• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, May 25, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Digirin Girmamawa: Ya Kamata Jami’o’in Najeriya Su Karrama Rarara

TSOKACI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 21, 2025
in Gizago
0
Digirin Girmamawa: Ya Kamata Jami’o’in Najeriya Su Karrama Rarara

Dr. Dauda Kahutu Rarara

29
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Digirin Girmamawa: Ya Kamata Jami’o’in Najeriya Su Karrama Rarara

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Dokta Dauda Kahutu Rarara

 

                  _______________

A jiya Asabar, 27-03-1447 (Hijiriyya) = 20-09-2025 (Miladiyya), a Birnin Tarayyar Najeriya Abuja, shahararren mawaƙin siyasa, Dokta Dauda Kahutu Rarara ya samu karramawa ta musamman daga “WASU” da suka yi amfani da sunan Jami’ar European American University, inda suka ba shi lambar girmamawa ta Digirin Digirgir (Honorary Doctorate Degree).

Sai dai kuma abin takaici, daga baya aka samu sahihin labarin cewa, jami’ar ta bayyana cewa ba ita ce ta ba Dauda wannan digiri ba. Wannan ke nuna cewa wasu ‘yan damfara ne suka shirya wannan digiri na bogi.

Amma dai duk da haka, wannan karramawa, duk da cewa ba American European University ce ta gaske ta ba shi ba, amma hakan ya nuna irin rawar da Rarara ya taka kuma yake kan takawa wajen bunƙasa fasaha da tasiri a harkokin siyasa da al’adu a Najeriya. Don haka, ya kamata a samu wata sahihiyar jami’a a Arewacin Najeriya, ta ba shi wannan digiri na karramawa. Su kuma mutanen da suka shirya wannan damfara, ya kamata jami’an tsaro, musamman ‘yan sanda da EFCC su binciko su, domin su fuskanci hukunci, musamman yadda suka tozarta Najeriya a idon duniya.

Rarara ya shahara wajen rera waƙoƙin siyasa da suka zamo ruwan dare tsakanin talakawa, matasa da kuma shugabanni. Waƙoƙin nasa sun kasance masu jan hankali wajen yaɗa manufofi da saƙonnin jam’iyyu da ‘yan siyasa daban-daban. Duk da yake ana ganin waƙoƙinsa na siyasa ne, sai dai a haƙiƙanin gaskiya sun kuma taka rawa wajen ilmantarwa da nishaɗantarwa ga jama’a, musamman ma yadda ya faɗaɗa su zuwa na soyayya da sarauta.

Fasahar Rarara ta sha bamban da ta sauran mawaƙa saboda yadda yake amfani da kalamai masu girman ma’ana da karin magana wajen isar da saƙo. Waƙoƙinsa sukan ƙunshi darussa kan zaman lafiya, haɗin kai, juriya, da kuma buƙatar talaka ya fahimci rawar da yake takawa a dimokuraɗiyya. Wannan ya ƙara masa karɓuwa a tsakanin al’umma, musamman a Arewacin Najeriya.

Baya ga waƙoƙin siyasa, Rarara ya kuma yi fice wajen samar da sabon salo na haɗa waƙa da tarihi, inda yake kawo misalai da tunawa da abubuwan da suka faru a baya, don nuna alaƙa da halin da ake ciki. Wannan fasaha tasa ta tabbatar da cewa waƙar Rarara ba wai kawai ta siyasa bace, har ma wata hanya ce ta rubuta tarihi ta hanyar waƙa.

Saboda irin wannan gudummawa da kuma tasiri a fannoni daban-daban, ba abin mamaki ba ne ganin yadda wasu suka yi amfani da sunan jami’a mai girma kamar European American University suka karrama shi da wannan digiri. Wannan karramawa alama ce ta yadda duniya ke gane irin gudummawar da mawaƙa ke bayarwa wajen faɗakarwa da sauya tunanin jama’a.

Karramawar da Rarara ya samu a yau, tabbas za ta ƙara masa ƙarfin gwiwa wajen ci gaba da fitar da waƙoƙi masu ma’ana da kuma ƙara bunƙasa fasahar Hausa. Haka kuma, zai zama abin koyi ga sauran mawaƙa da masu tasowa domin su ga cewa waƙa na da daraja kuma za ta iya kawo girmamawa daga manyan cibiyoyi.

A ƙarshe, muna taya Dauda Kahutu Rarara murna bisa wannan gagarumin matsayi da ya samu. Wannan karramawa ba wai tasa ce kaɗai ba, ta haɗa har ma da al’ummar Hausawa da Najeriya baki ɗaya.

Allah ya ƙara masa basira da kuma nasara a dukkan al’amuransa.
_______________

Previous Post

Katsinawa Suna Murna Da Ɗaukakar Da Maryam Idris Ta Samu

Next Post

KWANKWASO BAI CIKIN WAƊANDA SUKA KAFA APC

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
KWANKWASO BAI CIKIN WAƊANDA SUKA KAFA APC

KWANKWASO BAI CIKIN WAƊANDA SUKA KAFA APC

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Rigakafi Ne Babban Jagoran Yaƙi Da Sankarar Mahaifa – Janar Buratai

Rigakafi Ne Babban Jagoran Yaƙi Da Sankarar Mahaifa – Janar Buratai

May 29, 2023
SASSANYAN AMINCI (6)

SASSANYAN AMINCI (6)

September 13, 2025
OUTRAGEOUS: Why is Nigeria not Great?

OUTRAGEOUS: Why is Nigeria not Great?

April 13, 2024
TA’AZIYYAR PAPAROMA FRANCIS: SHIN INA LAIFIN PANTAMI?

TA’AZIYYAR PAPAROMA FRANCIS: SHIN INA LAIFIN PANTAMI?

April 22, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • POSITIVE COMRADE
  • BUKAR USMAN: The Human Library
  • Sule Lamido’s Theme of Authenticity

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

POSITIVE COMRADE

POSITIVE COMRADE

May 20, 2026
BUKAR USMAN: The Human Library

BUKAR USMAN: The Human Library

May 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.