• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, April 25, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Haramta Koyarwa Da Harshen Uwa: Koma Baya Ko Cigaba?

BABBAN LABARI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
November 16, 2025
in Babban Labari
0
Haramta Koyarwa Da Harshen Uwa: Koma Baya Ko Cigaba?

Haramta Koyarwa A Harshen Uwa: Cigaba Ko Koma Baya?

70
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Haramta Koyarwa Da Harshen Uwa: Koma Baya Ko Cigaba?

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026
Haramta Koyarwa A Harshen Uwa: Cigaba Ko Koma Baya?


                          •••••••
A makon da ya gabata ne Hukumar Ilimi a Najeriya ta soke koyar da ɗalibai da harshen uwa a makarantu, ta maye gurbinsa da Ingilishi.

A shekaru uku da suka gabata ne Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya ƙaddamar da dokar tilasta wa ƙananan makarantu da su riƙa koyar da ɗalibai cikin harshen uwa. An yi haka ne, a cewar ministan, bisa tunanin cewa yara sun fi fahimtar karatu da koyarwa sosai idan an yi musu da harshen uwa.

Tsohon Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu

Ministan Ilimi, Dokta Maruf Tunji Alausa, ya bayyana cewa shirin, wanda aka gabatar shekaru uku da suka gabata, ya gaza cin ma manufofinsa, don haka an yanke shawarar dakatar da shi nan take. A maimakon haka, za a dawo da Ingilishi a matsayin harshen koyarwa tun daga makarantun yara kanana har zuwa jami’a.

A wancan lokaci, Adamu ya yi nuni da cewa yara suna fahimtar darussa cikin sauri idan an gabatar musu da su a “harshe na uwa.” Lamarin da binciken Majalisar Ɗinkin Duniya ya goyi baya, dangane da ilmantar da yara ƙanana.

Tsarin ilimi a Najeriya yana fuskantar matsaloli masu tsanani, kamar ƙarancin ingantattun malamai, rashin kayan koyarwa, ƙarancin albashi ga malamai da kuma yawan yajin aiki. Kodayake kashi 85% na yara suna zuwa makarantar firamare, ƙasa da rabinsu ne suke kammala makarantar sakandare.

Ministan Ilimi na Najeriya, Dokta Maruf Tunji Alausa

Kimanin yara miliyan 10 ba su zuwa makaranta a Najeriya, adadi mafi yawa fiye da kowace ƙasa a duniya, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Yayin da yake sanar da janye dokar a Abuja, Minista Alausa ya danganta matakin ga sakamakon jarrabawar da ba su yi kyau ba daga yankunan da suka rungumi koyarwa da harshen uwa. Ya ambaci bayanai daga Hukumar Jarabawar Afirka ta Yamma (WAEC), Hukumar Jarabawa ta Kasa (NECO) da Hukumar Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a (JAMB).

Mabanbantan ra’ayoyi ne suka biyo bayan wannan mataki na soke harshen uwa a wajen koyarwa, inda wasu suka yaba da matakin, suna cewa koyarwa da harshen uwa ya haifar da matsaloli kuma ya taimaka wajen rage ingancin ilimi.

Sai dai kuma wasu na ganin an yi gaggawar soke shi. Suna cewa sauyin tsarin harshe babban abu ne da ke buƙatar kudi wajen horar da malamai, samar da littattafai da kayan koyarwa da kuma lokaci mai tsawo kafin a iya tantance nasararsa yadda ya kamata.

Da yake bayyana ra’ayinsa a tattaunawa da Rediyon BBC Hausa, masanin ilimi, Dokta Aliyu Tilde, yabawa ya yi da matakin. A cewarsa: “Shin Najeriya tana da malamai da aka horar domin koyar da darussa cikin ɗaruruwan harsunan da ke ƙasar nan? Amsa ita ce a’a. Haka kuma manyan jarabawa kamar WAEC da JAMB duk da Ingilishi ake gudanar da su, ba da harsunan uwa ba. Abin da nake gani shi ne buƙatar ƙara samar da ƙwararrun malamai.”

A nasa ra’ayin, mai sharhi kan al’amuran zamantakewa, Habu Dauda, adawa ya yi da lamarin. Ya ce “Ina ganin an yi gaugawar dakatar da shirin, maimakon a ba shi damar ci gaba. Shekaru uku sun yi kaɗan wajen kimanta irin wannan babban sauyi. Kamata ya yi gwamnati ta ƙara kuɗi da lokaci wajen aiwatar da shi.”

A binciken da na gudanar a Soshalmidiya dangane da wannan mataki na haramta koyarwa da harshen uwa, wasu sun bayyana cewa hakan ba daidai ba ne, domin kuwa zaɓen Ingilishi a matsayin yaren koyarwa zai ƙara tabbatar da al’ummarmu cikin ƙangin bauta.

“Tun da farko ma, rashin koyarwa cikin harsunan gida, shi ne ya ƙara dakushe ci gaban Najeriya. Daga lokacin da aka ba Najeriya ‘yancin kai a 1960, da a ce da harsunan gida ake koyar da ɗalibai, da yanzu mun fi ci gaba a rayuwarmu,” a cewar wani nazari.

