutanen cikinta ba wasu sababbi ba ne kuma ba sahihai ba ne. Mutane ne waɗanda akasarinsu, da  su aka rusa Najeriya, aka tatse ta kuma ‘yan Nijeriya kar suke kallonsu. Sun san taron fusatattu ne da waɗanda ba a yi da su, da waɗanda suka faɗi zaɓe. Saboda haka babu wata guguwa da za su yi amfani da ita wajen kayar da APC, kamar yadda Buhari ya yi a 2015.

“Abin da ya rage wa ADC,” in ji Aminu, “shi ne amfani da kaifin hankali wajen zaɓen ‘yan takararta. Da farko shi ne, Atiku Abubakar da Peter Obi su haƙura da takara. Dalilina kuwa shi ne, duk wanda aka ɗauka a cikinsu, APC za ta yi amfani da ƙabilanci wajen ɓata shi. Idan ka ɗauki Atiku, ‘yan Kudu za su ga Arewa suna so su ƙwaci mulki daga hannunsu ne, alhalin ba su gama zangonsu (tenure) na shekara 8 ba. Sannan Kiristocin Arewa tun da suka fahimci tsarin Muslim Muslim yaudara ce, za su gwammace su sake zaɓen Tinubu, tun da sun ga ya fi karkata a kansu fiye da Musulmai,

“Idan suka tsayar da Peter Obi kuwa, akasarin ‘yan Arewa Musulmai za su gwammace su sake zaɓen Tinubu, domin sun san sharrin Inyamiri ya fi na Beyarabe, sannan ana zarginsa da mugun ƙabilanci, lokacin da yake Gwamna a Jihar Anambra.”

A ci gaba da nazarin nasa, Malam Aminu ya ce, “abin da ADC za su yi shi ne, su nemo Goodluck Ebele Jonathan, su haɗa shi Dlda Rabi’u Musa Kwankwaso, su ba su takara.

“Tunanin masu tunani zai koma kan cewa, ai a lokacin Goodluck an yi fama da matsalar Boko Haram, sai dai kuma na san duk zargin da aka yi wa Jonathan bai wuce wannan ba; sai dai a ce an yi rashawa lokacinsa da ƙabilanci. Amma duk abin da za a yi zargi a wannan Glgwamnatin da ta Buhari, an yi ko ana yin sa ninki goma. Da Boko Haram, da ‘yan bindigar daji da ƙabilanci da rashawa da kama karya da sata, waɗannan sun ninka waɗancan.

“Hikimar kawo Goodluck ita ce, shi  Kirista ne, ɗan Kudu, mai sauƙin ƙabilanci, mai jin maganar ‘yan Najeriya, akwai tausayin talakawa  a lamarinsa kuma faɗuwarsa zaɓe ta sa ya fahimci kurakuran da ya tafka. Ga shi kuma zango (tenure) ɗaya zai yi, daga nan ɗan Arewa ya zo ya nema ba hamayya a gaba. Inyamurai za su haƙura su zaɓe shi. ‘Yan Nejdelta za su zaɓe shi. Kiristocin Kudu da Arewa za su zaɓe shi kuma zai samu goyon bayan ƙasashen Yamma saboda Obama ya bayar da gudunmawa wajen kayar da shi a 2015, Trump zai goya masa baya; domin ya baƙanta wa ‘yan Jam’iyyar Democrat rai kuma ga shi Shugaba Tinubu ba ya shiri da Trump.”

Malam Aminu ya ƙarƙare nazarinsa da cewa: “Haɗa Kwankwaso da Goodluck za ta sanya takararsu ta samu gagarumar nasara da miliyoyin ƙuri’u. Wani zai ce Kwankwaso a 2023 ƙuri’a miliyan ɗaya ya samu. Haƙiƙanin gaskiya Kwankwaso ya fi Peter Obi ƙuri’u. Shi  iya mutanen Kano ne suka zaɓe shi, sauran jihohin Arewa ba su zaɓe shi ba, saboda sun san mulkin Kudu zai koma. Saboda Arewa sun yi takwas kuma ga yaudarar tsarin Muslim-Muslim ya yi tasiri. Abin da zai daɗa karya APC, shi  ne ta maye gurbin Kashim Shettima da Kirista. A nan ne mutanen Arewa maso Yamma da na Arewa maso Gabas za su ce ba da su ake mulkin ba. Za su tuttuɗa wa ADC (Goodluck/Kwankwaso) ƙuri’u.

Aminu ya ce, “tabbas, idan ADC suka yi wannan haɗin, sai Peter Obi ya koma ya a nemi takarar Sanata, a banƙara ya zama Shugaban Majalisar Dattawa ko kuma a ba shi Sakataren Gwamnatin Tarayya. Yadda ‘yan Najeriya suke a ƙufulen nan, Goodluck ne kawai zai ci zaɓe, ba ba a yi hayaniya ba. Shugaba Tinubu ba zai yadda ya faɗi a hannun Atiku ba ko Peter ba.”

Abin jira a gani dai shi ne, ko Jam’iyyar ADC za su ɗauki waɗannan shawarwari? Haka kuma, idan sun amince da hakan, ko za su iya nasarar kayar da Shugaba Tinubu, kamar yadda Malam Aminu Hassan ya hasaso? Gare ku jama’ar ƙasa, yaya kuke ganin za ta kaya a zaɓen baɗi, idan Allah ya kai mu, rai da lafiya? Ku bayyana ra’ayoyinku a Comment Section.

______

Previous Post

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

Next Post

Nasihar Juma’a

Related Posts

2027: SABUWAR GUGUWAR SAUYIN SIYASA A KANO
Siyasa

2027: SABUWAR GUGUWAR SAUYIN SIYASA A KANO

February 24, 2026
Komawar Kwankwaso Zuwa APC: Gaba Kura Baya Sayaki
Siyasa

Abubuwan Da Za Su Iya Faruwa Idan Kwankwaso Ya Koma APC

September 28, 2025
KWANKWASO BAI CIKIN WAƊANDA SUKA KAFA APC
Siyasa

KWANKWASO BAI CIKIN WAƊANDA SUKA KAFA APC

September 22, 2025
Next Post
Nasihar Juma’a

Nasihar Juma'a

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Man of Letters

Man of Letters

March 8, 2026
KWATAM HUBA HALIMA TAHIR: Tattaunawa Da Fitattar ‘Yar Jarida Basarakiya

KWATAM HUBA HALIMA TAHIR: Tattaunawa Da Fitattar ‘Yar Jarida Basarakiya

August 19, 2023
Abba Kyari: Ya Kamata A Duba Lamarinsa Da Adalci

Abba Kyari: Ya Kamata A Duba Lamarinsa Da Adalci

July 2, 2023
Limamin Kirista Da Mabiyansa Dubu 100 Sun Musulunta

Limamin Kirista Da Mabiyansa Dubu 100 Sun Musulunta

July 3, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye
  • Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
  • MARTABAR MANZON ALLAH (SAW)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.