FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

__________
√ Ilimi Ginshiƙin Rayuwa:
Babu shakka ilimi shi ne jagora, gishiri kuma ginshiƙin rayuwa. Ilimi shi ne tubali na farko da ake gina tarbiyyar mutum da shi.
Ƙima da muhimmancin da ke tattare da ilimi ba su da iyaka. Allah (swt) a cikin Alƙur’ani Mai Girma, Suratu Muhammad, aya ta 19 yana cewa: “To ka sani (ka ilmantu) cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.”
Wannan aya tana nuna cewa ilimi (sanin gaskiya) ya gabaci komai kuma dukkan ilimi yana nan a cikin sanin Allah da kaɗaita shi, shi kaɗai – domin shi ne mahaliccin kowa da komai kuma shi ne mai ilimi na haƙiƙa. Hakan yana nuna darajar ilimi a cikin Musulunci.
Manzon Allah, Muhammadu (saw), Ibini Maja da Tirmizi sun ruwaito a hadisinsa, yana cewa game da ilimi: “Neman ilimi wajibi ne a kan kowane Musulmi (namiji da mace).”
Wannan hadisin ya tabbatar da cewa neman ilimi ba zaɓin rai ba ne, wajibi ne ga duk wani Musulmi. Wannan ke nuna cewa babu wani Musulmi da zai tabbata kuma ya cika Musulmi sai yana da ilimi, domin da ilimi ake sanin Allah, da ilimi ake sanin yadda za a bauta masa. Haka kuma da ilimi ne ake gudanar da dukkan wani al’amari na rayuwa.
Fitaccen ɗan gwagwarmaya, ɗan siyasa kuma mai kishin ɗan Adam, marigayi Nelson Mandela ya bayyana cewa: “Ilimi shi ne makami mafi ƙarfi da ake amfani da shi wajen sauya duniya.” Wannan kalami na Mandela yana nuna cewa da ilimi ake iya kawo sauyi da cigaba a kowanne fanni na rayuwa.
A matsayinsa na malami, mahaifin Tukur ya daɗe da sanin muhimmancin ilimi. Dalili ke nan bai yi wasa ba wajen ɗora shi bisa turbar neman ilimi. Tun da farko, ya fara sanya shi Makarantar Allo ta Malam Yakubu. Daga bisani aka mayar da shi Islamiyya, wacce ke jikin gidan Alhaji Sirajo Sanda Malumfashi. Kamar yadda aka tabbatar, wannan makaranta, ita ce ta farko a tsarin Islamiyya da aka fara kafawa a Unguwar Ƙofar Gardi, Malumfashi. A waɗannan makarantu biyu ne, Tukur ya fara ɗanɗanar garɗin ilimi – Ilimin sanin Allah, wanda shi ne tushe.
__________
Za mu ci gaba, in sha Allah