Ya ci gaba da cewa: “Duk manyan ƙasashen duniya da suka ci gaba a fannin ƙereƙere da kimiyya da kwamfuta, da harsunan gida suka riƙa koyar da ɗalibai ilimi. Misali, ƙasashen Jamus, China, Japan, Indiya, Faransa da sauransu.

Tsohon Ministan Ilimi, marigayi Farfesa Babatunde Fafunwa

“Koyar da ilimi cikin Ingilishi yana gajiyar da ƙwaƙwalwar yaro. A kowane lokaci, sai yaro ya koyi Ingilishi, sannan ƙwaƙwalwarsa ta fassara abin cikin yarensa na gida, daga nan ya fahimta da ilimin da ake koya masa. Misali da a ce kai tsaye da Hausa ake koya masa ilimin kimiyya, lissafi da sauransu, kai tsaye zai fahimta kuma ya aiwatar.”

Ya ƙarƙare da cewa: “Amfani da harshen waje yana dakushe ɗabi’un gargajiya da al’adunmu na gado. Yaren gida, shi ne tushen al’adar kowace al’umma.”

A nasa ra’ayin, Ibrahim Khalil Matazu, cewa ya yi: “Yana cikin tsarin bauta, a hana ka koyo ko koyarwa da yarenka.”

Wani malamin makaranta kuma marubuci a Kano, Malam Nasiru G. Ahmad ya bayyana wannan mataki na soke koyarwa a harshen uwa da cewa: “Ƙara hawa tafarkin jahilci ne da zai fi na yanzu. Don galibinsu matasa a yau takardun shaidar karatu suke da su amma babu karatun da aka ce sun yi a tare da su.”

Shi ma marubuci kuma masanin kimiyyar kwamfuta, Ɗanladi Z. Haruna, ya ƙyamaci matakin gwamnati na soke harshen uwa, ya ce: “Wannan ci baya ne kuma daƙile cigaba ne. Hatta Turawan ma ai suna ta kamfen a kan koyarwa a harshen Uwa. Wannan maganar ma dai na ɗauke ta tamkar batun banza.”

Alhaji Usman Babangida kuwa cewa ya yi: “Ai tun da suka yi watsi da Teachers Collages, tun a nan zance ya ɓaci; sai dai su yi ta mamurensu. In mutum ya sha abin maye, komai ma daidai ne a wurinsa.”

Alhassan Alhassan Mariya ya ce: “Ai matakin gane karatu, a yi shi da harshen uwa.”

Dokta Tsiga, a nasa ra’ayin: “Wannan mataki da gwamnati ta kawo, ci baya ne amma ita tana ganin kamar cigaba ne hakan.”

Shi kuwa Umar Badamasi Machika ya bayyana cewa: “Rashin fahimta ne, babu tsari mai kyau, babu alƙibla sam, ba su da sanin mene ne ya dace a yi amfani da shi. Domin ba ci gaban al’umma a tare da su.”

A can baya, an daɗe ana musayar ra’ayi, dangane da batun koyar da yara cikin harshen uwa. A shekarar 1990, Ministan Ilimi na lokacin, Babatunde Fafunwa ya bayyana goyon bayansa da cewa ya fi dacewa a riƙa koyar da yara cikin harshen uwa. Ya ce wannan mataki yana da alfanu har guda biyu. Na farko, ya ce hakan zai ba yaro damar koyo da ƙwarewa cikin harshensa na gado kuma zai taimaka masa wajen koyon Ingilishi cikin sauri kuma da sauƙi.

Daga dukkan alamu dai muƙabalar nan ta fito da babban ƙalubale da ke fuskantar Najeriya. Hakan kuma ke nuna cewa akwai buƙatar a daidaita kare harsuna da al’adun ƙasa tare da buƙatun tsarin ilimi na ƙasa da kuma tattalin arzikin duniya da ke fifita harshen Ingilishi.
_______________

Previous Post

Rai Baƙon Duniya: Allah Ya Ji Ƙan Abokinmu Yahaya Skito

Next Post

Matsalolin Da Suka Daƙile Super Eagles Daga Gasar Kofin Duniya

Related Posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Babban Labari

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume
Babban Labari

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026
Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel
Babban Labari

Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel

April 2, 2026
Next Post
Matsalolin Da Suka Daƙile Super Eagles Daga Gasar Kofin Duniya

Matsalolin Da Suka Daƙile Super Eagles Daga Gasar Kofin Duniya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Ɗan Kasuwa Ya Koka Da Rusau A Kano

June 25, 2023
Hajj 2023: Uba Sani, Arrigassiyu bag awards

Hajj 2023: Uba Sani, Arrigassiyu bag awards

September 24, 2023
GURƁATACCEN HATSI: An Ja Hankalin Hukumomin Jihar Katsina

GURƁATACCEN HATSI: An Ja Hankalin Hukumomin Jihar Katsina

August 20, 2023
An Karrama Bagizage Barista Kabir Mantissa

An Karrama Bagizage Barista Kabir Mantissa

July 10, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.