• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, April 18, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Hukuncin Nnamdi Kanu: Minista Bianca ta Nemi Igbo Su Guji Tada Fitina

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
November 22, 2025
in Labarai
0
Hukuncin Nnamdi Kanu: Minista Bianca ta Nemi Igbo Su Guji Tada Fitina

Nnamdi Kanu da Minista Bianca Ojukwu

11
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Hukuncin Nnamdi Kanu: Minista Bianca ta Nemi Igbo Su Guji Tada Fitina

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

February 13, 2026
Nnamdi Kanu da Minista Bianca Ojukwu


                        •••••••

Minista a Hukumar Al’amuran Ƙasashen Waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta yi kira ga ‘yan Najeriya, musamman al’ummar Igbo, da su kwantar da hankalinsu biyo bayan hukuncin da aka yanke wa Shugaban Ƙungiyar Rajin Kafa Ƙasar Biafra (Indigenous People of Biafra-IPOB), Nnamdi Kanu, dangane laifukan ta’addanci a Alhamis da ta gabata.

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a jiya Juma’a, Minista Bianca, wadda ta dawo daga birnin Zanzibar na ƙasar Tanzania, inda ta je aikin sa ido kan wata tattaunawa da ta shafi Najeriya, ta yi bayani dangane da sakamakon shari’ar da cewa “ba abin da muka zata ba ne, kuma ba abin da muka yi addu’a a kai ba amma wannan ita ce gaskiyar da muka tsinci kanmu a cikinta.”

Ta yi kira da a yi hattara, tare da gargaɗi kan duk wani abu da zai iya tayar da hankali a cikin Najeriya ko wajen ƙasar.

“Akan samu lokacin da ƙasa take buƙatar zaman lafiya. Saboda haka, ina shawartar al’ummar Igbo, da ‘yan Najeriya gaba ɗaya, cewa wannan ne lokacin. Akwai buƙatar yin hakuri da nisantar duk wata ɗabi’a da za ta tayar da hankali a wannan lokaci.

“Duk wasu matakai da za a iya ɗauka a fassara su a matsayin masu haddasa fitina, waɗanda za su iya ƙara tayar da hankalin mutanenmu na nan gida ko a ƙasashen waje, ya kamata a guje su,” in ji ta.

Odumegwu-Ojukwu ta bayyana cewa, maimakon tayar da hankali, kamata ya yi a je a tattauna, a samu haɗin kai tsakanin shugabannin Igbo, ciki har da gwamnoni, ‘yan majalisa, sarakunan gargajiya, malamai, ‘yan siyasa da shugabannin ‘yan kasuwa, domin nemo mafita tare.

Ta ce, “Hanya mafi inganci don warware wannan rikici ita ce tattaunawa. Neman zaman lafiya tsakanin Ndigbo a Najeriya bisa adalci, daidaito da mutunci wani abu ne da ke buƙatar haɗin kanmu gaba ɗaya. Kiyaye zaman lafiya da doka muhimmin abu ne domin tabbatar da tsaron ‘yan ƙasa dukkaninsu, ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba.”

Ta ƙara tabbatar wa ‘yan Najeriya da abokan hulɗar ƙasa da ƙasa cewa, har yanzu akwai hanyoyin da za a bi don rage tashin hankali da kuma ɓacin rai da jama’a ke ciki. Ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a Kudu maso Gabas da su haɗu “don tattaunawa tare, cikin gaskiya, domin neman mafita a siyasance dangane da wannan lamari.”

Tun da farko dai, an yanke wa Kanu hukunci ne a ranar 20 ga Nuwamba a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa tuhume-tuhume guda bakwai na ta’addanci. Mai shari’a James Omotosho ya yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai a kan tuhuma biyar, shekaru 20 a kan tuhuma ɗaya, sannan shekaru biyar a wata tuhuma ɗaya, kuma dukkan hukuncin za su gudana a lokaci guda.

Kotun ta zaɓi hukuncin ɗaurin rai-da-rai maimakon hukuncin kisa, bisa la’akari da ƙa’idojin ƙasa da ƙasa da kuma ganin an yi adalci.
_______________

Previous Post

Muhammadu (Saw): Haske Mai Haskakawa

Next Post

An Ɗaure Shi Shekara Biyu Saboda Ya Saci Mudun Wake

Related Posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Labarai

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina
Labarai

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

February 13, 2026
Bura women Celebrate Bukar Usman at 83
Labarai

Ƙungiyar Matan Al’ummar Bura Sun Karrama Dr. Bukar Usman Bisa Cika Shekaru 83

January 9, 2026
Next Post
An Ɗaure Shi Shekara Biyu Saboda Ya Saci Mudun Wake

An Ɗaure Shi Shekara Biyu Saboda Ya Saci Mudun Wake

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

RANAR HAUSA TA DUNIYA

RANAR HAUSA TA DUNIYA

August 26, 2023
Muhammadu (Saw): Haske Mai Haskakawa

Muhammadu (Saw): Haske Mai Haskakawa

November 21, 2025
RAMADAN KARIM: 28-1447

RAMADAN KARIM: 28-1447

March 17, 2026
RAMADAN KARIM: 12-1447

RAMADAN KARIM: 12-1447

March 1, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?
  • Mu Ji Tsoron Allah
  • Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

April 18, 2026
Mu Ji Tsoron Allah

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.